← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 127

Sashe 20

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya amsa mata kai, sannan ya fice sai kamshin tsadadden turare yake zubawa, taku yake irin na yayan manyan sarakai taku mai cike da kasaita da isa irin ta masu arziki da yake magana da kansa a jikinsu da kuma sarauta da ke cikin jininsu, one step yayi saura ya sauka daga entrance din Anty sai ya ji wata familiar voice ta kira sunansa.

“Abiey....”

Ya daga kai ya kalleta doguwar rigar abaya ce a jikinta sai wata yar karamar jaka makalle a hammantanta.

“Hi...”

Kamar wanda be ji abun da ta fada ba, ko kuma be san da yaren da take magana ba haka yayi mata ya cigaba da takunsa har ya isa gurin motarsa a daidai lokacin ne ita ma ta karaso.

“Hi”

Ya mata banza kamin ya kare mata kallon tun daga saman kanta da rabi ke waje saboda ya sha gyara har zuwa kafafuwanta, if he can remember ita ce yarinyar da ya gani a fadar Mai Martaba kuma ita ce ya gani a cikin jirgin lokacin da zai je Abuja, ba tare da ya ce da ita komai ba ya bude motar ya shiga yayi reverse ya fice daga gidan.

“Do i look ugly?”

Ta tambayi kanta tana karewa kanta kallo. A waje ya faka motarsa saboda gudun kar ya shigo da ita ciki Yasmin ta gani ko ta ji karar tsayawar motar ta gudu ta boya, slowly yake tafiya har ya iso kofar falon yayi knocked and he got lucky Yasmin ta bude masa da kanta. Wani irin bugawa zuciyarta ta yi da mugun karfi shi kuma ya tsare da ido fuska ba yabo ba fallasa.

“Can we talk now?”

Ta saki kofar ta dawo ta zauna rike da littafinta na islamiya da take home work, ya zauna a kujerar dake facing dinta.

“First of All Yasmin miyasa kika min haka?”

Ta kasa dagowa ta kalleshi gabanta sai faduwa yake kamar zai cire.

“Why? And kika maida ni kamar wani dan'iska kullum idan na zo sai ki boye”

Hawaye ne ya fara mata zuba.

“Talk to me ba kuka na zo ki min ba”

“Ban san miyasa na aikata hakan ba”

“As how baki san miyasa kika aikata haka ba? Hankalinki ya gushe ne?”

Ta girgiza masa kai.

“To ta ya? Zai da muka yi magana da ke ta fahimta tun kamin Mai Martaba ya aiko, amman kika lalata komai”

Wannan karon da fada yake mata magana saboda ta bata masa rai sosai.

“Fine abun da ya faru ya faru, yanzu zaki iya gyara ki fadawa iyayenki cewar ke kin janye ba ni kike so ba kinji?”

Ta dago ta kalleshi tana sauke wani irin wahalallen numfashi.

“Kin ji?”

Ta amsa masa kai hawaye na sauko mata sosai.

“Good girl, daman ni na san indai ba sherin shedan da zugar zuciyata as pretty as you are me zaki yi da ugly man like me, yadda kika da natsuwa ai you deserve someone better than me, ni kuma sai na je na ji da Zahra ta”

Ya karasa yana murmushi yana kallon fuskarta babu abun da take sai hawaye kamar ruwa, kamar ya tambaye wani abu sai kuma zuciyarsa ta hana shi.

“Now zaki iya min alkawarin zaki fada ma iyayen ki haka?”

Ta daga masa kai.

“Good Thank you, ina Momy?”

Bata iya amsa masa sai girgiza masa kai ta yi alamar Momy bata nan.

“Okay kar ma ki fada mata na zo”

Ta daga masa kai sai da ya sake kallonta sannan ya nufi kofar fita sai ta juya ta bi bayansa da kallona zuciyarta na mata mugun zafi. A compound din gidan ya ciro wayarsa ya kira Dr Zainab sai dai ba ta yi piciking ba har sai da ya sake kira.

“Hello aiki fa nake yi?”

“I need to see you kina ina?”

“Asibiti ya aka yi”

“Okay”

Ya sauke wayar ya danna key hannunsa ya bude motar sannan ya shiga yayi mata key heading to Favor Hospital gurin Yayarsa.
[10/9, 10:54 PM] Oum_Nuwaira🥰: 2️⃣3️⃣

Ban san gurin da zan same shi a aibitin ba, hakan ya saka lokacin da na shigo na kira shi a waya sai yace min na samu guri na zauna a daya daga cikin kujerun da suke ward din female surgical ward na jira shi, ba musu na zauna, jiki babu karfi ina ta kallon mutane, wasu da suke zaune kusa da ni suna ta hira kamar ba su da damuwa a tare da su masu tafiya ma kallonsu nake, ni kuwa tawa zuciyar kunshe da bakinciki da tunani kala kala, na zauna a gurin for moren 3 hours ina jiransa, na sake kiransa sai yace min na jira shi aiki yake, da na gaji da zama a ciki sai na fito waje ina zagayawa rumgume da hannayena, a wajen ma na yi awa daya ina jiransa be kira ni be kuma fito ba, hakan yasa na kira kiransa sai ya sake ce min aiki yake na jira shi. Na kusan awa biyar a aibitin ina jiransa be fito ba kuma be kira ni ba, wannan karon da na gwada kiran wayarsa sai na same ta a kashe, a take idona ya cika da kwalla, na gane idan kana nema a gurin wani kai ne abun wulakantawa, a yau saboda ni nake nema yaki ya bani lokacinsa wata kila saboda ya san dalilina na zuwa gurinsa, domin ba za a ce ya rasa lokacin kula da ko da 30min ne ba. Komawa na yi ciki ina tambayar mutanen ciki na fadi sunansa da kuma asibitin da yake aiki kamin wannan har na nuna musu numberta, sai wata yar albarka mai far'a a cikin mutanen tace bari ta duba min shi.

“Biyo ni mu je....”

Na bita muna ta tafiya har muka isa wani bangaren na dabam, sai ta saka na tsaya daga waje ta shiga ciki ta masa magana, kusan a tare suka fito yana ganina ya hade fuska kamar ba shi ba domin ban taba ganinsa a cikin wannan yanayin ba.

“Je ki jira a inda na ce zan fito”

“Toh”

Na amsa na juya na fice na dawo inda na tsaya dazun a nan ma sai da na gaji na fito harabar asibitin ina dan zagaya idona na zubar da hawaye sannan na hango shi ya fito zan tako na iso gareshi sai yayi min alama da na jira shi a nan, haka na ja na tsaya har ya karaso yana kallona.

“Ina wuni ya aiki?”

“Lafiya kalau, me kike so?”

Sai na samu kaina da nauyin baki na kasa furta komai, wata kila har da fuskarsa da na gani a hade.

“Zahra me kike son zama ne? Kin san da cewa zaki saka kanki a cikin matsala ne kawai idan kina kokarin tuntubata? Tun muna yin abu a sirrance har wani ya ji?”

Na sauke kai kasa hawaye na zuba.

“Me kike so?”

Na kasa magana, ya sake tambaya na kasa magana sai hawaye nake yanayin yadda ya zo min na san abun da zan tambaya ba zai samu a gurinsa ba. Tsaki yayi ya juya zai koma sai na kira sunansa.

“Dr Hamid”

Be juyo ba ya cigaba da tafiya sai na yi saurin binsa ina.

“Magana kawai nake son yi da kai”

“Wato na gane kina da matsala Zahra, karki saka kanki a matsala kuma ki saka ni ba zaki iya daukar wannan”

Ya fada a tsawa yana nuna da yatsa.

“Heyyyyyy kaiiiiiii”

From nowhere muka ji muryar da ba zan taba iya mantawa tana dira a kunnuwanmu kamar saukar aradu, wanda hakan ya saka mutane da yawa kallon inda muryar take fitowa ciki kuwa har da ni da Dr Hamid, na tabbatar be ji abun da muke fada ba, sai dai ya fahimci akwai rashin jituwa ne saboda nuna da yatsa da Dr Hamid yayi da kuma hawayen da suke min zuba.

“Be careful, you have no idea who this woman is”

Ya fada a lokacin da ya karaso kusa da mu, Dr Hamid ya kalleni

“Who's this”

Ni kaina na san ba tambayar waye yake ba, tambayar sanin matsayinsa yake a gurin.

“Ban san shi ba”

Na amsa ina amsa wani irin kallona na tsana.

“Malam Lafiya?”

“Zaka san lafiya idan ka sake nuna mata yatsa”

Dr Hamid ya tambaya sai Abiey ya amsa masa.

“Please tell me shi ne dalilin kukanki”

Ya tambaya yana kallona, wannan karon zubar hawayen da nake ba na komai ba ne sai na bakinciki ganin Abiey. Dr Hamid be ce komai ba ya juya ya bar mu tsaye a gurin.

“What now Abiey.... Sai me?”

Na tambaya ina masa kallon da shi kansa ya san ba shi da na biyu a mutanen da na tsana a duniyar nan.

“You called my name Hiayatee.. You say Abiey...”

The name part ‘Hiayatee’ ya fi komai kona min rai fiye da ganin fuskarsa a yau, haka yake kiran a wacan gurbatacccen lokacin da muke tare, domin a gurina gurbatacaccen lokaci ne wanda na bata shi a banza a wofi.

“Me kike nema a gurin mutumen nan Hiayatee? What do you want?”

Wani kallon nake masa zuciyarta na tafarfasa gabana na duka uku uku.

“Ka san abun da na ke so? Na daina ganin wannan mummunar fuskar taka, kuma na daina jin sunanka ko wani mai irin sunanka har karshen rayuwata”

Share hawayena na yi na juya taku daya biyu ban yi na uku ba ya sha gabana yana min wani kallo na tausayin munafurci.

“How are you now? Do you need someone to talk to? I know how you felt”

“No you don't... Karya kake yi baka san yadda nake ji ba, baka taba rasa kowa ba balle ka san yadda nake ji, kuma ka ci min fuska a lokacin da naje neman taimakonka and how you're standing in front of me kana tambayar how i feel? Ko kake na fada maka irin zafin da nake ji a cikin zuciyata na rasa masoyi da na yi so that ka yi celebration ranka yayi sanyi?”

Guntun murmushi na ga yayi ya sauke kansa kasa ya busar da iskar bakinsa ya girgiza kai at the same time. Na wuce shi na yi gabana.

“Sorry about your lost...”

Na juyo.

“Mijina ba ya bukatar addu'arka”
Chapter 20 · 0% Book details