← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 127

Sashe 15

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana fadar hakan sai ta mike tsaye ta shige cikin dakinta ta bar a gurin ina ta aikin rusar sabon kuka, gaba daya sai zuciyar ta ki yi min dadi gaba daya na ji ina ma a can na zauna ni kadai ban zo gidan ba, da ban ji wata magana marar dadi a akan Deen ba. Dayan dakin da na saba kwana lokacin da ina budurwa Mama ta gyara min na shiga na kwanta rai babu dadi har safe. Bayan na gama sallah asuba na koma na kwanta amman na kasa bachi har Mama ta gama shirya abinci safe ta shigo ta kawo min, sai na tashi da sauri ina gaisheta.

“Ina kwana Mama”

“Lafiya kalau, Zahra ki yi hakurin da maganar da na yi miki jiya kin ji? Tuntuben halshe ne da rashin fahimta”

Ta fada min fuska a sake sai na daga mata kai jina a sanyeye, zauna ta yi kusa da ni tana sauke ajiyar zuciya.

“Ban zan miyasa kika aikata haka ba tare da neman shawarata ba, Zahra ni mahaifiyarki ce kaf duniyar nan baki da kamar ni, kowa ya so ki to a bayana yake kuma ba zan taba son abun da zai cutar da ke ba ko ya jefaki a cikin wata matsala”

“Mama na yi tunanin idan aka yi ma masa aikin zai rayu ne, kuma na san idan na fada muku zaku iya hana ni”

“Ba zan bari ki aikata ba tabbas da kin fada min, domin ransa ba a hannunki yake ba a hannun Allah yake, amman yanzu kin riga kin aikata da zaki ji shawarata da na shawarce ki da shawarar da zata fidda ke da mu”

Na kalleta.

“Wace Shawara ce Mama?”

“Ki dauki kaddara wanda ita ta saka kika amince da wannan abun tun farko, kin riga kin yi alkawari tun farko kuma karya alkawarin na nufin bada wani adadi na kudi da ko an hada ni da ke an siyar ba zamu yi wannan kudin ba, kuma zaki jawa kanki abun magana ne kawai yan jarida su taru akanki ana miki tambayoyi haka kuma kutu zata hukuntaki, idan kuma kika gudu zaki iya jefa kanki a cikin hadari ne irin wanda kika saka kanki a yanzu”

“Mama na bata cikin kenan?”

Ta daga min kai.

“Shi ne kawai mafita ni da ke”

Wani abu na ji ya tsaya min a zuciya na juya kaina na juyo na rasa ina zan saka kaima na ji sanyi, ina zan jefa rayuwata na samu sassauci.

“Shikenan Mama zan bata”

Na amsa ina hawaye ita ma hawayen take tana kallo.

“Da kin shawarce ni tun farko da baki aikata wannan abun ba, da yanzu baki jefa kanki a cikin wannan halin ba”

Ta rumgume ina ta kuka babu kakkautawa. Misalin sha daya Yaya Maryam ta zo gidan ita kanta na lura tana cikin damuwa musamman da na fada mata shawarar da Mama ta ba ni.

“Mama ba zata baki shawarar da zata cutar da ke ba, ki yarda ki bada ďan karki sake aikata abun da zai saka ta yi fushi da ke, domin ranta ya bace sosai da na fada mata shiyasa ta yi fushi ko a lokacin da aka kira aka fada mana halin da kike ciki cewa ta yi ba zata je ba kuma ni ma ba zan je ba”

“Na aminta Yaya Maryam zan ba au duk abun da na haifa Allah yasa hakan shi ne mafita a gareni”

“Ameen yar'uwata”

Na kwantar da kaina jikinta ita kuka ni kuka, Mama ma dake zaune bakin kofar dakinta ina jiyo shisshikar kukanta wata kila ta ji abun da muke tattaunawa.

“Yaya Maryam dan Allah zaki je asibitin ki karbo min number likitan?”

“Saboda me? Me zaki yi da ita?”

“Na fada masa cewar ina nan, kuma na fada musu edd na domin wacan da na fada mata ba na gasken ba ne”

“Zan je na karbo miki Inshallah”

Da taimakonta da karfafa guiwa na ci abinci, ina gamawa sai ga Hajiya da wasu yan'uwanta da Bahijja gaba daya Hajiya ta canja kamar ba ita ba domin tana da jiki amman yanzu duk ta zube.ta rame sosai, ta nuna min damuwarta na tafiyar da ni bada sanin kowa ba, sannan ta karfafa min guiwa yadda zan sarrafa rayuwa na samu sukuni saboda Mama ta musu karyar cewar na kasa zama gidan ne saboda Deen baya ciki.

“Daman na sani sai kin shiga damuwa, amman ki bar wa Allah komai Zahra shi zai miki mafita ya yaye miki komai”

Hajiya ta fada, a gidan suka wuni har dare sannan suka tafi, lokacin da mijin yaya Maryam ya zo sai suka tafi gidana ita da shi suka kwaso min tufafina na sakawa suka kawo min sannan suka wuce.

Washe gari bata dawo gidan ba sai da number likitan ta fada min a gurinsa ta karbo da kanta, sai an saka line a wayar Mama na saka miki number na kira shi be daga ba har ta yanke ina kokarin kiransa na biyu sai gashi ya kira.

“Hello....”

“Zahra ya kike?”

“Lafiya Kalau”

“Maa Shaa Allah, wannan line ki ne?”

“Eh nawa ne”

“Wanda ta zo karbar numberki ta fadi min cewar yayarki ce hope dai bata san da maganar komai ba?”

Na dan yi shiru sannan na amsa.

“Ta sani”

“Haba Zahra ya zaki yi haka? Abun da ya kamata ace sirrinmu ne? Ta ya zaki sako wata a ciki?”

“Yar'uwata ce idan bata sani a taya zan kiraka ka karbi haihuwa ta? Dole sai wani na kusa da ni ya sani bayan ita babu wanda ya sani”

“Amman kamata yayi kamin ki sanar da ita ki fara shawartarmu saboda wannan abun da kike ganin sai iya jefa mu a matsala mu duka”

“Ni dai na kira na fada maka cewar edd da na fada ma Jamila ba daidai ba ne, na duba takardar zan haihu nan da sati uku Inshallah”

“Amman miyasa kika canja da farko?”

“Ba canjawa na yi ba, na fada ne ba tare da na duba ba ashe ba daidai na fada ba”

“Shikenan zamu shirya komai kamin lokacin, amman zan zo na karbi takardar anjima”

“Amman bana gida ina gidan mahaifiyata zan aiko maka addireshin yanzu idan mun gama waya”

“Amman ba matsala idan na zo?”

“Ka kira ni kamin ka zo sai na san yadda zan yi na fita”

“Okay”

Ya kashe wayar. Dare na yi sai ga kiranshi ya shigo na yi zaton da Jamila zai zo sai yace min

“Ga almajiri nan zan aiko idan ya shigo bara ki kira shi kamar zaki ba shi sadaka sai ki ba shi takardar ya kawo min”

“Toh”

Na amsa sannan na tashi na shiga daki na dauko takardar na rike a hannu, almajin na yin bara na kira shi ya shigo na mika masa takardar ba tare da nace masa komai ba shi ma ya karba ya fice be ce min komai ba.
Fitarsa da kamar minti goma Dr Hamid ya kira ni.

“Na karba, amman ya kamata idan zaki haihu ki kasance ke kadai sai wannan yayar taki da ta san komai so that mu samu yin aikin ba tare da sanin kowa ba”

“Toh”

“Sannan na ba Jamila number wayarki zata kira ki”

“Tace min zata yi tafiya”

“Eh taje Abuja kwananta daya ta dawo saboda wata yar matsala da mijinta ya samu, zamu shirya haihuwarta kamin taki haihuwar saboda komai ya zama daidai”

“Toh”

“Kuma idan kina jin wata matsala ki fada min mu tari abun da wuri”

“Bana jin Matsalar komai”

“Yaushe zaki koma awo?”

“Ranar Laraba na dade ban je ba amman zanje wannan larabar”

“Shikenan idan an fada miki wata matsalar ki kiri ni ki fada min”

“Toh”

Na amsa sannan ya kashe wayar, tun daga wannan ranar ban sake lafiya ba awon cikin ma da nace zan je ban je ba saboda ciwon zuciya da ya matsa min kuma ban fadawa kowa ba saboda kar a matsa min da zancen zuwa asibiti, ni kadai na san halin da nake ciki, kuma a kullum sai Dr ya kira ni ya tambayi lafiyata na amsa masa da bana jin komai a lokacin da ya tambaya ko naje awon sai na amsa masa da eh sun ce komai lafiya yake, na kwashe kusan sati daya kullum a daki nake bana fitowa sai idan zan yi fitsari so alwala wani lokacin ma sallah a zaune nake yinta saboda cikin ya kara yi min kasa a yanzu, ga tunanin da nake ya haifar min da rama sai cikin ya janye ni na koma kamar wata yar tsana.
Ranar wata jumma ina kwance daki rike da carji sai ga kira ya shigo wayata da bakuwar number, na dade ina kallon number har kiran yana daf da katsewa sannan na amsa na kara wayar a kunne.

“Hello”

“Zahra ce?”

Na ji muryar Jamila

“Eh ni ce ina wuni”

“Lafiya kalau, Dr ya fada min abun da kika yi na shigowa da yar'uwarki cikin maganar nan, Zahra kina ganganci da rayuwarki kuma kina kara jefa kanki a cikin matsala ne, domin na rantse miki da Allah idan maganar nan ta fita sai na aikata miki abun da baki yi tunanina ba, kin san wacece ni? Kin san su waye dangina? Kin san waye mijina? Kin san yan'uwan mijina? Fitar sirrin yana nufin rasa aurena rasa gatana kin kuwa san idan na rasa daya daga ciki sai na aikata miki abun da baki taba zato ba, kin san ba zaki iya ba waya cs ki fara? Ki gargadi yar'uwarki karta kuskura fadawa kowa? Kuma karki kuskura cewa zaki yi wasa da hankalina ko na Dr kika fada min fake date na Edd dinki sai yanzu zaki fada mana na gaskiya? Wani abu kike shiryawa ko? Sai na baki mamaki Zahra kina fama da talaucinki kin samu an taimaka miki kike kokarin jefa ni a matsala, wannan ya zama na farko kuma na karshe da wani zai ji zancen nan? Kuma da zarar kin mallaka min ďana ko ƴata ki manta da ni a rayuwarki dan kar zuciyarki ta raya miki wani abu”
Chapter 15 · 0% Book details