Sashe 115
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Shiyasa na yi saurin fahintarka ďana saboda na taba kasancewa a irin halin da na kasance a wani lokaci can ba, na kaunaci Mahaifiyarka irin kaunar da har yanzu babu wata mace da ta maye gurbinta a gurina, a wacan lokaci mu yayan sarakuna ba ma zaban matan aure, sai dai a zaba mana wannan ce kaddarata ta farko da, rabon a same ka ya kashe mijinta ya mallaka min ita, kamin mai faruwa ta faru mu kasance a haka a yanzu, wannan ya saka a lokacin da Lami ta shigo min da labarin abun da aka ce ka aikata, amaimakon raina ya bace sai na ji tausayi, ka rasa abubuwa da yawa da suke saka ka farinciki, na kudirta a raina idan har da haske ne ka aikata haka, zan maka uzuri domin idan na matsa maka ban san abun da zai biyo baya ba, indai kana son matarka mu masu yi maka marhabun ne, tunanin Babba be taba zama irin an yaro ba, babban dole ne ya kasance ta mai hakuri da kawar da kai kuma yin tunanin kamin yanke hukunci...”
Abiey be san lokacin da ya rumgume mahaifinsa ya fashe da kuka kamar mace, lallai a yau ya tabbatar mai hakuri mawadaci ne, kuma kowa yayi hakuri ya ce be ci riba ba to kadan yayi, abubuwa biyu masu matukar tsada a rayuwarsa sun zo masa a lokacin da be yi tsammani ba.
[12/6, 12:23 PM] Oum_Nuwaira🥰: 7️⃣0️⃣
Tun da na shiga falon ban yarda na kalli inda yake ba balle har mu hada ido, kaina an kasa har na zauna a kusa da kofar ba tare da na ce komai ba.
“Zahra na kira ki ne akan maganar yaronki, ke da Jamila dukanku ba ku yi tunani Mai Kyau ba kamin aikata abun, sai dai za a duba miki domin talauci da rashin mafita ne ya saka kika aikata, a yayinda ita kuma ta yi amfani da damar da take da shi ta aikata wannan laifi, wanda ya haifar mata da bakinciki a yanzu, ni ma kuma ya haifar min zai kuma haifarwa yan'uwana, kuma zai zame min abun magana a gari da dangi, abun da zai saka makiya na su jidadi su yi dariya, amman haka Allah ya kaddara ba mu sa mu zabi abun da zai faru da mu ba, kuma ba a mana ikon kawar da abun da bama so ba sai abunda Allah ya rubuta mana”
Yanayin yadda yake magana akwai matukar tawakkali da tausayi, muryarsa har rawa take wata na hawa kan wata.
“Ban aikata hakan saboda na cutar da daya daga cikinku ba, ban kuma yi tunanin nima hakan zai cutar da ni ba, idona ya rufe a lokacin da nake neman mafita akan rayuwar Deen, na manta da iyayensa, da kanwarsa da yan'uwansa, na siyar da Amir ba dan bana kaunarsa ba, sai dan ina ganin kamar hakan mafita ce a gareni, ina neman yafiyarki hakika mun cutar da kai na sani, kuma zaka iya daukar ko wane irin mataki amman baka dauka ba saboda hallaci irin naka”
“Zan hannata miki ďanki a hannunki, sai ki tanadi bayanin da zaki gabatar ma kakaninsa da zai wanke ki ke a gurinsu”
Na dago na kalleshi idanuwana cike da kwalla.
“Babu wani bayani da zan tana, abun da ya faru sirrina ne, babu wanda zai san da wannan sirrin har abada”
“Ban fahimci ki ba Zahra”
“Idan har akwai wanda ya cancanta ya rike Amir a yanzu to kai ne, yan'uwanka sun san Amir a matsayin ďanka, su kuma ba su san shi ba, ba su san dadinsa ba, amman kai kasan dadinsa domin ka rike shi na tsawon watanin a hannunka, duniya tana kallon Amir a matsayin ďanka abun tozarci ne a gareka a yanzu labarin nan ya fita cewar yaron da kake ikirarin naka ne an gano ba ďanka ba ne, nasadin haka labarinka da nawa da kuma na matarka zai fita, wata kila har ya janyo maka wata matsalar, idan har zaka rike Amir tsakani da Allah kamar ďanka da ka haifa, ni kuwa zan bar maka shi kuma ba zan tana siffanta kaina a matsayin uwarsa ba haka ba zai san wani a matsayin ubansa ba sai kai, wannan sirrin zai cigaba da rufuwa har kasa ta rufe idona”
Baki sake yake kallona, kamin ya girgiza min kai.
“Karki yarda ki sake aikata wani abun ba tare da neman shawara ba, ina tunanin yana daga cikin abun da ya haifar min da matsalar da kike ciki a yanzu, kuma idan mu ka yi haka kamar kin cutar da kakanin yaron nan ne, domin su ma suna da hakki akan dansu, kuma idan ban manta ba a cikin labarin da kika ba ni kin fada min cewar su biyu kawai ta haifa a yanzu kuma ya rasu, na tabbatar da ace ta san da cewar jikanta yana raye ba za ta bar ki da shi ba”
“Amman kai kuma fa?”
Ajiyar zuciya ya sauke ya kishingida jikin kujerar da yake zaune, yana kokarin magana sai ga Ummiter ta shigo hankali a tashi jikinta har rawa yake.
“Yaya ban ga Amir ba, na duba a dakinsa ban ganshi ba”
Mr Bashir ne ya riga ni zabura ya mike tsaye.
“What...! Kin duba da kyau kuwa?”
A lokacin ni ma na mike tsaye ina kallon Ummiter hankalina a tashe.
“Wallahi na duba ko'ina a dakin ban ganshi ba!”
“Kin duba dakin Jamila”
“Aa ban duba ba”
A gaba daya muka dugunzuma muka fice zuwa bangaren Jamila, da wani kalar sauri mai kamar gudu na bi bayan Mr Bashir na shiga dakin Jamila, sai muka sameta kwance a kasa rumgume da Amir tana rusar kuka, gaba daya ta hargitsa dakin ta watse tufafinta kamar dakin mahaukaciya. Mr Bashir ya karasa kusa da ita da sauri ya saka hannu ya dauki Amir.
“Akan me zaki dauki yaron mutane”
Sai ta tashi da sauri ta rumgume kafarsa ta fashe da kuka.
“Ka yi hakuri dan Allah, ka yafe min mijina”
“Ni ba mijinki ba ne a yanzu, kuma ki yi gaggauwar fice min daga gida tun kamin raina ya kara bace”
Martanin da ya maida mata ne na fahimci cewar sakinta yayi, ban san yadda saki yake ba ba a taba domin ba a taba min ba, amman na ji babu dadi musamman yadda take ta kukan nan akwai matukar tausayi, kamar ta san tausayinta ne ya cika min zuciya sai ta juyo gurina tana rokona.
“Zahra ki yi hakuri, ki ce yayi hakuri ya yafe min”
“Ba zan iya cigaba da zama dake ba Jamila, ko da na zauna da ke zuciyata ba zata sake natsuwa da ke ba, zan yi ta dubanki da wannan abun ne”
Mr Bashir ya fada sannan ya miko min Amir.
“Ga danki, hakan kuma ba zai hana na kyautata miki kamar yadda na yi alkwari ba”
Sai na tara hannu biyu na karba ina hawaye.
“Akwai kyautatawar da ta wuce wannan ne? Ni ka gama min komai tun da ka zabi rufa min asiri a lokacin da nake tsoron bayyanarsa”
Uffan be sake cewa ba ya dauke kai ya fice daga dakin. Ummiter kuma ta zo gabana ta tsaya tana kallon Amir ta kalleni
“Dan ki rufa asiri karki fadawa kowa abun da ya faru, Saboda ba ma son sirrin nan ya fita, babban mutum kamar yayana ace haka ta faru da shi ba zamu jidadi ba”
Ta juya hawaye na sauko mata ta fice daga dakin, sai ya rage daga ni sai Hajiya Jamila dake kuka ni kuma ina hawaye.
“Saninki be yi min rana ba Zahra, gashi yanzu zamanki a nan ya haifar min da ciwon da na dade ina tsoron ya kamani, da ace na san da zuwanki a gidan nan ba alheri ba ne, da na bar yaron nan a yadda yake ko kuwa idan ya sha nono mutuwa zai yi, da yanzu duk wannan be faru ba, da ban rabu da mijina ba, da yanzu asirina be tono ba, daman can kin ba ni dan ne ba da zuciya daya ba, shiyasa komai yake faruwa”
“Kaico yanzu duk abun nan da ya faru be isa ya saka ki nadama ba? Baki fahimci kin aikata kuskure ba balle har ki tuba? Sai neman kakabawa wani laifi kike? Ashe ke din ba abar tausayi ba ce, na yi kuskure da tausayinki ya darsu a zuciyata a yanzu, Wallahi kin cutar da mijinki kin haifar masa da bakinciki da damuwa marar misaltuwa kuma ya kamata ki gane haka”
Kamin ta sake ce min komai na juyo na fito ďakin rumgume da Amir, har na iso BQ ban daina kallon ďana ba ina shiga da shi dakin sai ya fara kuka sosai har wani fisga yake. Mama dake karyawa ta dago tana kallonmu.
“Yau kuma ta barki kin taho da ďan?”
“Mama Amir ya rabu da Jamila da mijinta a yau, ya dawo a matsayin ďana na asali, Mr Bashir ya mallaka min shi”
A take Mama ta tsame hannunta a abincin da take ci ta mike tsaye.
“Miya faru?”
“Ya saki Jamila, saboda ya gane gaskiya tun da dadewa amman ya saka mana ido ya ga iya gudun ruwan mu, ya tambayi labarina na fada masa komai na rayuwata sai ya biyo min da abun da na aikata, shi ya nemi na fasa auren Sauban indai saboda tsoron tonuwar asirina ne har ya bukaci aurena a yanzu kuma da komai ya faru, sai ya mallaka min ďana kuma ya zabi rabuwa da matarsa”
Mama ta saka hannu ta karbi Amir idonta na cika da hawaye.
“Hukunta ki zai yi kenan?”
“Aa yace ba zai yi komai ba, domin abun kunya ne a gurinsa, Mama tausayinsa ya kama ni, ban ga wani mutum mai hakuri da kawaici irinsa ba, wata kila da zai yardar da karbi Amir a matsayin ďansa ina da tabbacin zai rike shi amana”
“Su kuma iyayen Deen ki yi yaya da su?”