Sashe 85
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Shiru yayi har sai da na dauka kiran ya tsinke ne, na cire wayar a kunne na duba sannan na sake maida.
“Hello”
“Ina jinki, bana son na ce miki ba ni da shi ne, na san idan na ce haka ba zaki yarda ba, kuma idan ma na hana ki zaki iya samu amman Zahra ki natsu akan abun da zai faranta ranki ya kwantar miki da hankali, i think tunanin Abiey ko kallon hotonshi ba zai kara miki komai ba sai damuwa, a yanzu babu abun da nake so kamar kwamciyar hankalinki”
Samun kaina na yi da murmushi ko a munafurce Sauban yake nuna min kulawa ya damu da ni kuma hakan ya faranta min rai a yau, ko ba komai ya nuna min kauna da hanyar nuna kulawarshi a kaina.
“Zan yi kokarin kiyayewa”
“Good ya kika tashi? And tell wannan mutumen ya miki fadan ganinmu da yayi a tare?”
“No be yi min ba”
“He got lucky da ace yayi miki fada ba za mu kwashe lafiya ba, domin ba zan yarda kowa ya rika saka min ke kuka ba”
Na yi murmushi.
“Yana da kudi fa ai ba zaka ita masa fada ba, kuma ya fika gaskiya domin kai ka tarar da shi a gidanshi kuma ka karya dokarshi”
“Idan baya son ganina a gidanki ya sallame ki mana dokarshi dokar banza ce tun da har ya aje kyakkyawar mace irinki”
Murmushin da ya kusan zama dariya na yi, ina ta saurarenshi har ya gama maganar da zai yi yayi min sallama, kiranshi na sauka na Dr Hamid ya shigo sai da na gyara kwanciyata sannan na amsa kiran sai ya sanar min cewar yana bangaren Hajiya Jamila na same shi a can, kamar wanda bata son motsa jiki haka na aje wayar na sauko saman katifar na fito waje, Mama na fadin na tsaya na karya na fada mata cewar ba zan dade ba. A bude na tararda kofar part din da alama an shiryawa zuwa, abun ka da marar gaskiya kamin na shiga cikin falon tsoro ya kamani domin na san ni da shi da Hajiya Jamila duk muna cikin wani yanayi ne mai kama da kwai da zarar ya fashe zamu kunyata ba mu san iya abun da zai biyo baya ba. Murmushin sa ne abun da na fara yin arba da shi, Hajiya Jamila tana zaune a kujerar dake fuskata ta shi fuskarta ba yabo ba fallasa.
“Karki tashi hankalinki ba laifi kika yi ba, na ga tsoro a tare da ke wani albishir na ce ni zan miki shi da kaina”
Cikin rashin fahimta na karasa na zauna. Sai da ya waiga ko'ina na falon ya tabbatar mu ne kadai a falon sannan yayi kasa da murya ya ce.
“Dr Zainab ta mince ta karbi kudin kuma ta ba ni takardun yau zan maida nata da su, bayan na canja shiyasa na ce ni da kaina zan miki wannan albishir din kin ga sai ki kwantar da hankalinki ki sake yadda kike so a yanzu”
Ya san kwanciyar hankalin nawa domin wannan maganar na daya cikin abun da ya kwantar min da hankali a yanzu, fargaba be wuce ace watan tonuwar asirina ya kama ba, amman amincewar da ta yi zai sanya salama a zukantan mu, sai dai ban san miya na kasa murna da haka ba ina ta jin kamar ba mu aikata abu mai kyau ba.
“Ko ba ki yi farinciki ba ne Zahra?”
“Na yi murna mana na ji dadi”
Na fada ba domin na ji dadin ba sai domin na kare kaina, idon Hajiya Jamila yana kaina wani kalar kallo take min da ban san na minene ba, har sai da na soma tsawalla ina unkurin tashi na musu sallama Dr Hamid ya riga ni.
“Bari na tafi saboda ina da aiki da yawa yau kuma ya kamata na maida takardun hannun Dr Zainab kamin lokacin ya kure”
“Amman Yaya da zaka dan dakatar da zuwa domin na kura idon Hubby kamar yana kan mu bana son ya kula da yawan zuwanka ko kuma yawan kebewa da Zahra”
Dr Hamid ya kalleta.
“Ya miki wata maganar ne?”
“Aa lura dai na yi da hakan, ya kamata mu yi taka tsantsan dukanmu”
“Yeah you're right, zan kiyaye see you later”
Ya karasa yana kallona tare da sakar min murmushi, kofar da Dr Hamid ya rufe bayan ya fita falon bana tunanin ta gama rufuwa aka bude yar'uwarta dake can kusa da stairs. Mijin Hajiya Jamila ne sanye da kananan kaya da suka karbe domin ni ma kaina sai da na yaba yadda kyaushi ya kara bayyana a tufafi balle kuma ita da take matarshi. Da sauri ta mike tsaye ta nufi shi sai dai hakan be hana shi barinta ya karaso gurin Set din kujerun da muke zaune ba zauna a kujerar da Dr Hamid ya tashi, cikin hanzari na mike tsaye ina mika masa gaisuwa.
“Ina kwana Yallabai”
“An tashi lafiya”
“Lafiya kalau”
Na juya da zimmar ficewa sai ya kira ni.
“Zahra”
Na juyo sai dai ban yarda na kalleshi ba, duk kuwa da jikina ya ba ni cewar shi din kallona yake.
“Madam me kika shirya mana na breakfast?”
Hajiya Jamila da a yanzu ta karaso kusa da mijina ta amsa tana kallon yadda yake kallona.
“Mun makara ba mu barka da wuri ba, shiyasa ban dora komai ba Ummiter ma yau ba zata je aiki ba kai ma i thought bachi kake yi shiyasa ban girka komai ba, amman zan dora yanzu”
Ya daga mata hannu yana kallona ni ma kallonshi nake a munafunce ina dauke ido.
“No no ya kamata ki huta, bari Zahra ta shirya mana abun karyawa, Zahra kin iya girki?”
A take ido suka rain fata a duniyar nan ba abun da na tsana kamar ace min na yi girki ba dan bana son girkin ba sai dan ban iya ba, gudun na kunyata kaina ya saka na daga kaina har sau uku a na hudu na samu na iya furta.
“Eh na iya”
“Good the kitchen is yours now ki girka mana farfesu sai ki soya mana dankali bana cin kwai amman Matata tana ci ke ma idan kina ra'ayi zaki iya soyawa Ummiter ma tana so, and Wife ina ganin a maida girkin su tare da na mu gaba daya ba dole sai sun girka na su dabam ba”
Karashe maganar yayi yana kallonta kamar mai neman shawara.
“No ba zan iya ba, girkin mutum uku na ya nake yinsa balle na mutun biyar? Already ka zuba musu abin ci a store to miye na neman a hade abinci da masu gida?”
“Idan ba zaki iya ba Zahra sai ta cigaba da girka mana”
Ni kaina mamakinshi na ke balle kuma ita da mamakin ya bayyana a fuskarta.
“Excuse me, Hubby baka cin abincin masu aiki fa?”
Kallona yayi sai na yi saurin sauke ido kasa ina jin bugawar gaba.
“Wannan tana da tsabta kuma na ga kin aminta da ita, daman ni kazanta ce bana so a kula da tsabta kin ji Zahra”
Na daga mashi kai sannan na juya na nufi kofa sai ya sake kirana ina juyowa ya nuna min kitchen.
“Ki girka mana abu na ce”
Kamar a rikice na nufi kitchen din ina jin wani abu mai kama da kuka na neman hanya a idona, katon kitchen da komai a akwai a ciki wani abun ma ban san amfaninshi ba ban kuma san abun da ake da shi ba balle na san yadda ake kunnawa ko kashewa, ba abun da ya tsaya min a rai kamar dafa farfesu, har ga Allah ban san yadda ake yin farfasu ba domin ban taba yi ba, a gidan Ammy ma na ga ana yi ban tana tsayawa na kalli yadda ake ba, haka ma Mama da take girkawa wani lokacin ban san yadda take ba sai dai idan ta girka ta na ci.
“Farfesun ma na miye zan yi?”
Na tambaya kaina da muryar da kuka ke son ya ci karfinta, dankalin na fara gyarawa na kunna gas sannan na dora fraying pan na bude cabinet ina dubawa sai ko zan ga mai, daker na gano inda take aje mai na dauka an zuba, da na lura ba rawa ba tumame sai na cire hijab dina na aje gefe daya na takarkade ina ta soya dankalin sai da na yi kwasar farko, sannan na leka falon ban ga kowa ba daga ita Hajiyar uwar izza har mijin nata, sai dai idona ya sauka akan wayar dake hannun kujerar da Alhaji Bashir ya zauna, kafafuwan na sauko na fito daga kitchen din ina kallon stairs na karaso gurin wayar kamar na kai hannu na dauka sai kuma tsoro ya kamani, na juya na koma kitchen din cikin tsanda.
“Idan ban dauko wayar ba kuma da me zan yi farfesun? Ko kuma na ce musu ba iya ba? Ai kuma dai da kunya ace ban iya ba, to ko dai na tafi na dauko tawa wayar? Kuma ai ba ni da data, ko kyma na kira Mama ta zo ta girka musu?”