← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 127

Sashe 58

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya miko min dariyar ya dauki dari biyu daman dari bakwai ne Mama ta ba ni, ban iya tsayar da kuka na har na shiga cikin gidan, na samu unguwar babu wutar nepa hakan ya taimaka min na shiga cikin gidan ba tare da kowa ya lura da halin sa nake ciki ba. Ina shiga dakin na samu Mama tana sallah isha'i sai na zauna a kusa da kofa na jingina da ginin na dafe zuciyata ina jin kamar na mutu na hutu, ji nake kamar na yi bankwana da Abiey kenan bankwana irin na wanda zai mutu ya barka, kuka na ke sosai marar sauti numfashi na yin sama kamar zai rabu da jikina, ba hawaye ba har majina zuba take min balle hawayen da nake jin kamar domin ranar yau kadai aka yi min su. Mama na gama sallah ta dauki fitila ta haska fuskata.

“Zahra lafiya?”

Na kasa magana sai kuka nake marar sauti ina jan nunfashi da mugun karfi.

“Mi Malam yayi miki? Wata maganar ya fada miki?”

Na kasa magana domin na tabbatar idan har na bude bakina kuka ne kawai zai fito min. Mikewa ta yi ta dawo kusa da ni tana kallon fuskata.

“Fada min mana, wannan abun ya isa haka, ba zan dauki cin mutunci ba saboda yana a matsayin magabacinku ba shi yake nufin ya wulakanta ku ba”

Ta mike tsaye ko bata fada min ba na san ba zai wuce tace zata tafi gurinshi ba, sai na rike kafarta ina girgiza mata kai domin abun da zan iya yi kenan a lokacin nan, dokowa ta yi ta rika fuska.

“Bude baki ki yi min magana”

“Ba... Ba... Ba... ”

Na kasa fada kuka ya ci karfina jikin ko'ina rawa yake, sai da na yi da gaske sannan na iya furta

“Abi....ey ne....”

Maganar na yankewa kukan yana karuwa.

“Mutuwa ya yu?”

Na girgiza mata kai alamar aa, zaunawa Mama ta yi kusa da ni ta rumgume hakan ya bude min kofar wani sabon kuka marar misaltuwa, har wani kara numfashi yake gurin fita, a daren kam kuka be tausayawa idona ba tun ina yi da kuzari har na ji jikina ya zama kamar kaďa.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un Allah ya dauke miki wahala Zahra ko na mutu iyar kukan da zaki yi kenan”

Mama ta fada tana kokarin tare nata kukan daman tuni hawaye suka wanke mata fuska, sai da na yi kukan sosai na gaji sannan ta daga ni jikinta ta fita ta debo ruwa ta saka cire min hijab ta cire dankwalin kanta ta saka cikin ruwan ta matse ta daga rigata ta saka min saitin zuciyarsa sai naji rahama, ta sake natsewa ta saka min goshi sannan ta share min majinar ta share hawaye.

“Zahra na hada miki ruwa ki yi wanka?”

Na daga mata kai na kara matsawa kusa da ita na dora kaina saman cinyarta na runtse ido zuciyata na min ciwo sosai, sai da bachi ya fara daukata sannan ta dauko filo ta saka min a kasan kai ta tashi ta fita, can cikin bachi na ji Mama na tashi na sai na bude idona da suka kumbura na tashi zaune.

“Ga ruwan zafi can na dora miki a gidan Maman Mufeedat kuma na bada an siyo miki tea ki sha kin ji Auta ta”

Ta miko min kofin shayin sai na karba na kafa kai na sha, sannan na cire tufafina na daura zane na fita na dauki ruwan dake da ďan dumi na shiga bandaki na yi wanka, ko da na dawo Mama ta zuba min shimkafar sai dai ban iya ci ba kaina sai ciwo yake kamar zai tsage, ban iya bachi ba har sai dai Mama ta fita ta samo min magani na sha. Nan da nan bachin wahala yayi gaba da ni, ban farka ba sai safe shi na sai da Mama ta tashe ni, wanka na fara yi sannan ta zuba min kokon da aka kawo mana, na sha kadan Mama kuma ta ci dumame, abun da ya faru ya zame min kamar mafarki.

“Ko na siyo miki tea”

Na turo baki gaba na kwanta jikinta cike da shagwaba.

“Ni bana ci”

“To ya jikin na ki?”

“Da sauki”

Ta kai hannu ta taba ni.

“Miya samu Abiey?”

“Ba Abiey ne...”

Na fada a shagwabe ina kokarin dora mashi laifi kamar ba ni na bukaci haka ba.

“Miya faru?”

Kamin na gama bata labarin ma wani aiki ne domin kuka ya gama cin karfina har ya tafi da kuzarina.

“Indai saboda ni ne Zahra da baki aikata haka ba, na san mutane za su yi gulma kuma dole a dora miki laifi amman idan bera da sata daddawa ma sa wari, laifin ba naku ba ne ku kadai har da na Malam sai dai dole ne a fi dorawa Abiey laifi domin shi kamar suruki yake a gurinmu dole ne ko zaginshi muke yi kullum idan yana kaunarki ya hakura ya jure, sai dai ina ganin kamar abun be kai ki yankewa kanki wannan hukuncin ba, saboda zaki iya cutar da kanki kuma shi ma zaki cutar da shi domin na tabbatar yana kaunarki sosai”

Na gyara hancina wasu hawayen na sauko min.

“Ba saboda ke da Baba kawai na yanke wannan hukunci ba, har dan saboda Ammy da Mai Martaba, tun kamin na fahimci gaskiya Ammy ya fada min cewar Mai Martaba ya zaba mashi mata, kuma jiya ma ta kara tabbatar min da haka, Mama na san irin yadda Mai Martaba ya tsani Abiey Abiey kuma yana ta neman mafitar da zata aadashi da mahaifinshi, yanzu kuma ya samu har Mai Martaba ya nema mashi aure da kanshi ba zan yarda na zama sanadiyar lalara wannan alakar ba, kuma Ammy tace min idan har ya zabi zama da ni su kuma za su yafe shi, Mama bana son na zama silar shiga tsakanin ďa da uwa, kuma ban ga laifinta ba, domin kowa uwa tana nemawa ďanta mafita ne da farinciki ina ganin kamar idan mun auri juna ba lallai mu samu farinciki ba, saboda akwai rashun jituwa tsakaninshi da Baba ni kuma zan samu tsakani da Ammy ina ganin kamar hakura da juna shi ya fi”

Mama ta yi murmushi ta shafa fuskata.

“Kin yi tunani mai kyau Zahra, kuma fatar hakan ya zama silar samuwar farincikinki, Allah ya sa haka shi ne alheri a tsakaninku kuma yayi muku mafita dukanku”

“Ameen Mama”

Na fada ina kara fashewa da kuka, nan wata duniyar kukan na gina sai da Mama ta rarrashe ni sannan na yi shiru na kwanta akan tabarmar da muka kwana a jiya. Misalin tara na safe Yayanyun mahaifiyata da kanenta suka shigo na gaishe su na koma na kwanta, ina ta sauraren hirar da suka da Mama yawancin su Abiey suke dorawa laifi wasu kuma Mama domin a ganinsu ita ta bar ni na fita alhalin ina cikin jego. A nan take labarta musu cewar tana son zata kama haya babu wanda ya bata goyon baya suna ganin kamar be dace ta bar gidan ta je ta kama haya a wani gurin ba.

“Ba zan kama inda zan zauna ni kadai ba, amman dai na fi son na kama hayar ko dan Zahra da bata gama wanka ba, ba zan zauna ace kullum sai na je kofar wasu na dora ruwan zafi ba, ko kuma idan zan dafa wani abu ko ita na dafa mata sai na je wata kofar ba, kuma ďakin nan ba gyaren ba ne bandakin ma sai ka zagaya a na mutane ai dai ba haka ake so ba, kenan miji ya fi miji kyau”

“To ai zaman da zaki yi ba wani mai dade ba ne, domin fatan a gyara muke ba wai a yi ta zama a haka ba, na san idan an kwana biyu ya huce zai nemi ki”

Cewar wani kanenta sai ta yi murmushi ta ce.

“To ko da za a koma din ai ka ga na samu muhallin zama, ba sai yayi wahalar nema ba, ni dai kam da zaku yarda ku bar ni da na saba da wacan unguwar sai na kama hanya a can mu zauna”

Ganin ta dage yasa suka amince mata ta kama hayar a can, ni kaina zan fi jindadi zama a can sama da irin wannan gidan da yake na iyalai wani lokacin akwai ganin laifi da gulma kara dai gurin da kake zaune kai kadai ko kuma da wasu da ba yan'uwanka ba. Sun dade suna hira sannan suka fita Mama ma fita ta yi ta shiga bangaren Matar kanenta ta yi wanka ta dawo ta shirya a dakin.

“Akwai abun da za a dauko miki a can? Zan tafi na dauko wasu kayan na mu kuma na fadawa Malam Zubairu ya nema mana gidan haya a can unguwar”

“Babu abun da za a dauko min”

Na fada ina ta jin haushin mutane da zarar na tuna abun da ya faru a daren jiya sai na ji kuka na kwankwaso min kofa, sai faman sharar hawaye nake musamman ma da Mama ta fita sai ya zamana ni kadai ce a dakin hakan ya bani damar fashe kurjin kukana na tausayawa kaina, idan na ji motsin matan gidan kamar za su shigo sai na fake na yi kamar bachi nake. Daga Maman Mufeedat har Matar Kawu Bala da suka kawo mana abincin rana ba su ga fuskata ba. Mama kuma bata dawo ba sai kusan la'asar ina jin sallamarta na tashi zaune ina jiran ta shigo na yi mata nata kukan na tafiya ta bar a ni kadai a ďakin domin a yanzu laifin kowa nema nake na rasa abun da yake min dadi.

“Zahra kina nan ďaki har yanzu”

Sai kawai na fashe da kuka.

“To Mama ba kin tafi tun safe sai yanzu kika dawo kin bar ni ni kadai kuma kin san ba wani guri nake zuwa ba kuma ba sabawa na yi da gidan nan ba”

Tsayawa ta yi tana kallona daman can ta san ni da shagwaba sai dai bayan na yi aure Shagwabar ta koma gurin Deen.

“To ba ni kadai na dawo ba, tashi ki wanke fuskarki”

“Da wa kika zo?”

“Hajiya Jamila gata nan kofar ďaki”
Chapter 58 · 0% Book details