Sashe 59
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ban san lokacin da na zabura na tashi tsaye ba.
“Mama Hajiya Jamila kuma? Mi ta zo yi a nan? Mama kin san gidan family ne fa miya sa zaki zo da ita?”
“Na je can ina cikin unguwar sai gata ta zo, kuma ta matsa tana son na kawo ta gurinki na nuna mata ba zan yi haka ba, amman ta dage tana son ta yi magana da ke”
“Mi zan mata?”
“Shiyasa na zo da ita, sai ki ji bakinta”
Mama ta leka ta ce ta shigo, sai ga ta shigo dakin tana sanye da dogon hijab har kasa fuskarta da mask hannunta rike da makullin mota, hannu ta saka ta cire mask din tana kallo na fuskarta abun tausayi idonta har ya fada kamar wanda ta yi kuka ko kuma ta kwana da ciwo.
“Zahra...”
Ta kira sunana ban amsa ba.
“Na san zaki yi mamaki ganina a nan ko?”
“Ki yi saurin fadar abun da zaki fada a gidan taro muke kuma wannan ya zama karo na karshe da zaki shigo gidan nan”
“Toh daman na zo ne akan maganar mu”
Yanayin yadda take maganar sai ka rantse da Allah masinja ne yake magana da ubangidanshi.
“Na ce zan yi shawara ai”
Ta matso kusa da ni sosai ta kama hannuna sai ta fara hawaye.
“Zahra ina cikin babbar matsala, asirina zai iya tonawa idan baki koma kin cigaba da shayar da yaron nan, akwai barazanar rasa rayuwarshi, kuma asirina yana gaf da tonuwa, tonuwar asirina na nawa ba ne ni kadai har da ke da Dr Hamid”
“Miya hada ni da tonuwar asirinki?”
“Saboda Mai gidana ya dage yana son a kai yaron asibiti a duba lafiyar shi, kuma hakan zai iya sakawa a gane cewar ba ďanshi ba ne, idan kuma ya gane gaskiya zai iya hukunta ni da ke da Dr Hamid, sannan aurena mutuwa zai yi kuma shi ma yaron zamu jefa rayuwarshi cikin wata matsala, mijina ma zai shiga damuwa sosai, amman idan kika yarda kika koma a gidan ki ka cigaba da shayar da shi babu wanda zai gane, kuma kin ce ci rayuwata da ta mijina da taki da ta yaron da kuma ta Dr Hamid...”
Na kalli Mama sannan na sake kallontabna girma mata kai ina bude baki kamin na ce komai ta yi saurin durkusawa masa ta kama kafafuwana tana kuka sosai.
“Ki taimaki rayuwata Zahra dan Allah ki rufa min asiri ki fada min ko nawa kike so zan biyaki, dan Allah ki taimaka min, Ki tausayawa yaron nan shi kanshi abun tausayi ne ya zai ji idan ya bude ido ya ga abun da muka aikata? Da wane idon zaki kalleshi? Kuma dukanmu zamu jefa rayuwarmu cikin hadari kuma duniya zata ji abun da muka aikata, za mu kunyata Zahra karshenta mu kare rayuwa a gidan yari, Mama ki sa baki dan Allah”
Ya juya gurin Mama tana kuka sosai kamar ba ita ba, daga ni har Mama mamanki ta muke.
“Idan na koma a can me zan fadawa mutane? Ba zan iya ba gaskiya”
“Babu wanda zai gane a yanzu saboda gidanku da aka rusa Mama ta fada min abun da ya faru, ina son ku koma gidana da zama a akwai BQ zaku iya zama a can kin ga mijina ma ba zai gane ba, kuma nutane ba za su yi zargin komai ba, na miki alkawari idan kika gama shayar da yaron zan siya miki gidan da za ku zauna, kuma zan baki enough kudin da zai taimaka muku, kuma ki fadi ko nawa kike so a yanzu zan baki”
“Duk da haka dai ina bukatar shawara”
“Zan barki ki yi shawara Zahra, amman ba tafiya zan yi mai nisa ba, zan je na zauna a mota na jiraki dan Allah ki tausaya min kar na rasa ďana da mijina”
Wani irin kuka take sosai har gabana faduwa yake kar wani ya ji kukanta ya leko ya same mu a wannan halin.
“Dan Allah ki tashi ki tafi kar wani ya shigo ya same ki a nan”
“Idan ma ba a same ni a nan yau ba, za a same ni a gobe da jibi har sai Allah ya saukar da tausayi a zuciyarki kin amince da bukatata, Wallahi da kin san mawuyacin halin da nake ciki da kin tausaya min, rashin haihuwa masifa ne shi yaja min komai”
Ta mike tsaye tana share hawayenta ta fice, daga ni har Mama da kallo muka bita, ko da karya Hajiya Jamila take ta yi nasara akaina domin kuwa tausayinta ya kama ni, kamar yadda na ga tausayinta a fuskar Mama.
“Mama ban san miyasa kika kawo a nan ba, yanzu damu na zata fara yi har sai asirina ya tonu”
“Irin magiyar da take miki yanzu tana kuka irin ta ta yi min a can kofar gidan mutane, tausayinta da kuma gudun zargin mutane ya saka dole na amince na kawo ki gurinta, kuma idan har baki son tonon asiri dole ne ki amince da abun da take rokonki domin idan mijinta ya gane gaskiyar siyen yaron nan ta yi zai daureku daga ke har ita, kamin ayi bincike a gano mai gaskiya har a fitar da ke kin kunyata a idon duniya kuma kin yi zaman gidan yari, Hajiya da duk wanda be san komai ba zai sani, kuma ba za su dubi abun da kika yi a matsayin taimako da ceto rai ba, za su ce da gangan kika aikata, labarin ki zai yadu a ko'ina wata kila har ya shafi Abiey, kuma idan kika taimaka ke ma kin ceto rayuwar ďanki ba wai ita kadai kika taimakawa ba, kuma a irin wannan lokacin kike da damar taimako domin idan har muka riga muka kama haya ba zai yiyu mu bar gidan mu koma wani guri da zama ba, kuma zai yiyu ki koma can da zama ba, amman a yanzu babu wanda zai zargi wani abu domin kuwa rufin asirin ba nata ba ne ita kadai har da ke, a halin yanxu idan asiri ya tonu daga Malam har Hajiya sai sun maka ki kotu akan kin siyar musu da ďa kin musu karyar ya mutu”
Na kalli Mama cikin yanayi na damuwa.
“Idan kuma muka koma gidan wata matsala ta faru fa?”
“Ba na fatar haka, kuma ina fatar nan ba da jimawa ba Allah ya baki mutumen kirki ki aura ki cigaba da rayuwarki a gidan mijinki ita kuma ta cigaba da na ta rayuwar”
“Amman yanzu me zamu fadawa mutane?”
“Mai sauki zan ce wata mata yayar kawarki ce da ta ji abun da ya faru sai ta ba mu muhalin zama a gidanta kenan babu wanda zai makuri ni akan sai na fadi gaskiya, amman ba zan cilasta ki ba idan har kina ganin zaki takura kanki ne ko kuma saka kanki a cikin wata matsalar karki amince, ni ma na fada ne kawai saboda ina ganin hakan shi ne mafita a gurin gaba daya”
“Amman Mama idan aka shirya aurenki da Baba ya zamu yi? Kin san ba lallai ya yarda ya zauna a can ba”
“Idan ma be zauna acan ba, ai dole ya kama min haya domin ba shi da wani gida da zai aje ni a yanzu sai wanda yake ciki tare da Hajiya shi ma kuma na haya ne ba na shi ba, idan ma na dawo mun zauna a wani gurin shi ma mafita ne domin a gidan Hajiya Jamila zan barki ki cigaba da zama har sai yaron yayi kwari albashi idan mutane suka tambaya sai na ce ita Hajiya Jamila ta bukaci na barki a can, ko ya ta kama mafita ce a garemu Zahra”
Na zauna akan tabarmar ina nazarin maganar Mama, tabbas tana da gaskiya ta wani bangare amman ina tsoron halin Hajiya Jamila tun tafiya bata yi nisa ba ma ta fara wulakanta ni a gidanta balle kuma ace nan gaba! Na san tana cikin matsala sosai tun da har ta iya dukawa har kasa tana rokona tana kuka, idan ma zan yarda na zauna a gidan sai da sharadi da kuma yarjejiyar abubuwan da tace zata yi min kuma ba zan shayar da yaron a kyauta ba sai ta na yanka mata albashin da zata rika biya duk karshen wata.
[11/7, 11:12 PM] Oum_Nuwaira🥰: 4️⃣1️⃣
Ban yi zaton da gaske take a waje zata jiramu har mu yi shawara ba sai da na ga ta dawo cikin gidan. Wannan karon idonta a kumbure yake sosai da alama zaman jiran mu da ta yi a motar ma kuka ta yi, yadda ta shigo cikin ďakin sai ka rantse da Allah ba za a saka mata yatsa a hannu ta ciza ba sumi sumi da ita abun tausayi.
“Allah yasa kar na yi mummunan ji dan Allah Zahra ki amince da kudirina ki taimaki rayuwata dan girman Allah”
Na kalli Mama Mama ta kalleni sannan ta kalli Hajiya Jamila ta ce.
“Zauna Hajiya”
A take Hajiya Jamila ta zauna kamar daman can umarni kawai take jira, hankali a tashe take kallonmu na san fargabar ta ba zai wuce na tsoron kar mu ki aminta da kudirinta ba.
“Na yi magana da Zahra ko kuma na ce mun yi shawara kuma Zahra ta amince da bukatarki, amman bisa wasu sharuda da zan gindaya miki yanzu nan”
Hajiya Jamila ta tattara hankalinta gaba daya ta maida gurin Mama ni kaina kallon Mama nake domin ban san sharudan da take magana akai ba, na sai dai na ce ni ma ina da nawa sharadin amman ban fada mata ba a zuci na yi maganar.
“Ina jinki Mama”
“Na farko ba zan dauki ki wulakanta min ya ko ki ci mutuncinta ba, na biyu a duk lokacin da yata tace zata daina shayar da ďanki zata daina ko da kuwa ba ki so haka ba a wannan lokaci, abu na uku Zahra zata shayar da yaron ne a matsayin yar raino saboda haka dole ne duk wata ki biyata naira dubu ashiri, babu barazana ko kulla wani makirci a tsakaninki da ita”
“Shikenan sharadin ki Mama?”
“Eh kuma zamu yi haka ne a rubuce kamar yadda kika wacan yarjejeniyar a rubuce”
“Na yarda”