Sashe 71
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na sauke kaina kasa ina jin hawayen idona na kafewa saboda tsoro, ashe ba komai ake iya yi ma kuka ba, muna a wannan halin Hajiya Jamila ta shigo dauke da tray ta aje a gaban mijinta.
“Na fada miki ki rika hutawa mana, wani lokacin ki rika bari Zahra tana girkawa ko tana wata hidimar so that ke kuma ki samu hutu idan kuma wata mai aikin za a dauko miki sai a karo”
Kallon da yayi kama da na mamaki ta yi mashi.
“Hubby kai da na san baka son mai aiki?”
“Na lura kamar Zahra tana da tsabta ba kamar yadda nake tunanin sauran yan aiki suke ba”
Na dago na kalli Hajiya Jamila.
“Aikina kula da Amir ne kawai ban zan iya wani aikin bayan wannan ba, ni ban ma iya girki ba”
Hajiya Jamila ta kalleni ta sake kallon Mai gidanta.
“Hubby wani laifi ta yi aka kirata nan?”
“No na kira ne na fada mata cewar ina son gobe ta je asibiti a auna jininta saboda an ce hepatitis ya kashe mijinta so that mu tabbatar bata dauke da shi kuma bata sakawa Amir ba”
Da ace dan'adam zai iya shiga zuciya ya ga tashin hankali da take ciki wata kila da za a ga tashin hankalina da na Hajiya Jamila zai iya cika duniyar nan, musamman ni da nake ganin kamar na fi kowa laifi domin ita zai iya yi mata da sauki kasancewarta matarshi tsabanin ni, Hajiya Jamila ta zauna kusa da shi da sauri ta dafa shi.
“Amman Hubby kamin a kawo ta nan sai da na bincika komai nata lafiyarta, wacece ita da duk wasu abubuwan bata dauke da cutar komai”
“Ina son na kara samun natsuwa da ita ne, gobe likita zai kaita asibiti a duba lafiyarta daman can ya kamata na yi haka tun kamin ta fara kula da Amir”
“Haka ne wannan ba matsala ba ne zan kira Dr Hamid na sanar mashi”
“Dr Hamid is not our family Doctor, Dr Zainab zata duba su”
“Su? Ita da wa?”
“Ita da Amir”
Ya fada kai tsaye yana kallonta tashin hankalin dake fuskarta irin shi a fuskarta jiki yayi sanyi gaba daya.
“I thought i didn't tell you that, Zahra don't tell har kun yi shakuwar da zaki zauna kina ba mijina labarinki da rayuwarki”
Ta tambaya tana kallona kamin na ce komai ya amsa mata.
“Na dan tambaye ta few things ne ta fada min you can go Zahra”
Na mike tsaye ina kallon yadda ya daure ni a gaban matarshi da cewar na fada mashi cewar mijina yana da hepatitis alhalin ban san inda ya samu labarin ba, Hajiya Jamila kuma ta watso min wata uwar harara da na tabbatar idan muka kebe ba karamin cin mutunci zata min ba.
[11/14, 7:36 PM] Oum_Nuwaira🥰: 4️⃣7️⃣
Ina shiga BQ kamin na labarta ma Mama komai na dauki wayata na kira Sauban na sanar da shi gargadin da Alhaji Bashir yayi min.
“Miye matsalarshi da zuwa na gidan?”
“Baya son ganin kowa a gidan shi daman na fada maka ai masu kudin basa son shisshigi, daman ina ta jin tsoro gashi nan kuma ya gani har yayi min magana”
“Saboda ya gani ko yayi magana ba zai saka na daina zuwa gidan ba, Zahra idan kika ga na dauke kafata a gidan to kin bar gidan ne”
Na mike tsaye ina nuna gina kamar yana gabana.
“Sauban bana son matsala na gargade ka tun yanzu, ina ce saboda ni kake zuwa yanzu kuma bana son zuwanka ai akwai waya”
“Waya ba zata wadatar ba Zahra dole sai ma ganki”
Na kashe wayar na kalli Mama girar sama da ta kasa a hade. Kamin na ce komai wayar ta yi ringing da sauri na yi picking ganin Sauban ne.
“Ki fada mashi idan baya son ganin baki a gidanshi to ya sallame ki”
“Bana son abotar na fasa”
Na fada ina zare ido sai ji na yi ya saka dariya.
“Now i understand why Abiey yake son ki, dan zaman da na yi da ke na fahimci abubuwa na rayuwarki”
“Ni dai na fada maka kuma ka zo ka karbi wayarka idan har ba zaka ji magana ta ba”
“A matsayinki na wa zan ji maganarki? Kin ba ni shekara nawa?”
“A matsayina na kawarka”
“Ai kin ce ba ki son abotar ko kin manta? Kuma zan so na karbi wayata da duk wani chocolate da na taba baki”
Na yi shuru ina tunanin da gaske yake ko wasa dai.
“Ai ba ni nace ka ba ni ni ban taba cewa ka bani abu ba, dan haka ba zan biya ba”
Na kashe wayar, na kalli Mama dake kallona da mamaki a fuskarta.
“Ke dai kam ba zaki girma ba Zahra, sai na ga kamar kin yi wayo kuma ba wayon kika yi ba”
Na turo baki gaba na zauna kusa da ita.
“Toh Mama ba ki ga mijin Hajiya Jamila yana min fada ba wai kar ya sake ganina da kowa a gidan nan, kuma har yace wai zamu je ayi gwajin jini ni da ďanshi Mama ke kika fada mishi na aure mai hepatitis?”
Mama ta bude baki tana kallona.
“Ikon Allah Zahra Ina zan ga mijin Hajiya Jamila har na fada mashi haka? Ba dan dake da wautarki ba, kuma dai ko na ganshi sai na zauna na bashi labarin abun da ya kashe mijinki?”
“To a ina ya ji?”
“Waya sani, amman yana babbar magana ce ina ya ji labarin nan? Ko dai ita Jamilar ce ta fada mashi”
“Ba ita ba ce kuma ya hada ni fada da ita yace da ita wai ni na fada mashi, yace gobe zamu je gwani ni ba zan je ba, idan anje gwaji aka ce jinina daya da ďanshi sai ya saka a kamamu”
“Toh ko dai ya gane gaskiya ne?”
“Idan ya gane Mama ba zai bar mu ba, da yanzu ya rufe mu, amman dai ina ganin mu gudu kamin ya gane”
“Mu gudu muje gurin uban waye? Duk ba rashin tunaninki ne ya janyo komai ba, ga makiya ki sake saka mu a cikin wata masifar kin san dai Hajiya da Malam ba za su kyale ki ba”
Na dora hannu a saman kai.
“Ni dai yau na shiga uku, Mama ya zan yi to?”
“Ya zaki yi dole ki je a dauki jini ainita Jamilar dole ta nema muku mafita, wata kila ma yayanta zata saka ya auna jini”
“Tace haka yace mata aa wai Dr zata auna”
Har lokacin kuka nake ba hawaye tashin hankalin dake zuciya ya cika har yayi yawa, haka dai muka yi ta tattauna maganar da Mama har muka ji sallamar Hajiya Jamila jikina na rawa hantar cikina na kadawa na fito domin bayan ta yi sallama sunana ta kira bata shigo dakin ba, a tsaye na same ta tana jirana ina isowa kusa da ita ta kama hannuna ta matsa nesa da kofar BQ din wata kila bata son Mama ta ji.
“Akan me zaki fadawa mijina cutar da ta kashe mijinki? Tambayarki yayi? Kuma ko tambayarki yayi ai kamata yayi ki boye, ba wai ki sake baki kina ta zuba ba, gashi nan yanzu kin janyo mana wata matsala”
Ni dai na yi shiru to me zan ce, ko da na fada mata ba lallai ta yardar ba kuma ba zan iya karyata mijinta ba, haka dai na yi shiru ta yi ta fadanta har ta gaji ta yi shiru, bayan ta gama fadanta ta shige bangarenta ni kuma na dawo BQ a nan kuma Mama ta rufe ni da wani fadan wai miyasa ban fada mata gaskiyar cewar ba ni na fadawa mijinta komai ba. Haka na kwana cikin bacin rai washe gari ma ana gama sallah asuba muka ji an bude gate din gidan, ni dai ban leko ba domin ba aikina ba ne kula da wanda zai shigo ko ya fita, ba a dade ba na ji muryar Dr Zainab tana mana sallama a dayan bangaren kuma tana hira da mijin Hajiya Jamila, ina jin sallamarsu na koma bachi karya Mama ce ta amsa ta tashi ta leka waje ta gaisa da shi.
“Zahra na nan?”
“Eh ranka ya dade amman bachi”
“Yauwa haka na ke so, a tashe ta please”
Ina jin haka na yi zumbur na tashi zaune.
“Mama dan Allah ki ce na suma”
Na roka kamar na yi kuka.
“Tashi ki je ana kiranki ba zan yi karyar komai ba, ki daina jin tsoro idan ma kina da laifi ai ita Hajiya Jamilar ta fi ki laifi, wata kila ma wannan ta san Dr Zainab zata iya rufe mata asiri tare take da ita saboda haka ki tashi kawai ki tafi”
“Amman Mama Dr Zainab zata fada ma Abiey kuma zata san gaskiya”
Ina maganar hawayena na zubar min a ido, haka na tashi cikin tsoro cikin kuka Mama na min fada na natsu na daina kuka amman ko saurarenta ban yi ba na fita a haka.
“Lafiya kike kuka?”
Dr Zainab ta tambaya.
“To ba jinina za a dauka ba na sani ai”
“Daukar jinin shi ne abun kuka kamar za a cire ranki”
A cewarta tana dariya, ni dai kukan kawai nake, Mijin Hajiya Jamila kuma na tsaye gefe daya ya maida hannayenshi baya yana kallona uffan be ce ba.
“Na rantse da Allah an auna ba ni dauke da cutar Wallahi Wallahi”
Har kasa na kai ina mashi rantsuwar an gwada ni ba ni dauke da cutar.
“Zahra ba wai yace kina dauke da ita ba ne, kawai za a sake gwadawa ne, daman yana da kyau ko baka dauke da cuta ka je a gwadaka, kuma be kadai za'ayi ma wannan ba, kin ga jinin ďanshi da na matarshi ma an dauka, daman an fi son kamin a ci komai”