Sashe 4
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Anty ta yi shiru fuskarta na nuna tsananin damuwa domin ita ma kanta har ga Allah bata so sai dai bata iya musawa Mama Lami duk abun da tace shi za'ayi, tana matukar tsoron ta kamar uwarta.
“Toh ni yanzu da kika fada min me kike so na yi? Na cilasta Narjis auren wanda bata so saboda tana jin magana ta? Ai ba ma mutuncin gidan nan ba ne da masarautar nan ace yar masarautar da ta auri dan Justice Umar, ba kudi muke nema ba balle ace zata auren shi saboda kudinsa, ba zan cilasta ba kuma matukar bata so Wallahi ba za'ayi ba, na san ni ba kowa ba ne a gurin Mai Martaba amman wannan karon abun ya isa haka”
Yana fadar hakan ya mike tsaye ya fice daga falon a fusace.
ZAHRA POV.
Duk yadda zan bayyana yadda mace take ji idan ta rasa miji sai na ga kalmomin kamar ba za su hadu su wadatu na isar fassarar yanayin ba, shiyasa wasu suke cewa mutuwar miji ta fi ta uba ciwo, sai dai ni a yanzu na kasa banbancewa tsakanin rashin uba da muka a shekarun baya da kuma rashin miji da na yi a yanzu. Musamman da dare yayi zan kwanta sai yanayin yadda muke kwance ya dawo min a rai, ko tufafinsa na kallo wani abun nake ji yana ta so min, sai dai fa kam hawaye Allah ya dauke min su, ba sakafai suke zubo min a ido ba idan dare yayi bana kwana sai na tashi na raya dare da addu'a ina rokon Allah ya yafewa mijina ni kuma ya bani juriyar cin jarabawar da na fada. A haka dai har aka yi sadakan uku a ranar kan na shiga tashin hankali sosai domin na tabbatar Deen ya tafi ya bar ni kenan har abada, ba laifi mun yi ta samun abinci daga abokansa yan'uwa da makota kowa yana ta kawo mana daidai gwargwadon hali, har mai gidan da muke haya sai da ya kawo mana abinci kuma yace idan muna bukatar wani abun na fada, duk wata soyayyar irin ta bahaushe da kuma dangantaka ta musulunci an nuna min ita sosai kuma na yaba domin ba ko wane musulmi ne yake samun irin gatan da na samu ba a cikin yan'uwan miji da makota na nesa da na kusa. Washe garin ranar da aka yi sadakan uku Jamila ta sake dawowa gidanmu, ban yi mamakin ganinta ba daman ta fada min zata dawo, yau kan gidan daga ni sai Bahijja ne a waje, Mama na daki tare da Yaya Maryam suna kintsa min dakin, Hajiya kuma tana gidansu gurin danginta saboda jinyar da take har yanzu jikin be saki da kyau ba,hakan yasa ana gama amsar gaisuwa sai yan'uwanta suka maida ita kusa da su saboda kar damuwar ta yi mata yawa....
Yau kan Hijab ta saka har kasa sai dai kamshin turaren da ta saba yi be canja kala ba, tun kamin ta karaso Bahijja ta janyo tabarmar dake kusa da mu ta shimfida mata sai ta zauna fuskarta da murmushi.
“Ya hakurin hakuri Zahra?”
“Alhamdulillah”
Ta kalli Bahijja.
“Wannan kanwarki ce?”
“Aa kanwar mijina ce”
“Allah sarki ya hakuri?”
“Alhamdulillah”
Bahijja ta amsa, sai shiru ya biyo baya idonta na kan cikina ni kuwa nawa suna kasa ina ta tunanin yadda zan fara yi mata magana.
“Allah yasa tare da Dr kuka zo”
“Aa ni kadai na zo, kina son magana da shi ne?”
“Aa”
Na amsa saboda kar Bahijja ta zargi wani abu, sai ta kalli Bahijja ta kalleni.
“Mama na nan zan gaisa da ita”
“Bahijja kira mata Mama”
Na fada ina shafa wuyata da kassafan wuyan suka gama fitowa. Bahijja ta tashi ta shiga falon, sai Jamila ta yi saurin matsawo kusa da ni.
“Me kike son magana da Dr akwai wata matsala ne?”
“Gani na yi an yi aikin ba a yi nasara ba, abun da ake kokarin cin ma be samu ba, ran da anke son na ceta be tsaya ba, hakan na nufin yarjejeniyar bata zauna ba tun da be rayu ba”
A take yanayin fuskarta ya canja tana min wani irin kallo na mamaki da rainin wayo.
“Lallai baki da hankali, ko mijinki ya rayu ko be rayu ba yarjejeniya ta zauna saboda kudi ya fita daga hannuna yaje asusun asibiti, kuma bari na tunatar da ke, karki kuskura ki bari wani likita ya duba ki ba Dr Hamid ba, haka ma karki yarda ki haihu sai a hannunsa, idan kuma kika saba yarjejeniya kin san abun da doka tace”
Hawaye na zubo min sai na yi saurin sauke kaina kasa, ita kuma ta daga da hikima tana kallon Mama da Yaya Maryam.
“Ashe kuna ciki”
Suka amsa mata suka zauna aka gaisa sannan ta yi musu sallama ta tashi har ta fice tana fadin Allah ya kara hakuri.
“Gaskiya Likitan nan yana da kirki ina jin shi ya turo ta yace ta zo ta duba Zahra, ya nuna tausayawa sosai”
Mama ta fada cikin jindadin yadda aka nunawa yarta kulawa, Yaya Maryam kan bata ce komai ba sai wani kallo take min mai kama da harara, na saka hannuna na share hawayen sannan na mikar da kafafuwana da suka kumbura.
ABIEY POV.
Be dawo gidan ba sai dare. Ko da ya shiga bedroom dinsa ya samu Ammy tana ciki tana kimtsa masa kayan da zai tafi da su.
“Yanzu da kana da mata ba ita za ta yi wannan aikin ba?”
Yayi murmushi yana zaunawa kusa da mahaifiyarsa.
“Ki yi addu'a Allah ya kawo”
“Addu'a ai kullum ina yinta, kuma ya kawo sai dai idan ba so”
Yayi murmushi.
“Matar ce ta aure har yanzu bata zo ba shiyasa ban ga wanda ta yi min ba, idan lokaci yayi ko wacece sai na aura”
“Toh Allah yasa, amman lokaci tafiya yake yi Aliyu baya jiran kowa kuma idan ya wuce ba zaka iya dawowa da shi ba”
“Haka ne, amman na Tambaye ki mana”
“Ina ji”
Ta fada ba tare da ta kalleshi sai kokarin rufe traveling box din take. Sai yayi shiru domin tambayar tana da nauyi sosai ko a gurinsa balle kuma a gurin Ammy.
“Wane irin tsabani kuka samu da Mai Martaba... Har ta kai ga kun rabu...? Kuma miyasa kuka tsani juna ke da shi?”
Juyowa ta yi ta kalleshi a take yanayin fuskarta ta canja.
“Miyasa ka yi min wannan tambayar Aliyu?”
“Wata kila amsar tana da nauyi ko Ammy?”
“Kai ne mutun na biyu da yayi min wannan tambayar bayan Zahra”
Ya furta cikin yanayi na rashin jindadi sannan ta mike tsaye ta fara takawa zuwa gurin kofar, Abiey ma ya mike tsaye.
“Tsawon shekarun nan da na dauka na girma ne a hannunki ban tana kauna ko soyayya ta mahaifi ba, ban san abun da kika masa ba har ya tsane ni, be taba kula da ni ba balle ya damu da ni, idan kuma na tambaya sai ki ce ban masa komai ba, na kasa fahimta Ammy miyasa uba zai tsani dansa ba tare da ya masa komai ba? Tsana kuma irin wanda ban taba ji ko gani ba, har yanzu ba ki taba fada min abun da ya raba ki da Mai Martaba ba...”
Yana kai aya ta juyo ta wanke masa fuska da mari mai kyau, sai ya lumshe ido ita kuma ta juya ta fice rai bace. Sai da ya ji karar rufe kofar dakinsa da ta yi sannan ya bude idon ya zauna bakin gadonsa, yana kokarin gano kuskurensa a cikin kalaman da yayi ma Ammy, haka nan dai yake jin kamar ba magani ne kadai abun da ya saka Mai Martaba ya tsane shi ba, idan har magani ne Anty ma ai ba za su bar yaranta a banza ba amman shi yadda Mai Martaba yake dauke kai a lamarinsa abun yayi yawa.
“Zahra ta san dalilin da ya saka Mai Martaba ya tsane ni da yawa kenan? Kuma ta san dalilin rabuwarsu da Ammy?”
Ya furta sannan ya mike tsaye ya nufi gurin madubi yana kallon kansa, fuskarsa sak irin ta mahaifinsa balle ya ce ko shi din ba shi ne mahaifinsa ba. Haka dai ya kwana da tunani kala kala har bachi ya dauke shi yana tashi da safe kuma ya dasa da wani, sai dai ya lura da yanayin Ammy gaba daya ya canja. Bata fasa yi masa abun da take masa ba sai dai fuskarta babu annuri, tana aje masa kofin tea ya kalleta ya ce.
“Ba ki saba fushi da ni ba Ammy, idan maganar da na yi miki jiya ta bata miki rai ki yafe min dan Allah, ba zan jure ki yi fushi da ni ba”
Dagowa ta yi ta kalleshi sai yayi arba da hawayen idonta.
“Kai kadai ne na yi raino ba tare da iyaye da mahaifi ba, ba dan kuma naka uban ya mutu ba sai dan kiyayya kuma ka zama abun da ka zama a yau duk ta dalilina, yaya hudu na haifa amman na fi son ka fiye da sauran, ina son alakarka da mahaifinka ne saboda ina son ka samu aljannarka a karkashin kafarsa da tawa, zuciyarka ta daina raya maka komai Aliyu”
Ya daga mata kai cike da gamsuwa.
“Inshallah”
Daga haka be sake cewa komai ba, bayan ya gama karyawan ya fita zuwa office din Sauban suka dade a a tare suna hira, har la'asar suna tare daman dai idan ba dayansu yana wani abun ba basa rabo da juna kusan ko da yaushe suna tare, most hiran da za ayi Sauban ne mai surutun Abiey shiru yake sai dai yayi dariya ko murmushi a wani gurin, idan ma yayi magana ba da yawa sosai ba. Suna kokarin rabuwa kira ya shigowa Sauban, kamin ya daga sai da ya fadawa Abiey cewa mutumen da ya saka yayi bincike akan ciwon Deen ne har yana fadin.
“Bari mu ji ko ya samo mana labarin wanda ya biya kudin ne”
Abiey ya maida hankali sosai yana kallon Sauban da ya amsa kiran.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, yaushe? Ya Sallah ya masa Rahma”
Ya fada sannan ya sauke wayar yana kallon Abiey.