Sashe 2
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na maida likkafanin ina masa bakwana na har abada, duk yadda kuka ya so ya ci karfina sai na danne domin kukan ba zai dawo da rayuwarsa ba, haka ma kuka ba zai canja abun da Allah yayi niya ba, kuma idan har ban yi hakuri na ci jarabawar nan ba, toh zan yi hakuri don dole ne a inda hakurin ba zai min rana ba. Na mike tsaye ina ta kallon gawarsa sannan na juyo na fito cikin karfin hali da ni kaina ban saka ran zan iya ba, kusa da Mama na je na zauna mutane sai kallona suke hawayen kuma sai suka tsaya min cak kamar an yi ruwa an dauke, gidan yayi tsit kamar babu kowa a ciki. Wata a cikin makotana ta miko min carbi na karba na yi ta nanata Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un. Har maza suka shigo suka shiga har cikin falona suka dauko gawar Deen suka fito da ita, ina ji ina gani aka fice da gawarsa fita ta har abada, lumshe ido na yi na kwanta jikin Mama tana ta kuka ita da Yaya Maryam da Bahijja da har rike ta ake ana rufe mata baki, ni kuwa Allah ya dauke min kuka sam bana jinsa a kusa da idona. Kudin da suke hannumu wadanda muka fara tarawa na aikinsa kamin na samu wata mafita su aka karba aka yi ta biya masa bashi da ya fada, wasu kuma sai su ce sun yafe, wadanda suke nesa kuma Baba ya dauke nauyin bashin a kansa.
A wajen gidanmu aka yi masa sallah, sannan aka dauki gawarsa zuwa gidansa na gaskiya, kamin a isa da shi gafara kawai nake nema masa har aka rufe shi aka dawo, masu amsar gaisuwa suka zauna a waje wato maza kenan, mata kuma na ciki gida tare da ni, duk wanda ya shigo ya kalleni sai ya zubar da hawaye, ba dan ina kuka ba sai dan kukan da na sha dazun da jiya ya saka fuskata ta canja kamarba tawa ba, kowa ni yake tausayawa domin duk wanda ya san mun yi aure da Deen ya san irin soyayyar da muke nunawa juna, musamman yan'uwa da kuma makotanmu domin baya jin nunawa duniya ni kuma baya shayin nuna soyayyata a ko'ina.
Sai dare aka ta ho da Hajiya a lokacin Mama na ta son tirsasani na sha furar da aka kawo daga makota, domin sun mana kara sun kawo abinci kala kala da botoci da tabarmi, suna ta tambayar lafiyata hakan kadai ya isa ya nuna maka yadda zama da makota yake da dadi. A nan ta bude wani sabon babin kuka mutane na ta bata hakuri, domin ita ma kanta abar tausayi ce kasancewar daga Deen sai Bahijja ta haifa, saboda wabi take (Mutuwa yayanta suke idan ta haifa) ni kam ina rike da carbina ina da ambaton Allah, can bayan gama sallah Isha'i mutane na ta shigowa wasu wadanda ba su samu shigowa ba da rana ba, wasu kuma makotanmu ne da suka shigowa su sake duba ni. A cikin mutanen da suka shigowa gaisuwa har da Jamila uwar dan da zan haifa ko ya, yanayin surarta da kamshin turarenta irin na manya masu kudi ya banbanta ta da sauran bakina masu rufi asirina wasu kuma ma talakawa ne talaf, fuskarta kuma ta fita kar a idona duk sa kasancewar babu wuta sai fitilu da aka kunna, kuma ai ba zan taba manta fuskar matar da ya siye abun da zan haifa ba, idan m nace na manta na yi karya, ta kusa ta ratsa mutane ta zauna kusa da ni da katon cikinta kamar nawa. Gaisawa muka fara yi sannan ta yi min rasuwar rashin Deen kana ta dora da wa'azi da nasiha.
“Ki bar wa Allah komai Inshallah Allah zai miki sakamako mai kyaut na abin da kika yi, dan Allah karki saka damuwa a cikin ranki abun ya zo ya taba lafiyar da abun da ke cikinki, kin san ba a son mace mai ciki da yawan tunani ko kuka saboda zai iya shafar lafiyar yaro”
Na kalleta da kyau sai na ga kamar magana take min saboda zafin yayi min yawa.
“Ya akai yi kika san gidan nan?”
“Dr Hamid ya sani, shi ya kawo ni suna tare da Barrister a waje za su miki gaisuwa”
Na yunkura na tashi tsaye domin na kagara ta bar gidan, haka nan nake jin kamar na tsane ta a yau. Sai ita ma ta mike tsaye tana tambayar mahaifiyata ni ban amsa ta ba sai Yaya Maryam dake rike da Husna.
“Ga ta can, Mama za a miki gaisuwa”
Ta karasa tana nuna mata Mama tare da kiran Mama, sai Mama ta taso ta karaso kusa da mu Jamila ta yi mata gaisuwa ta ciro kudin da zai kai 20k ta mika mata Mama ta karba tana godiya tare da addu'a, Yaya Maryam kuma ta bi Jamila da kallo na mamaki, kamin ta juyo kaina.
“Ina zaki je Zahra?”
“Waje Kanena ne zai mata gaisuwa”
Jamila ta amsa da kanta, sai Yaya Maryam ta sauke Husna daga jikinta ta mike tsaye.
“Muje na rakaki”
Ban musa mata ba, sai dai na lura kamar Jamila bata so haka ba, mu muka fara fita sannan ta fito mun dan yi nisa da gidan kadan zuwa inda muke hango mota a fake Jamila tana bayanmu domin ta fini nauyin jiki, Dr Hamid na hango ni sai ya bude motar ya fito tare da Barrister suka rufe motar suka jingina suna jiran karasowarmu, Yaya Maryam na ta haska min hanya har muka isa, sannan Jamila ta iso daga baya Yaya Maryam na ganin Dr Hamid ta gane shi.
“Wannan ba likitan da ya duba Deen ba ne”
“Ni ne, ya hakuri?”
Ya amsa mata da kansa.
“Alhamdulillah”
“Allah ya jikansa yayi masa Rahma, Zahra ya hakuri”
A lokacin ne hawaye ya cika idona tunawa da yadda na salwantar da rai saboda wani rai da ban samu abun da nake so ba.
“Alhamdulillah”
Barrister ma ya dora min da tashi gaisuwar na amsa hawaye na sauko min.
“Na san zaki yi mamakin yadda na san gidanki ko? Akwai addireshin a file din mijinki, kuma dazun tare da mu aka masa sallah dazun har aka kai shi Allah dai ya masa Rahma”
“Ameen Allaah ya bada lada”
Yaya Maryam ta fada ni kan ban da hawaye babu abun da bake.
“Ki yi hakuri duk mai rai mamaci ne, kuma Inshallah zaki samu kyakkyawan sakamako a gurin Allah”
“Na gode”
Na furta daker sannan na juyo da zimmar tafiya sai Jamila ta kira ni na juyo.
“Please take care of yourself”
Kallonta kawai nake na kasa ce mata komai, har sai da Yaya Maryam ta dafa ni.
“Zahra”
Sannan na juyo muka nufo gida ni da ita.
“Ya kyauta da wasu likitocin suna da tausayi, wannan matarsa ce?”
Na girgiza mata kai kawai sai kuma na yi saurin daga mata kai, idan na ce ba matarsa ba ce to wacece ita? Kamar na san zata tambaya sai na ce.
“Mun taba haduwa da ita asibitin ina tunanin yar'uwarsa ce”
“Allah sarki ita ma ciki ne da ita, Allah ya sauke ku lafiya”
Wani sabon kuka na ji ya zo saboda na san idan na haihu baby ba nawa ba ne, amman ai aikin da aka yi ba a samu rayuwarsa ba? Hakan na nufin jarjejeniyar ta fasu kenan? Na share hawayena da sauri ina jin kamar na juya na kira Dr na yi magana da shi, wata kila ma zuwan da yayi magana yake son yi da ni, haka dai muka shigo cikin gidan zuciyata da tunani kala kala.
ABIEY POV.
A hankali yake saukowa downstairs din yana gyara hannun rigarsa, Ammy dake zaune a kasaitacciyar kujera ta dago tana dubansa.
“Sai ina?”
Ya dan yi shiru kamar mai tunani.
“Wai zan je na yi ma Mai Martaba bakwana gobe zan wuce”
“Ka kyauta, ka gaishe shi amman ga breakfast din nan yana jiranka”
Ammy ta fada tana murmushi.
“Maybe zan karya a gurin Anty but yanzu bana jin zan iya cin komai”
“Why”
“Just”
Ya daga kafadunsa shi kansa ba zai iya fadar abun da yake damunsa ba, kawai dai yana jin jikinsa ba dadi haka ma ransa a bace yake for no reason, sai ta nuna masa guri kusa da ita
“Zauna Aliyu”
Ba musu ya zauna ana sauke ajiyar zuciya a sirrance.
“Me yake damunka?”
“Wallahi Ammy ban sani ba, kawai dai na farka na ji ni wani iri, and ina son na tambaya ke kika ba Zahra kudin aikin ne?”
“Aa ba mun yi da kai cewar zaka saka a bata ba?”
“Yeah Sauban ya fada min ko da yaje biyan kudin ya tararda wani ya biya, na kira Dr da Anty sun ce duk ba su suka biya ba”
“Toh ni ma ban biya ba, maybe Allah ya kawo mata wata mafitar ne”
“Maybe”
Ya fada yana mikewa tsaye.
“Ka gaishe shi”
Ammy ta sake fada sai ya juyo yana kallonta da murmushin da be san inda ya samo shi ba.
“Yau kuma ke da kanki”
“Ranar na masa rashin kirki shiyasa”
Murmushi yayi ya juya ya nufi kofar fita, da dan kuzarinsa ya sauko entrance din ya nufi motarsa tun kamin ya karasa ya danna key hannunsa sannan ya bude ya shiga motarsa yayi reverse. Cikin natsuwa yake driving har ya fice daga gidan, be yi nisa da unguwar ba PA ya kira shi sai ya bude Bluetooth din dake cikin motarsa yayi connecting.
“Ranka ya dade komai ya zama ready karfe biyar za su tashi gobe”
“Okay”