← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 127

Sashe 63

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A firgice Sauban ya kalli Abiey kamin ya juya ya cigaba da tukin da yake he never thought Abiey da gaske yake sai yanzu, sai dai shi baya jin cewar Abiey yana cikin hayyacinshi yake mishi wannan maganar, har suka isa gida Sauban be sake cewa Abiey komai ba, Abiey kuma be sake kallon side da Sauban yake ba. Rai a bace Sauban yayi reverse ya bar gidan ba tare da ya shiga ya gaishe da Ammy ba kamar yadda ya saba.
Abiey kamar wanda aka cirewa lakka haka ya hau entrance din Ammy ya murda kofar falon da ya samu a bude ya shiga ciki sam be lura da Ammy da bakuwarta dake zaune a wani bangare na falon ba domin hankalinshi ba ya gurin kowa sai Zahra dake can kwance.

“Aliyu”

Ammy ta kirashi sai ya juyo ya kalli saitin inda take zaune.

“Ina ka je? Na ga fitarka a firgice kuma na kira wayarka baka daga ba”

Sai a lokacin yana tuna da ya saki wayarshi a Garden.

“Na barta a Garden”

“Ina ka je?”

“Asibiti na duba Zahra bata da lafiya”

Ya fada cikin yanayi na damuwa, Ammy ba yarda ta sake yi mashi maganar abun da ya shafi fitarshi ba balle har tace mashi ya jikin Zahra.

“Ba ku gaisa da Hajiya Asma'u ba”

Ya Abiey ya cira kafa ya karasa kusa da su ya gaishe da Hajiya Asma'u ta amsa mashi cikin far'a tana mashi ya aiki.

“Alhamdulillah”

Ya fada sannan ya juya ya fara takawa. Ammy ta ce

“Yasmin tana ďakina tana jiranka zaka kai ta gida”

“Okay let me get my keys”

Ba tare da ya juyo ba ya fadi haka ya cigaba da taciyarshi har ya haye sama ta tura kofar ďakinshi ya shiga, kamar yadda ya fada gurin da yake ajiyar keys din ya nufa ya dauki na motar da yafi yawan hawa ya fito ya nufi ďakin Ammy. Yasmin na ganinshi ta yi saurin gyara zamanta ta sauke kai kasa.

“Mu je na sauke ki gida”

Ba musu ta mike tsaye shi kuma ya juyo sai ta biyo bayanshi, yana gaba tana kallon yadda yake sauka stairs din kamar mai kirga step dinshi, yana sauka ya nufi kofar fita ita kuma ta nufi gurin su Ammy ta yi musu sallama sannan ta fice daga falon, ko da ta fito Abiey na tsaye bakin kofar Garden rike da wayarshi yana jiranta, tun da ta fito yake kallon lafiyarta har ta iso.

“Ki yi hakuri da abun da na yi miki a dazun”

“No ba sai ka ba ni hakuri ba, ba ka yi laifi a abin da ka aikata ba, kuma kana bukatar ayi maka uzuri idan ma ka yi laifin”

He smile in pain.

“Har zuwa yaushe zaki yi ta min uzuri?”

“Har zuwa lokacin da Allah zai cire min son ka”

He smile again.

“Idan kuma be cire ba fa?”

Ta kalleshi.

“Ban roka ba ma ya ba ni ya kake gani idan na roka?”

“Ashe son da kike min ba mai karfi ba ne tun da har zaki iya rokon Allah ya cire miki so na a zuciyarki”

“Mu musulmai be Abiey mun yarda da kaddara mai kyau da marar kyau, kuma ko da yaushe muna neman zabin Allah a cikin lamurranmu ne, ina addu'ar ne da neman zabin Allah idan alheri ne ko akasin haka”

Da hannu yayi mata alama da ta wuce gaba sai ta jera da shi suka nufi motar a tare, shi ya fara shiga sannan ta bude ta shiga tun da yayi ma motar key be sake kallon gefen Yasmin ba kuma be sake ce mata komai ba, ita ma bata ce mashi ba sai dai tana satar kallonshi jefi jafi har suka isa gidan.

“Na gode”

Ta fada tana kokarin bude motar ta fita.

“Mai Martaba yace zai saka lokacin aurenmu nan da wata uku”

Juyowa ta yi ta kalleshi.

“Wata uku kuma?”

Ya daga mata kai har lokacin be kalleta ba.

“Wata uku ai yayi kusa, yaushe muka fahimci junanmu ma? Ya kamata ace musan wane irin zama zamu yi idan muka yi aure”

“Karki damu zan iya iya kokari na ga ban cutar da ke ba, zamu aure saboda cika umarnin Mai Martaba, kuma saboda Zahra ta bukaci haka?”

“Me kake nufi? Ita kuma ta yi Yaya?”

“Ammy ta ce ba zan aureta ba, Mai Martaba ma be goya min baya ba saboda abubuwan da suka faru, and na samu matsala da iyayenta dalilin wannan an kulle mana kofar da muke ganin kamar idan mun bita zamu mu bulle”

“Ina Zahra take a yanzu?”

“Asibiti an kwantar da ita”

“Saboda kai?”

Ya kalleta ya daga mata kai.

“Kai da Zahra kun cancanci juna Abiey, ba zan iya shiga tsakanin wannan soyayyar ba, saboda ni ba zaka rasa wanda ka mutu kana so ba, a dalilina Zahra ba zata rasa ka ba”

“Babu yadda zamu yi, mun saka kanmu a sarka ne domin Mai Martaba ba zai yarda a fasa auren nan ba, kamar yadda iyayenki ma ba za su tunkari Mai Martaba da zancen ba ki nuna so na ba, domin sun fada tun farko ba za su zubar da kimarsu ba”

Bata sake ce mashi komai ba ta fice daga motar, binta yayi da kallo har ta shige cikin falon Momy sannan ya jinginar da kanshi jikin kujerar motar ya sauke ajiyar zuciya ya runtse ido yana jin yadda zuciyarshi ke mashi mugun zafi da radadi kamar an saka wuka an yanka ta an saka mata barkono a ciki tsabar ciwon da take mashi.
[11/10, 4:58 PM] Oum_Nuwaira🥰: 4️⃣3️⃣

“Sannu...”

Na ji wata muryar da ban gama tantancewa ba, a hankali na bude idon sai na yi arba sa kyakkyawan murmushin dake shimfide a fuskar Dr Hamid.

“Sannu Zahra”

Na dauke kai daga barin kallonshi na kalli Mama da fuskarta ta fada saboda tashin hankali, sannan na kalli Yaya Maryam ita ma sannu take min.

“Mi ya faru?”

Na tambaya gaba daya jin nake kamar babu kwakwala a cikin kaina na kasa tuna komai right now miyasa aka kawo ni a nan miya faru kamin a kawo ni daga ina aka kawo ni nan duk ban tuna ko daya ba.

“Ya jikin na ki?”

Dr Hamid ya tambaya sai na unkura na tashi zaune cikin rashin kuzari.

“Alhamdulillah”

Na amsa ina hade yawu, sau Dr Hamid ya matso ya rika fuskata ya bude idona yana kallo.

“Kina jin wani abu yanzu?”

“Aa bakina da ba dadi”

“Zai daina”

Na daga mashi kai.

“A bata abinci ta ci babu matsalar komai yanzu da yardar Allah idan ta gama sha zan shigo na bata magani”

“Toh an gode”

Mama ta fada sannan ta bude manyan kulolin da na san gidan Dr Bashir suka fito ko Dr Hamid domin kulolina da ni na san ba za mu iya siyensu ba. Lafiyayen abinci ne har kala biyu dafadukar shinkafa da kayan ciki sai kuma tuwon semo miyar agushi da ta ji kifi da nama sai kamshi mashanu take. Tuwon Mama ta zuba min domin ta san na fi son shi ta dora min plate din akan gado sai na sauko da kafafuwana cikin rashin kuzari.

“Ina zaki?”

Dr Hamid ya tambaya.

“Bandaki”

“Zaki iya zuwa ko a rika ki?”

Ya amsa min da kai sannan ya juya ya fice ni ma na taka na shiga bandakin, ina kunna tap sai abubuwan da suka faru suka dawo min a kai. Bakina na wanke na wanke fuskata sannan na yi fitsari na fito na dawo saman gadon na zauna. Kasa cin tuwon na yi sai ruwan tea Mama ta hada min na sha. Bayan kamar mintuna asirin Dr Hamid ya dawo dakin sanye da safar hannu fuskarshi sanye da farin gilashi.

“Madam ya jikin?”

Ya tambaya da murmushi, sai Mama ta amsa mishi.

“Da sauki dai a yadda muka gani yanzu”

“Allah kara sauki ta ci abinci?”

“Aa gashi nan na rufe bata ci ba, tea kawai ta sha”

“Okay”

Ya nufi akwai da aka jera magani yana fadin.

“Mama ko zaku dan ba mu guri”

“Toh”

Mama ta amsa sannan suka tashi tare sa Yaya Maryam suka fice, sai da suka rufe kofar sannan ya turo akwatin maganin ya karaso inda nake zaune ya cire safar hannunshi ya mika hannu ya bude plate din tuwon da Mama ta rufe ya zauna saman gadon ya aje tuwon tsakiyarmu.

“Ko wani abun kike so a siyo miki?”

“Aa bana jin cin abincin ne”

“Idan ba ki ci abinci karin damuwa ne, ba ki son ki warke da wuri ne?”

Na yi shiru ina sauke kai kasa.

“Zahra”

Ya kira sunana sai na dago na kalleshi kadan shi ma kallona yake.

“Mama ta fada miki abun da yake damunki?”

Na girgiza kai.

“Zuciyarki ce ta buga, irin wannan yana faruwa idan wani abu ya faru kamar mutuwar wanda baka zata ba, ko rabuwa da wanda kake tsananin kauna sai kuma zuciya ta kasa jurewa, ba ko wace zuciyata take jure daukar wahala ba, wanu lokacin kuma kamar idan mutum yana da hawan jini ko damuwa irin wannan yana faruwa”

Ta saka hannunshi ya dauki spoon din dake cikin tuwon ya gutsara ya kai min saitin bakina. Kasa ce mashi aa na yi kuma na kasa bude bakin na karba har sai da ba bani umarni.

“Bude bakinki”

Na bude bakin kadan sai ya saka min karamar lomar mai kamar ta jarirai.

“Ban san wacece ke ba kamin yanzu, saboda haka ba zan yanke hukunci akan rayuwarki, wane irin kalubale kika fuskanta kamin ki kawo yanzu, a yanzu din ma wane kalubale kika fuskanta”

Ya sake dibar tuwon ya kai min a bakina na karba na fara taunawa, sannan na debi kifi ya kai a baki.

“Idan wani ya tambaye ni wacece Zahra? Amsar da zan bashi ita ce Zahra wata yarinyar ce mai karancin shekaru kyakkyawa mai saukin kai mai hankali mai tarbiya wance take rayuwa tare da mahaifiyarta da yayarta”
Chapter 63 · 0% Book details