Sashe 119
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Abun da ya kawo mu kenan, Yaya ya fada mana komai kuma ya ce Zahra ta yi nufin bar masa Amir amman yaki ya karba saboda yana tsoron abun da zai biyo baya, ni da Ummiter muna ganin kamar karbar shi ne mafita a garemu da kuma ku gaba daya, domin ba ma son labarin nan ya fita, kuma ina kallon wannan abun kamar wata kyauta ce da Allah ya fara yi mana ta bangaren Yaya ba mu san abun da gaba zata haifar ba, domin ba shi ya aikata ba, kuma ba da saninsa aka yi komai ba, wannan kukan da yaron nan yake yi ma kadai ya isa ya saka mu fawwallawa Allah komai, kuma mu masa godiya”
Mr Bashir da ya dora Amir a kafadarsa ya sauke ajiyar zuciya, sai tausayinsa ya kara kamani lallai rashin haihuwa wani mugun ciwo ne, musamman a gurin mutum mai son yara da kuma tara iyali, ba dan haka ba wata kila da Mr Bashir da yan'uwansa tsanar Amir za su yi jin cewar ba jininsa ba ne, amman hakan be canja komai daga soyayyar da suke masa ba.
“Allah ya baka ikon rike shi amana, kuma ya baka ikon tarbiyantar da shi, amman ina son ka yi min alkawari ko da bana raye ba zaka taba bari hawayen Amir ya zuba a gurin da ka san zaka iya share masa ba, kuma ba zaka taba bari ya san komai akan lamarin nan ba”
Na furta hawaye na masu zafi na sauko, ina jin wani irin kaunar yarona da kuma tausayinsa na kama ni fiye da zatona, zuciyata ta yi mugun karaya.
“Na miki alkawari Zahra, ko da bana raye Amir ba zai taba kukan maraici ba, soyayyar da zan nuna masa ko dan da na haifa jinina iya ka kenan, daga ni sai yan'uwana muka san wannan gaskiyar, kuma na tabbatar ba zasu fada masa ba za a rufe maganar nan har a bada”
“Hajiya Jamila zata iya fada”
“Na gargade ta, kuma ita ma kanta ta san abun kunya ne a gareta ta fadi abun da ta aikata shiyasa da tafi gida sai ta fada musu cewar aure zan yi shiyasa na rabu da ita”
Na matsa kusa da Mama na kwantar da kaina a kafadarta, ina jin wani abu mai kama da kewa na yi min yawo a zuciya.
___________________________
(Ni ko na ce anya Zahra zata iya hakura idan ta kyautar da Amir 🤔 to zamu dai gani WANI GARI Littafin da zai zo a 2050😁 nan da 28years masu zuwa amman fa a rayuwar littafi)
[12/8, 5:19 PM] Oum_Nuwaira🥰: 7️⃣2️⃣
YASMIN POV.
Tana gama karanta jaridar ta dauki wayarta da sauri ta kira Abiey gabanta sai faduwa yake, sai da wayar ta kusan yankewa sannan ya amsa kiran.
“Hello Yasmin”
“Na'am an tashi lafiya”
“Lafiya Kalau, ya Momy”
“Lafiya kalau take”
Sai kuma ta yi shiru, hakan ya saka shi aje wayar a jikin madubin dake dakin ya cigaba da lika batulan rigarsa.
“Yasmin”
“Na'am”
“Kin yi shiru”
“Wani abu na gani a jarida yanzu nan, wai an daura aurenka da Zahra a sirrance”
Abiey ya dafe kansa da sauri.
“Oh abun har ya kai a buga a jarida?”
“Da gaske ne kenan?”
“Eh gaskiya ne”
Yasmin ta mike tsaye da sauri ta dafe zuciyarta tana haki.
“Yaushe? Abiey da gaske kake?”
“Yau kwana biyu, ina zaton ban taba miki karya ba”
“Amman ba ni da hakkin da zan sani ne? Da ba za a fada min ba sai dai na gani a jarida?”
Jikin Abiey yayi sanyi domin ya san be kyauta mata ba, ya kamata ya sanar da ita komai ko shi ko Ammy amman be iya yayi ko daya ba saboda murna da farinciki sun dauke masa hankali, zauna yayi a kujerar madubin yana kallon kansa.
“Ki yi hakuri Yasmin, ban kyauta miki ba Wallahi na sha'afa ne gaba daya, amman zan zo na same ki anjima zamu yi magana akwai ma labarin da zan baki mai daďi idan na zo”
Lumshe ido tana hawaye masu zafi ma sauko mata, har cikin kokon zuciyarta take jin zafin abun da Abiey yayi mata.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”
Ta furta tana jin wani irin azabar sonsa da kishinsa na fisgarta, fashewa ta yi da kuka mai karfi abun da bata taba yi ba, da gudu Momy ta shigo dakin ta zauna kusa da ita ta dafa ta.
“Lafiya Yasmin?”
“Momy da gaske ne Abiey yayi aure”
Momy ta yi murmushi ta kwantar da ita kan kafadarta.
“Shi ne kike kuka? Daman can zuciyarki ta raya miki ke kadai zaki zauna a gidan namijin da zaki aura ko da ba Abiey ba?”
“Aa Amman Momy ai an saka ranar aurenmu fa”
“Auren Zahra zai hana shi aurenki ne? Bayan ke zai iya karo auro wata ma, kuma kin gani a jaridar ance an daura auren ne a sirrance, Allah kadai ya san abun da ke nan”
Momy ta dago ta ta share mata hawayenta.
“Ni shawara daya zan baki, karki yarda ki nuna masa kishinki a kan Zahra, matukar kina son ki zauna lafiya da shi, to ki koyi sonta, ni a ganina ai wannan abun farinciki ne ya same shi da ya kamata ki taya shi murna ki nuna masa kin fi shi jindadi, kamin na auri Mahaifinki ni da Hajiya Umaima miji daya muke aure, ba za a ce babu kishi ba, domin duk mace tana da kishi amman mai hankali da wayo ita take boye kishin nata, ita kuma wanda miji yafi so idan tana da wayo da hankali sai ta rika dora shi akan hanya ta gari, da ace ba mu yi zaman lafiya da juna ba, da Abiey ba zai yarda ya aureki ba, idan ma ya yarda mahaifiyarsa ba zata yarda ba, amman zaman lafiya ya saka mun zama yan'uwa wani lokacin Abiey da kansa zai kawo min karar mahaifiyarsa ko kuma yayi fushi da ita ya dawo nan ya zauna, mi ya kawo haka ba zaman lafiya ba? Ki yi kishin mijinki kishi abu ne mai kyau amman karki yarda kishin nan ya fi karfinki domin zai cutar da zuciyarki ne ita kuma ta cutar da ke, ki rike Zahra kamar yar'uwarki, idan abun farinciki ko sabanin haka ya same ta ki taya ta murna ko jajantawa ko da kuwa ita din bata miki haka, ki bita irin bin da mijinki zai fahimci babu wata cuta ko kiyayyarta a ranki, musamman Abiey da yake matukar son Zahra, idan kika nuna masa baki kaunarta abu ne mai wahala ya iya zama da ke”
“Amman Momy ai yafi sonta”
“Dole ya fi sonta ai, daman namiji ba zai iya daidaita soyayyarsa tsakaninsa da matansa ba, Allah be bashi wannan ikon ba, amman mai yawo shi yake boye soyayyar kuma ya kwantanta adalci a tsakani, karki yarda Zahra ta fiki kyautatawa Abiey da yan'uwansa da iyayensa, da wannan zaki karbe soyayyarsa har ya dawo yana sonki fiye da ita”
“Toh”
Ta amsa wasu hawayen na kuranyo mata, wayarta ce ta dauki kara tana duba mai kiran sai ta yi arba da Abiey.
“Shi ne ya kira”
Ta fada tana dubi Momy, Momy ta yi matan alama da ta amsa da hannu.
“Hello”
“My dear ina wajen gidan zan samu ki fito please”
For the second time ta ji ba zata iya yi masa abun da ya bukata ba.
“Ni aiki nake yi”
“Toh ni gani nan shigowa”
Ta sauke wayar tana kallon Momy dake hararta domin ta ji abun da ya nema ita kuma ta yi ta yi masa.
“Yanzu wannan ba soyayya ce ya nuna miki ba? Ina kara gargadinki Yasmin matukar kika biye zuciyarki to zata kai ki ga halaka ne”
Momy ta mike tsaye ta fice daga dakin, tana fitowa falon ta samu Abiey tsaye yana kallon kofar dakin Yasmin kamar mai neman wanda zai aika a kira masa ita, a da can babu kunya tsakaninsa da Momy sai dai a yau yana hada ido ta ita sai ya ji kunyarta ta kama shi irin ta sukuri da ya shigo gidan surukansa, har yake jin ina ma be shigo falon ba har sai da aka yi masa izini.
“Momy”
“Abiey ne”
Ya risina mata abun da be taba ba.
“Eh Momy ya gida”
“Lafiya Kalau ya Hajiya Umaima”
“Lafiya kalau take”
Yayi shiru na wani lokaci Momy ta nufi kitchen domin kawo masa abun karyawa kasancewar safiya ce.
“Momy zan wuce daman na zo ne kawai na gaishe ki”
Momy ta juyo tana murmushi.
"Toh a gaida gida, amman ka jira waje Yasmin zata fito yanzu”
“Toh Momy thank you”
Ya juya ya fice yana shafa kansa kamar ba shi ba, mutumen da ada idan ya shigo gidan har kusa da ita zama yake, kai ta girgiza tana jindadin samun Abiey a matsayin sukukinta domin miji ne da ko wace mace zata yi alfahari da shi, ta sani matukar Yasmin ta kwantar da hankalinta shi kuma ya kwatanta adalci zata jidadin zama da shi. Dakin Yasmin ta shiga ko da ta shiga ta same ta har ta saka hijab dinta tana ganin Momy ta boye fuska tana jin kunya.
“Je kitchen ki sama masa abun karyawa ki fitar masa da shi”
“Toh”
*** *** ***
Abiey na zaune cikin motar yana video call da Zahra ya hango Yasmin ta fito dauke da faranti sai yayi saurin gyara zamansa.
“Hiayatee i will called you back Okay”
“Miya faru?”
“Ba komai wani abu zan yi, ina gamawa zan je gurin Mai Martaba idan na dawo sai na zo na dauke ki mu tafi shopping din, i love you”
“I love you more”
Ya sumbanci wayar sannan ya daga mata hannu ya kashe, hakan yayi daidai da bude front seat da Yasmin ta yi da dayan hannunta ta shiga ta zauna, amman ta ki yarda ta kalli inda Abiey yake zaune kuma ta ki tace masa komai haka ma ta kasa boye fushinta. Abiey yayi murmushi mai sauti ya mika hannu ya karbi tray ya dora a jikinsa.
“Na san na yi laifi, amman neman yafiya na zo fa ko karyawa ban yi ba”
Ta nade hannayenta ta juya masa fuska.