← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 127

Sashe 78

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Wata rana kamar haka zaki hango damuwarki, ki zauna da wani kina bada labari cewar a da can na yi kaza na shiga hali kaza da kaza”

“Ina fatar haka”

Na furta cikin hardewar halshe, sai ya kalleni yana dariya.

“Kamar ban taba ganin kina kuka ba sai yau, ashe kina kyau da kuka”

Ya ciro wayarshi ya fara daukata hoto ina wani gurin ina hararar camerar wani kuma ya dauke mu tare.

“Ki taimaka min ki yi murmushi ko kadan ne”

Ya bukata yana kallona lips dina.

“To ina kuka zan yi murmushi kuma?”

“Kadan za ki yi, saboda tarihi”

Haka dai ya takura ni na yi murmushin kadan na yi zaton hoto yake ashe video ne, sai jin na yi ya tintsire da dariya sosai.

“Zahra idan ba ke ba, wa za a cewa yayi dariya yana cikin kuka kuma ya aminta yayi?”

Murmushi na yi na rufe fuskata ina jin kunya sosai, na dade a haka sannan na dago sai na ga idonshi yana kaina fuskarshi cike da annashuwa.

“Na yi farinciki da na ga murmushi a fuskarki Zahra baki san abun da na ji ba a lokacin da na ga kina kukan nan Wallahi na ji kamar ace zan iya saka hannu na cire miki damuwarki a take”

Na sauke idona kasa domin wani kallo yake min na kurrilla.

“Tashi tsaye”

Na mike tsayen kamar yadda ya bukata shi ma ya mike tsaye yana cigaba da kallona.

“Promise me ba zaki sake kuka irin na dazun ba, kin karya min zuciyata sosai, kin ba ni tsoro”

Sai na ji kamar ya tuna min da dalilin kukan ne a take na sake jin wani sabon kuka na dusaso duniyata, domin na san watan kuka na ne ya tsaya, ba ni da wata mafita a yanzu domin Hajiya Jamila ta kasa fada min cewar ta bawa Dr Zainab kudi amman har yanzu bata aminta ta ba su result din ba, hakan na nufin zata bar Mijinta ya san gaskiya kenan kuma ita ma zata sani wanda hakan zai haifar min da matsala, ba ta bangaren mijinta kadai ba har ta gurin Hajiya da Baba kuma mijin Hajiya Jamila ma zai iya daure mu ni da Mama.

“Zahra...”

Ya kira sunana jin na yi shiru ina tunanin makomata.

“Sauban ina son na shiga ciki”

“Okay, amman zan iya sanin dalilin kukanki? A yanzu ma ina karantar damuwa a fuskarki”

“Bada maka ba shi da amfani domin ba zaka min magani ba, kuma matsalata bata shafe ka ba, kar ma ka saka kanka a ciki da haifar maka da matsala”

Ya rumgume hannayenshi.

“Indai ya shafe ki ya shafe ni Zahra, amman ba zan cilasta ki fada min ba, hakan kuma ba zai hana ni aiwatar da abun da na yi miki alkawari ba zan yi ta roka miki Allah sauki har sai ya samu a rayuwarki”

Na daga mishi kai ina share hawayen da suka fara min zuba. Ina kokarin ce mishi ya tafi kar Mai gidan ya sake zuwa ya tarar da shi sai kawai na ji an bude gate din gidan da gudu, ba ni tabbacin mijin Hajiya Jamila ne ko wani ni sai dai yanayin yadda suka bude motar da gudu ya nuna haka.

“Ka gani ko? Mai gidan ya dawo kuma yace min kar ya sake ganina da kai gashi ina cikin wata matsala zan haifar da kaina wata, yau dai na shiga uku”

Na fara kuka Sauban ya juyo yana kallona, iyakar abun da na sani ya bude baki zai yi min magana amman ban tsaya sauraren abunda ya fada ba ko zai fada na ranta a na kare kamar wata aljana haka na isa BQ da guduna ina haki, yadda na fada dakin da guma ma sai da hankalin Mama ya tashi.

“Lafiya”

Sai kawai na fashe da kuka.

“Mai gidan ne ya dawo ya same ni da Sauban? Na shiga uku”

“Sauban kuma?”

“Eh ashe ba Hajiya Jamila ce take kirana ba, shi ne amman a falon Hajiya Jamila na same shi”

Na fada jikinta na kara fashewa da kuka, dazun dai kukan rashin mafita da tsoron tonuwar asirina nake yanzu kuma na amsa tambayoyin mijin Hajiya Jamila nake, Mama sai aikin ba ni hakuri take can kuma ta rufe da fada wai ai ni na bashi fuska tun farko gashi nan yanzu abu yana son ya zame min matsala.

“Kuma da kika je kika ga ba Hajiyar ke kiranki ba, ai sai ki dawo ki bar shi a can amman kika tsaya tuntuni har Mai gidan ya same ki...”

Mama na rufe baki na karawa kuka nawa mai, haka muka kwana cikin zullumi da tunani ni da Mama, ko iska ya kada sai na ji kamar wani ne zai zo yace min min mijin Hajiya Jamila na nemana. Misalin karfe bakwai na safe Mama na shirya mana abun karyawa ni kuma ina kwance saman carpet din da na yi sallah ina tunani muka ji sallamar Ummiter da sauri na tashi na koma saman katifa na kwanta na fara bachin karya gabana sai bugawa yake jinina na yawo kamar zubar ruwa tsabar tsoro. Haka Mama ta shigo tana tashina domin ta san ba bachin gaske nake ba.

“Zahra tashi ki tafi yana nemanki”

Da gangan na ki motsa na yi samo kamar mai bachi gaske.

“Kin san dai jinkirinki zai kara bata mashi rai ne kawai ko?”

“To ni Mama me zan ce mashi?”

“Ya zan yi na sani, ki tashi ki tafi kika sani ko ya yanke shawarar korarmu a gidan ma mu huta”

A dole na tashi na fito daman ban ban cire hijabin da na yi sallah ba, ko da na fito na samu Ummiter sanye da uniform dinta na aiki yayi matukar yi mata kyau duk da kasancewar ta baka. Tana gaba ina biye cikina sai kuka yake na tsoro har muka shiga bangarenshi.
[11/16, 8:51 PM] Oum_Nuwaira🥰: 5️⃣1️⃣

Na kara samun kaina cikin tashin hankali a lokacin da na ga muna nutsawa cikin falon shi da ban taba shiga ba.

“Ummiter”

Na kira sunanta ta juyo.

“Idan bachi yake karki tashe shi ki kyale shi kawai sai zuwa anjima”

“Wani irin bachi kuma? Ba shi yace a kira ki ba”

Na yi shiru ta dan tabe baki sannan ta juya ta cigaba da tafiyar, ni kuma a cilas na bi bayanta muka doshi falon.

‘Idan ya tsiye ni da tambaya zan ce mashi ba ni ba ce Mama ce ta fito ta yi magana da Sauban’

Na ayyana a raina ina ta nemawa kaina mafita, can kuma wata zuciyar ta raya min wata kila ba akan ganina da Sauban zai yi magana ba, wata kila ya gano gaskiyar abun da muka aikata ne, domin da maganar Sauban ne da tun a jiya yayi min magana ba sai an kwana ba, a take na ji cikina ya murda da karfi har na ji kamar zawu zai zubo min, sai da na karanta Bismillah ba adadi kamin na shiga falon gumi har ya samu hanya a jiki, ni da Ummiter kusan zan iya cewa idon mu sun yi bakin gani, domin Hajiya Jamila muka gani akan kafafuwan Mijinta tana dariya kamar wanda bata da damuwa shi ma murmushin yake kana ganin fuskarshi ka san yana cikin farinciki, da sauri ta tashi saman jikinshi ta zauna gefe.

“Haba Ummiter ba ko sallama”

“Ban san kina ciki ba ai, dazun da na fita Yaya kawai na bari”

Ummiter ta fada sannan ta kalli mijin Hajiya Jamila tace.

“Yaya ni na wuce”

Kai ya daga mata alamar okay, Hajiya Jamila kuma ta bita da harara na yi mamakin karfi hali irin na Hajiya Jamila kamar wanda ta shiga tashin hankali a tsakanin shekaranjiya da jiya ba, musamman jiya da ni kaina sai da nawa hankalin ya tashi sakamakon kin karbar kudin da aka ce Dr Zainab ta yi, amman gata a yau har su dariya ko da yake wanda ya iya ya huta da ni ce da tuni na gudu na bar gidan, jiya ma na so mugu sai dai Mama bata ba ni hadin kai ba, wai a cewarta guduwa ba mafita ba ce idan ma mun gudu ina zamu je, ko da mum samu mafaka zai iya nemanmu kuma ya samu.

“Lafiya ka kira Zahra?”

Ta tambaya tana kallona

“Lafiya Kalau, akwai wanda na ce bana son na sake ganinshi a idan nan kuma jiya na gansu tare”

Hankalina ya dan kwanta jin cewar ba magana ce akan ďanshi ba.

“Oh Okay daman akwai mai zuwa gurinta ne? Ban sani ba wake zuwa gurinki Zahra?”

Yanayin yadda Hajiya Jamila ta yi tambayar sai ka rantse da Allah ba a gabanta Sauban ya aika aka kira ni ba jiya, sai dai be zama lallai ace ta san zuwan da yake ba, domin bata da alaka da camers din gidan balle na ce ta gani kuma bata taba fitowa ta gan mu a tare ba idan ba jiya ba. Kaina na kai kasa ina murza yatsun hannuna kamin na ce komai mijinta ya karbe.

“No bari na yi magana da ita, dan ba mu guri”

Ya dauki kofin dake gefenshi ya shanye abin da ke ciki gaba daya, kamar an cilasta haka ta tashi ta fice daga falon ni dai ban yarda na kalleta ba har ta fice ina jin karar rufe kofa gabana ya kara faduwa, hausawa suka ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake tun kamin yace min komai na dago na kalleshi ina kuka da turo baki.

“Wallahi bana son zuwanshi kuma na fada mishi cewar baka so amman be daina ba, kuma jiya ma da ya kira ni ban fito ba shi ne ya shiga falon Hajiya yace a kirani kuma da na zo shi ne yayi dabara yace mu fito waje”

Kallona kawai yake be ce min komai ba har na kai aya na yi shiru dan kaina sai dai ban daina kukan ba domin na san hukuncin da zai min a yanzu babba ne domin yayi min gargadi tun a farko ni ce ban ji ba, ya dauki tsawon lokaci yana kallona ba tare da ya ce komai ba.

“Miye alakarki da shi?”

“Babu alakar komai”

Na amsa mashi da sauri.
Chapter 78 · 0% Book details