← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 127

Sashe 106

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abiey ya tambaya cikin fargaba duk da kasancewar ya ga murmushi a fuskarmu, ni kuma sai na amsa masa da cewar, ina bawa Ammy labarin mahaifina da ya rasu ne shi ne abun ya saka mu kuka, ya fada cikin labarin da muke aka dasa wata sabuwar hira. Na dade a gidan sannan Abiey ya maida ni bayan ya bi da ni ta gida. Hiayatee haka Abiey yake kirana tun daga lokacin da aka yi ana baiko, muka cigaba da rayuwa da nunawa juna soyayyah, Ranar da na gama graduation na Secondary school na ga gata kamar yar wani minister duk wani abu da zan rawa kawaye da kuma wanda na yi amfani da shi Ammy ce ta yi min, sannan ta tara yan'uwanta da Anty Amarya daga bangaren Mai Martaba suka zo. A lokacin ne Abiey yayi min kyauta da wayar hannu daman na dade ina mafarkin samun wayar amman ba dama domin Mama ba zata siya min ba, na san kuma idan na yi ma Ammy ko wani magana za a ce na bari sai nan gaba, ashe gaban a kusa take. Daga lokacin sai shakuwa da soyayya ta karu tsakanina da Abiey wayar safe dabam ta rana dabam haka ma ta dare, ban tabbatar ina Abiey sosai da sosai ba har sai da na fara damuwa da alakar dake tsakaninsa da Safeena, duk kuwa da na san kawarsa ce tun kamin ya hadu da ni, sai dai a yanzu kawance su na cutar da ni, ko dariya yayi mata sai na ji raina ya bace, sanadin haka na shata musu line da ban yi zaton Abiey zai bi ba, sai gashi ya saurareni kuma ya jingine abotarsu a gafe.

Bayan kammala bikin makarantar sai aka fara maganar aure a tsakanina da Abiey, a lokacin ne Mama ta tuntubi Baba domin ya fara bata wani abu a cikin kudin gadon mu da ta bashi ta fara siya min wasu abubuwan, sai ya fara kame kame daga karshe ya sanar da ita cewar ya taba kudin kuma sa'ar siyar da Furnitures da ya fara abun be karbu ba, ba Mama kadai ba ni ma kaina na shiga tashin hankali a lokacin, domin na san da kudin Mama ta dogara kamar yadda ta yi ma Yaya Maryam hidima da su. Yaya Maryam da Mama suka rika siyen abubuwa da be fi karfinsu ba suna aje min. Ana sauran wata biyu bikinmu Ammy ta samu Mama ta fada mata cewar ba za su kawo lefe a yanzu ba saboda gujewa idon mutane tace za a aje min komai a dakina sai dai na tararda shi acan, amman za su min tufafin da zan saka na biki, a nan ta yi ma Mama albishir da cewar bata bukatar komai daga garemu apart from kayan daki har zuwa na kitchen ta tanadi komai, idan an daura aure ni kawai za a kai musu, a ranar Mama ta kwana da farinciki domin samun mace irin Ammy abu ne mai matukar wahala.
Bayan sati daya da faruwar hakan Ammy ta maida ni gidanta aka fara min gyaran jiki ana ba ni kulawa, kar ka so ganin yadda fatata ta zama, fari na ya kara fitowa kyauna ma ba a magana, hankalina a kwance muna ta zuba soyayya ni da Abiey, sai dai duk tsawon lokaci Deen ya dauke kafa daga zuwa gidanmu sai dai dukanmu mun dora hakan a kan rashin lafiyar da aka ce yana yi, na sha zuwa duba shi kamar yadda Mama ma take zuwa, sai dai daga lokacin da na koma gidan Ammy da zama sai ya zamana bana fita ko'ina daga gida sai gida, Abiey ma sai a waya muke hira, idan kuma yana son ganina sai dai yayi irin shigowar nan da babu sanarwa ko kuma ya ritsamu a falo ko ďaki.
Ba ni da wani damuwa ko tashin hankali ina rayuwar kamar wata yar sarki kauna ake nuna min ga ko'ina, har auren mu ya gabato ban ga wani canji a gurin Abiey ko iyayensa ba har sai da ya rage sauran kwana biyu bikimmu, duk wasu shagulgula an gabatar kamin ranar sai dai na lura Ammy da Dr Zainab kamar akwai abun da suke boye min, Abiey ma na fahimci akwai damuwa a tare da shi ta hanyar hirar da muke, Dr Zainab ta zo ta dauki jinina ta fada min cewar ta dauki na Abiey zata je ta gwada, ban kawo komai a raina ba duk da kasancewar an dauki na farko tun kamin a saka mana rana, sai na dogara da abun da ta fada cewar ba zata bari a daura auren ba tare da ta sake yi mana gwaji ba, ba a matsayinta na yayar miji kuma likita, ni kam ban dauki abun da muhimmanci ba, har zuwa ranar da za a daura aure ban samu wata matsala ba, ina wani dakin Ammy ana min kwalliya na kira Abiey na tambaye wane kalar tufafi ya saka sai yace min farare kamar nawa. Bayan na aje wayar ya sake kirana yace yana son magana da ni a kebe, na ji tsoro sosai kuma na samu kaina da faduwar gaba. Shi ya fada min dakin da zan same shi na taka da kafa cikin farin lace da mayafi na isa har gurin na shiga cikin dakin, sai na same shi rai a matukar bace har baya iya kallona.

“Zahra.... ”

Sai yayi shiru, hakan ya saka na tari gabansa ina kallonsa fuskata da murmushi.

“Minene?”

Be iya fada min ba ya fice ya bar ni, cikin tunani da sake sake kala kala, dawowa na yi dakin Ammy na zauna cikin damuwa da sanyin jiki, mutane da ke cike da dakin sai tambayar damuwata amman na kasa furta komai domin ni ma ban san damuwar tawa ba, kawai dai na fahimci akwai matsala ne. Babu wanda ya iya fada min komai sai Ammy da kanta ta kori kowa a dakin ta zaunar da ni tana karantamin yadda kaddara take zuwa da yadda ake son bawa ya karbe ta.

“Ammy duk ban gane wannan ba, mi ke faruwa ne?”

“Zahra ina son ki dauki wannan a cikin kaddararki, ina mai baki hakuri kuma ina mai bakinciki sanar da ke cewar ba za a iya daura aurenki da Abiey ba a yau...”

With full confidence Ammy ta fada min haka, da farko ban yarda ba sai na dauka wasa suke min, har sai da ta jaddamin cewar da gaske ne ba za a daura ba, da na nemi hujja sai ta dauko takardar gwajin da Dr Zainab ta yi ta, bana bukatar wani ya karanta min abun da takardar da kunsa domin ni ma na yi karatu kuma ina cikin yan gaba gaban da makaranta take alfahari da su saboda kokarinsu.

“Ammy ko dai ba daidai ba ne”

Na tambaya bayan hawayen idona sun gama jika takardar jikina yana ta rawa.

“Ki yi hakuri Zahra kadarar ku kenan, shi kansa Aliyu yana cikin wani, shiyasa ya kasa sanar da ke”

“Ina son na ganshi Ammy, Ammy wannan takardar da gaske ne?”

Kai kawai ta daga min ta share hawayen da suka cika idonta ta juya ta fice a daki, kamar makauniya haka na fadi ina lalaben abun da be bata ba, kuka ya hado kayansa yayi masauki a gurina. Abiey na shigo yana ta kallona ya gagara ce min komai, sai na isa gabansa na nuna masa takardar.

“Kalli abun da suka ce amman na san ba gaskiya ba ne, kalli Abiey wai ina dauke da kwayar dake karya garkuwar jiki”

Be duba takardar ba sai kawai ya dauke kai.

“Hakuri zamu Zahra, na so na aureki a haka amman ban isa na taka dokar Ammy ba, saboda bata yarda ba”

A ranar na ga rashin imanin Abiey kuma na yi mamaki, domin a irin soyayyar da yake nuna min na yi zaton zai iya aurena a haka amman sai ya juya min baya, har kasa na kai ina rokonsa ina masa magiya kar ya ba wa iyayena kunya, kar ya watsa jama'ar da aka tara mana, amman ina be saurareni ba, da na fahimci ba shi da niyar canja kudinsa sai na roki ya amince a daura auren daga baya sai ya sake ni, nan ma ban samu ba daga gareshi. Ni da Mama da Yaya Maryam muka shiga cikin tashin hankali saboda abun da ya faru, Baba ma ya nuna damuwarsa sosai musamman ganin sa'a daya ta rage a daura auren taya za a sanar da mutane cewar an fasa auren. A nan ya kawo shawarar a daura da Deen albashi idan ma bana son sa sai ya sake ni bayan an fita kunya, a lokacin na yaba da kokarin Baba da kuma na Deen duk da kasancewar ba shi a gidan a lokacin, haka kuwa aka yi sai aka daura auren da Deen a maimakon Abiey. Kamar wanda aka yi ma mutuwa haka nake ta rusar kuka Mama na ba ni hakuri, ita ma kukan take Yaya Maryam ma haka. Washe garin ranar da aka daura auren aka sake yin gwaji har kala uku yana bada results daya cewar bana dauke da cutar daga lokacin sai na gane yaudara ne Abiey yayi, kuma na gasgata maganar Deen. Daga lokacin sai ala ta yanke tsakanin mu da su Ammy. A lokacin sai na zama wata sarauniya a gurin Deen ya fara nuna min kaunar ba shi ba, duk wani abu da yake marar kyau ya daina kuma yayi min alkawarin cewar har a abada ba zai sake kusantar kayan maye ba, ni kuma na yarda da yi zaman aure da shi domin na karbi kaddarar da ta zo Baba ya kama mana haya, Mama da siyar da daya daga cikin gidan da Baba ya bar mana ta yi min kayan daki, aka bar dayan. Na sha wahala kamin na saba da Deen, sai dai na same shi ba a yadda na yi zatonsa ba, a lokacin na fahimci Deen mutum ne mai sauki kai kuma mai kauna ta fiye da Abiey ma wacan lokacin da ban san komai akai ba, ya mayar da ni sarauniya.......”
Chapter 106 · 0% Book details