Sashe 8
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na sake fada ina turo baki gaba cike da jin bakincikin gaisuwar da suka zo min, ni da Yaya Maryam muka yi ta zancen abubuwan da suka faru muna jin bakinciki, idan na tuna Abiey sai na ji kamar ba ni da wani makiyi da ya kai shi, and the most annoying thing is memories rayuwar da muka yi cikin farincika ya dawo fara dawo min a rai zuciyata ta fara nuna min his ugly happy face, na yamutsa fuska kamar zan yi amai, gaba daya ma sai na ji abincin ya fita a raina.
Wasa wasa kwanaki suka fara mikawa aka share sati daya da kwana biyu da rasuwar Deen, kullum cikin yi masa addu'a nake zuciyata kuma tana ta begen masoyinta, ga kuma tunanin rabuwa da cikina da ya saka ni gaba, na rasa makama zuciyata na ta raya min ba ni da wata mafita data wuce guduwa, ga shi alamun haihuwa sai kara bayyana suke, cikina ya kara nauyi yayi min kasa sosai, zaki sai zuba yake min saboda Mama ta jika min zobo ina sha, Hajiya kuma ta aiko min da kayan jike jike da ake sha na mai ciki, duk bayan kwana biyu kuma sai ta zo ta duba ni, ko kuma ta kira waya ta tambaya me nake son ta girka min, wannan gatan da soyayyar da suke nuna min saka ko na yi unkurin guduwa sai na yi tunanin wane hali zan saka su idan suka wayi gari babu ni? Ni ma idan na gudu wahala zan sha saboda cikin nan, ta inda na samu kwanciyar hankali Dr Hamid ko Jamila babu wanda ya sake zuwa gidanmu, sai dai yanzu Mama ba kullum take kwana da ni ba, Yaya Maryam ma tun da aka yi sati daya sai ta daina zuwan dake tana min wuni sai an kwana biyu, daga ni sai Bahijja sai wata kanwar Kakata da bangaren uba muke koma kwana a gidan.
*LAHADI 5:39pm*
Ina zaune rike da carji ina ja Bahijja na zauna kusa da ni tana fadin na yi rama sosai ni da Hajiya bata san wanda yafi wani jin zafin mutuwar Deen ba. Kamar daga sama muka ji sallama daga kan da zan yi na yi arba da Jamila tana sanye da katon hijab har kasa sai bakin tabarau da facemask dake fuska ta rufe ko'ina ruf domin har hannunta sanye yake da safa, sai wata kudaddiyar yarinya tana rike da jakarta kana ganinta kasan yar aikinta ce, wani irin faduwa gabana yayi domin wannan karon ta tararda ni tare da Bahijja ne ga kuma Kakata dake taya ni kwana.
“Wa'alaikissalam”
Na amsa mata daker, sai ya karaso inda muke ta yi tsaye ganin hakan ya saka Bahijja tashi ta dauko mata tabarma.
“Ai ba zama zan yi ba, daman na zo ne kawai na duba lafiyarki, ya hakuri”
Ta fada fuska ba yabo ba fallasa, ban yi mamakin ganin fuskarta a haka ba wata kila bata huce daga kin amincewa na bita a waje da na yi.
“Lafiya ta kalau hakuri kuma mun gode Allah”
“Maa Shaa Allah, Allah kara hakuri ya saukeki lafiya shin yaushe ne edd ki? Kila mu haihu tare”
Wannan karon da dariyar yake ta karshe maganar saboda kallon mamaki da Bahijja take mata, wata kila bata son Bahijja ta zargi wani abu.
“Sun ce May 23, ke fa? Ko da yake haihuwa sai lokaci yayi”
Na fada mata ba kamar yadda yake rubuce a takardar scanning dina ba.
“Ni ai na shiga wata ba, ashe baki shiga wata takwas ba ma ke, toh Allah ya raba lafiya daman dai nace bari na biyo ne kawai saboda zan tafi tare da miji Abuja”
“Allah sarki Allah ya tsare”
Ta amsa da Ameen sannan ta juya sai kuma ta sake juyowa.
“Wai babu wayar da za a iya kira a same ki ne? Ya kamata ace kina da waya fa”
“Toh ki saka min number ki a nan, kuma ki siya da wuri please”
Ta fada tana saka hannu ta ciro tsadaddiyar wayarta ta miko min, ba musu na karba na saka mata numberta sannan na mika mata wayarta, sai da ta yi mana sallama sannan ta fita, zuciyata na tsaka da raya min cewar da biyu ta zo, Bahijja ta jefo min tambaya.
“Anty Zahra wacece wannan?”
“Kawata ce amman ta bani shekara biyar gaskiya can suke sama”
Na amsa mata, sannan na sauke ajiyar zuciya, a ranar kamin dare yayi har na matsu, suna sallah Isha'i na bude jakar da Mama ta saka mana kudin da muka samu da kuma wadanda muka rage na aikin Deen da muka samu na dauki kudin da zai kai dubu dari na saka a jakata ba tare da na bari Bahijja ko Daada sun lura ba, a yadda muka saba dukanmu a daki muke kwana amman a yau sai na zabi kwana a falo saboda na samu mafita a abun da nake shiryawa, a falon na kwana har safe washe gari na fito harabar gidan na yi alwala na shiga falo na shimfida dankwalina na yi sallah, Bahijja da Daada suna daki suna na su Sallah na dauki handbag dita na fito waje kamin na kai bakin kofar fita gidan har hawaye sun wanke min fuska, bayan na bude gidan na juyo ina kallon gidan, sannan na fito kamin na isa titi ma na gaji sosai ga shi safiyar ma bata gama waye ba, haka na isa titi ina yi ina waigawa gabana sai faduwa yake kamar zai fasa kirjina ya fito. Na isa titi ina ta rabon ido daker na samu wata Napep shi ma da wani mutum a ciki sai da na fara shiga sannan na fada masa inda zai kai ni.
[10/3, 4:49 PM] Oum_Nuwaira🥰: 1️⃣8️⃣
Ko da tara tayi na safe na hau motar Zaria domin ya fi min kusa fiye da ace na tafi garin Mama tafiyar kwana uku wata kila ma kamin na kai za tararda da domin na fadawa Yaya Maryam kuma be zama lallai ta boye ta ki fadawa kowa ba, kusan duk wanda ke cikin motar kallona yake saboda yadda nake hawaye kamar zan karar da hawayena ga kuma katon cikin dake jikina numfashina har wahalar ita yake. Ba ku dade ba muka isa Zaria kasancewar daga Kano zuwa Zaria babu nisa, na sauka ta shar sai na ji dabam ina tajin kamar ace na taho da mask dina ko Niqab, cikin tashar na kusa na nemi shagon da ake siyar da kayan ciye ciye provision na siya mask a gurin da biscuits ya miko min lemu mai gas sai na tuna Deen ya hana ni shan abu mai gas.
“Malam ba ni mai madara”
Na mayar masa sai ya miko min mai madara ya bani canjina kasancewar dubu daya na bashi ya kuma miko min leda na saka, sannan na kama hanya ina tunanin ko zan iya gane Kauyen su Hafsat, wata tsohuwar kawata ce da muka taso tare tun muna yara yar zaria ce sai dai tana zaune a kano ne a unguwar mu hannun yayarta kamin ayi mata aure da wani dan'uwanta a kawo ta Zaria, sai dai iyayenta suna kauyen Kalbana (sunan kauyen Kalbana na kirkira ne).
Kai tsaye na nufu inda ake faka motocin kauyen na taba zuwa sau daya lokacin da tana Kano na saci kafa na tafi ba tare da sanin Mama ba, aiko ranar da na dawo na sha duka a gurin Deen kamar zai kashe ni domin a tunaninsa lokacin na je gurin wani saurayi ne. Ina isa na tararda mutun mutun biyu kawai ake jira a take na biya kudin mutun biyu saboda na samu wali kasancewata mai ciki. A cikin motar na bude lemun da biscuits ina ci, wani dan tsoho mai zubin mayu sai kallona yake, ni ko na daddage ina ta karanto addu'a, idan ma mayen ne sai dai ya ci kasan, daman ance mayu sun fi son mace mai tsohon ciki ko amarya ko mai jego ta fi saukin kamawa a garesu domin jikinta a sake yake kurwarta kuma a kasa take ba kamar sauran da kurwarsu take tashi ba. Ina fara karanta wa'inyakadun lazeena kafaruu.... Har zuwa karshe sai ya fara tsarguwa ya juya fuska be sake kallon inda nake ba har motar ta isa da ni yar karamar kasuwar da ake hawan babur a isa kauyen Kalbana. Na fito na dauki jakata na rayata na kara gyara mask dina da na yi kasa da shi saboda biscuits din da na ci, na nufi gurin da babura suke fake wasu tuni ma sun nufo motarmu da ta tsaya domin aikinsu kenan daukar passengers zuwa cikin kauyen ko kuma gaba da kauyen domin babu titi mai kyau idan da mota za a je za a sha wahala sosai saboda rashin kyaun hanyar, na fada ma mai achaban inda zai kai ni sai ya fada min kudin zuwa can, a take na hau ya fara tuka babur din muka dauki hanyar kauye mai cike da albarkar Manoma. Tafiya ce mai dan karen nisa domin ta dauke ni awa daya da rabi kamin mu isa, aiko kafafuwa kamar na fasshe da kuka abun cikin na sai motsi yake daga ni har shi ko ita mun matsu. Babban family a kauyen domin gidan irin gidan nan ne na gado irin wanda kowa ke ware na shi bangare ya gina nasa a ciki, kuma mahaifinta shi ne sarkin majema na yankin kamin Allah yayi masa rasuwa. Ina tsaka da tambayar wani matashi gidansu sai mai achaban yace min ya sani.
“Ai da kin yi magana da can zan sauke ki, waye be san gidan Margayi Musa Sanga ba”