Sashe 82
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Eh amman na wanda nake kwana ba, dayan ďakin dai”
Na tashi na nufi dakin dana ga namijin da Ammy ta kira da ďanta ya shiga, zaune na same shi bakin gado yana dannar wayar, sai dai shigowata ta saka ya dago kai yana kallona.
“Ammy ce ta ce wai na shigo na kwanta bachi nake ji”
“Okay”
Ya amsa ni with so much respect ya mike tsaye ya fice daga ďakin tare da ja min kofar a hankali. Farkon abun da na fara yi shi ne na nufi makunne ac dakin na duba ban ga gurin da ake karawa ko rage sanyin ba, garin kalle kalle idona ya kai gurin remote din ac, cikin farin na dauka na karanta komai na kure sanyin ac na sake na kunna fankar sama na kunna na kasa dake aje sannan na haura saman gadon na kwanta. Wani kalar sanyi ne an musamman ya rika ratsa fatata yana shiga cikin kashina kamin bachi ya dauke ni jikina har rawa sanyi yake amman ban yarda na kashe ac ba, domin babu shi a house a nan kuma banza ta samu ai kara a sha kamin a mutu. Ban farka sai kusan azahar, a kashe na ga ac da ceiling fan din da kuma standing fan din da na kunna, ni kuma an lullube ni da blanket, ko waye da aikin na san ba zai wuce Ammy ba. Gurin da na ga kofa na nufa na bude sai na tsinci kaina a wani bandakin da ban taba shiga ba tun da Mama ta kawo ni duniya domin ko bandakin gidan Yaya Maryam da nake ganin mijinta ya gyara mata, be kai wannan kyau da tsaruwa ba, bana jin kashi amman a haka na kirkiro shi na yi na danna ruwa suka wuce da shi, na wanke hannuna na yi alwala na tsaya na kalli kaina a madubi sannan na fito. Blanket din na fara nadewa na aje a saman gadon sannan na bude kofar na fito falon ban samu kowa a falon ba na nufi gurin da jakata ta makaranta take na dauka na yi sallah azahar a gurin sannan na dauki jakar na goya na nufi kofa na bude na fice abina ban tsaya neman inda Ammy ta shiga ba. Ina tsaka da saka talkamina na makaranta na ji irin kamshin turaren dazun na bakon Ammy domin zuciyata bata natsu na kirashi da ďanta ba.
“Where are you going?”
“Home”
Na amsa ina kallon kitson dake kamshi gashi dai kyakkyawa amman yayi kitso a kai kuma shi ba mace ba, hannu ya saka aljihu ya ciro kudi ya miko min.
“Ammy tace idan kin tashi a baki, na shiga na samu kina ta bachi har lokacin baki tashi ba”
Sai da na karewa kudin kallo sannan na tambayesa.
“Na minene”
Cikon kudin ankon da kike nema, cikin farinciki na saka hannu na karba ina godiya
[11/19, 1:46 AM] Oum_Nuwaira🥰: 5️⃣3️⃣
Baki har kunne na isa gida ina jin kamar an biya min kujerar hajji domin dubu biyar da Ammy ta bani a yanzu idan na hada da 3500 da Yaya Maryam ta bani zai wadace ni na dinka atamfar har na siye mayafi ma. Ina isa na samu Mama ta yi wanke da shinkafa, dacan ba shiri nake da wake da shimkafa ba sai na shige dakinta na bude jakata na dauko ragowar nama da na ci gidan Ammy na bude na cinye ragowar na tsude ledar, na jefa mata ledar karkashin gado na shafe bakina na fito. Ruwan zafin da Mama da dora min na dauka na sirka ma shiga bandaki na yi wanka, tun kamin na fito na ji muryar Deen yana magana da Mama, ina fitowa wankan ya bini da kallo idonshi zai fado, ba wani baya ni da ni ba balle na ce su yake kallo haka ma kirjina be gama girma ba shi ma balle na ce mamana yake kallo sai dai ko farin fatata da kuma kyau da Allah yayi min.
“Laa Yaya Deen yaushe ka zo”
“Yanzu”
Ya amsa min fuskarshi ba yabo ba fallasa daman can a iya sanin da na yi masa ba mutum ne mai yawan dariya ba. Daki na shiga na shirya da atamfa na dauko hijab din islamiya na saka na dauko jakar na fito.
“Mama makaranta zan tafi”
“Ba ki ci abincin rana ba?”
“Mama ai kin san bana son shinkafa da wake kuma kika girka”
Mama ta riko hannuna tana lallabani.
“Yi hakuri daure ki ci, kamin ki dawo sai na girka miki wani abun me kike so?”
“Indomie ki saka min kwai”
“To je ki ci shimkafar da safe ma baki ci komai ba, shiyasa kullum gaki nan sai rama kike kamar marar lafiya”
“Sai dai ki ba ni kudi na siya a makaranta”
“Ki siye kayan kwadayi ki zuba a ciki anjima ki dawo kina cewa ciki na miki ciwo ko?”
Na turo baki gaba.
“To ni dai Mama zan tafi a haka idan ba zaki ba ni ba, na wuni da yunwar”
“Je ďaki ki dauko 100”
“150 dai Mama kin san fa ina jin yunwa sosai”
Ta amsa min da kai, cikin murna na koma dakin na dauko 150 na fito na tsaya kusa da Deen.
“Ya Deen ina kudin anko da Yaya Maryam ta ba ni? Zaka raka ni kasuwa na siyo ankon please sai ka sauke ni a makaranta”
“Ba da babur na zo ba, mu je dai na tara miki napep”
Ya mike tsaye, ni kuma na sake komawa dakin a karo na biyu na dauko kyalen ankon na fito ina labartawa Mama kudin da Yaya Maryam ta ba ni, sai dai ban fada mata cewar Ammy ta ba ni wasu ba. A zaure na samu Deen tsaye yana jiran fitowa ta, 3500 din ya fara ba ni sannan ya miko min wasu 3k dabam.
“Wannan zai isa a miki dinkin?”
Cikin murna na karba.
“Na gode Ya Deen, ka ga wasu nan ma Aliyu ya ba ni dazun sai na hada na siye mayafi da sabon jaka ma”
A take na ga yanayin fuskarshi ta canja, dan matsawa na yi baya domin ya saba dukana idan na karbi abu hannun saurayi, Mama kuma bata cewa komai balle ta hana shi.
“Wane Aliyu”
“Wani bakon gidan Ammy ne yace Ammy tace na cika kudin ankon?”
“Wacece Ammyn”
“Wannan matar da na taba fada maka tana ba ni kayan dadi, wadanda suke bayanmu”
“Miye alakarki da Aliyun da zai dauki kudi ya baki? Nawa ne?”
“5k ne yace Ammy ta ba ni”
“Ba ni kudin”
Ya miko min hannu fuska kamar bakin hadari, hannu na maida baya na lake kafada, na san matukar na bashi kudin ba zai dawo hannuna ba.
“To ai Ammy ce ta ba ni..”
Ina ruwa baki na yi arba da wasu taurari masu kyale har guda hudu, ba shiri na saki kudin tare da jakar makarantar da kyalen ankon na dawo cikin gidan da gudu ina kuka Mama ta mike tsaye da sauri tana ta rika ni.
“Lafiya?”
“Ya Deen ya mare ni wayyo idon”
Ji nake kamar idon ya tsiyaye tsabar azaba domin hanninshi har cikin idona ya shiga, ina ganin ya shigo cikin gidan na boya bayan Mama ina kuka sosai.
“Mama ta fada miki an bata kudi?”
“Kudi kuma? Waya bata kudi”
“Wai wani Aliyu na gidan Ammy”
“Ban san shi ba, amman dai na san Ammy makociyarmu ce ita ma kuma ina jinta ne a bakin Zahra, ka san duk kofar gidan masu abun hannu ta sani, amman bata fada min Aliyu ya bata kudi ba”
“Amman Mama taya Zahra zata samu kudi baki sani ba, abun nan fa yana yawa”
“Ban da abinka Deeni taya zan san ta samu kudi, tun da bata nuna min ba kuma yaron yanzu ka haife shi ne baka haifi halinshi ba, ina kudin yake”
Ya mikawa Mama har da wanda Yaya Maryam ta ba ni, Mama na jugowa ta cire talkaminta ta fada duka na da shi ina kuka sai ga ni na gudu na neman mafaka a gurin Deen din, daker na sha a hannu Mama daman irin wannan duka biyun bana tsira a gurin Deen idan ma Mama bata min ba shi zai min idan kuma Mama na yi min ba zai ceto ni ba, sai idan na wani laifin ne. Islamiyar da ban tafi ba kenan na yi yammaci ina kuka har kaina yayi ta ciwo, Mama kuma ta yaga katin auren ta kona bayan Deen ya ce ba zan yi ankon ba. Bakinciki kona iv da Mama ta yi sai ya fi min ciwo fiye da karbe kudin da aka yi da kuma hanani anko. Da dare ma daker bachi ya dauke ni sakamakon tsamin da jikina yayi domin ba dan kankanen duka na sha ba a hannun Mama, jiki kuma irin na yayan manya ne da baya son wahala sai hutu.
Tun daga ranar ko kofar gidan Ammy ban sake be bi ba domin Mama ta yi min gargadi cewar kar na sake zuwa gidan, ba wai na ji gargadin ba ne kawai dai na daga kafa ne na kwana biyu domin bana son na tafi gidan da tabon hannun dukan Deen da yayi min kamar dunkulen jini a ido. Irin shiriritar da muka saba ita ka yi a a yau ma sai da muka bi gurin masu kayan itatuwa muka debi na diba muka kamo hanyar gida, a hanya muka rabu da Hafsa ta nufi gidansu ni ma na nufi na mu gidan, ina sallama Yaya Maryam ta amsa min tana gyara daurin dankwalinta.
“Oyoyo yar kanwata”
Na fada jikinta ina shagwaba daman na saba yi mata haka wani lokacin, lura da na yi da ita ma son da take min ba na wasa ba ne wani lokacin har ta fi Mama tausayina ma.
“Yaya Maryam kudin da kika ba ni na anko Mama ta karbe kuma Ya Deen har da dukana yayi”
Ya dafa ni ta kalli Mama.
“Mama saboda me?”
“Bata jin magana, zuwa ta yi ta karbi kudin wani, kin san abun da ke hada ta da Deeni kenan, kuma yana da gaskiya Zahra tana wuce gona da iri”