Sashe 37
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya nuna min hanya sai na wuce gaba yana bayana, ina ta jiran ya fara rokona na shiga motar ya kai ni gida amman be yi ba har na wuce motar ina jin lokacin da ya rufe ta ya biyo bayana muka fara takawa a kasa ga ruwa sai karfi yake karawa, na san kuma idan na yi tafiyar lafa ni da isa sai Asubahi domin ni ba gwanar tafiya a kafa ba ce ga unguwar babu mutane sai mu kamar mayu.
“Na fiki zama bad boy ai, idan arziki be miki ba ai tsiya zata miki”
Na juyo a fusace.
“Ina ruwanka da ni wai? Na tsane ka Abiey ka fita daga rayuwa”
“Ba zan fita ba, kuma idan an sake ganinki da wani namijin sai na ba ki mugun mamaki ”
Ya amsa min kamar zai doke ni yana matsawo kusa da ni har muna shakar numfashin juna ni da shi...
[10/21, 8:03 PM] Oum_Nuwaira🥰: 3️⃣0️⃣
Kansa ya daga sama ya sauke sannan ya matsa baya.
“Kana tunanin karfi zai saka na manta abun da ka yi min Abiey? Ko kuma cilasta ni zaka yi na yafe maka”
Ina rufe baki sai ya daka min tsawa ya sake matsowa wannan karon kamar zai doke ni.
“Ba yafiyarki na ke so ba Zahra..kuma ba rokon na ke ki so ni ba, ki cire wannan a ranki”
“To me kake so? Dawowa ka yi ka takurawa rayuwata?”
Na tambaya hawaye na sauko min, sai na juya ba tare da yace min komai ba ya koma gurin motarsa ya bude ya shiga yayi mata key sannan ya jan motar ya karaso inda nake ya faka bude min front seat. Wannan karon bana bukatar ya fada min na shiga, domin ina jin tsoron tafiya a hanya ni kadai ko mu biyu domin hudu yayi, shiga na yi na zauna sai ya fisgi motar kamar zai tashi sama.
“I'm sorry i don't mean to be rude to you, ke din ce wani lokacin sai...”
“Sai me?”
Na tambayana ina kallonshi.
“Zahra ta ya zaki manta duk rayuwar da muka yi, ko da ace da gaske na yaudareki ya kamata ace kin yafe min mana”
“Ba da gaske ba ne a Abiey?”
“I don't want to say this Deen ya shirya komai, kin kasa fahimta kin kasa ba ni damar da zan wanke kaina”
“Tun a lokacin da abun ya faru ya kamata ka wanke kanka ba wai yanzu! Kuma da zaka rabu da ni da ka rabu da ni kamin ranar da ka so ka kunyata wata kila da yanzu na manta da an taba halittarka, kuma baka bar ni ba sai da ka yi min kazafi, ban taba Zina ba Abiey amman ka ce ina da hiv kuma ta hanyar sex na samu taya zan manta wannan ranar?”
“Deen yayi kidnapping Mijin Dr Zainab and he force her ta shirya haka, saboda a fasa aurena da ke, and Ammy support her saboda yayi mata rantsuwa da al'kur'ane idan aka dauren auren nan zai kashe mijinta, he already told her ya san rayuwar shi ba mai tsawo ba ce so be damu ya rasa ransa akanki ba, after the wedding kuma babu damar mu kama shi saboda za ki iya cewa ana binsa da shi ne, besides ba mu da wasu evidence a lokacin, and hana su yin komai ne saboda ke kar a daga miki hankali a lokacin da kika aure shi, amman ban gujeki ba Zahra ban yaudareki babu dalilin da zai saka na yi haka, yanzu ma ba ki san halin da nake ciki all because of you, Mai Martaba ya tambaya min auren Yasmin ina ta kokarin na yi cancelled abun and you slap me in front of my Step Mom, ranta ya bace sosai ta je gida tana ta masifa Ammy ma ranta ya bace”
Tun da ya fara maganar bance masa uffan ba, hawaye kuma ba su daina min zuba ba jiki ya mutu na kasa yarda da abun da Abiey ya ke fada a yanzu, kuma na rasa courage din karyata shi, but deep down inside my heart wani irin yaki ne tsakanin zuciyata dake karbar sako da kuma kaina da ke aikawa. Har kofar gidanmu ya faka motar sai na cire rigar da ya saka min na mika masa na cire hular kaina na mika masa, na kai hannu na bude motar ya kira sunana.
“Zahra...”
Sai na juyo na kalleshi hawaye na sauko min kamar ba gobe.
“Abiey i need some space, i need to think kaina a kulle yake a yanzu ina bukatar hutu...”
Na fada muryarta a sanyeye sai ya daga min kai.
“I understand i just want you to know that i love you and if you need anything I'm here for you”
“I need some space...”
Na sake maimaitawa sannan na bude motar na fita, kamar zan fadi haka na isa kofar gidanmu kafafuwana babu karfi, ina tabawa na ji kofar a rufe daker na daga hannu na kwankwasa kofar kamar daman can Mama na tsaye jikin kofar tana jirana sai ji na yi bude da sauri.
“Zahra ina kika je kika zauna haka?”
Na shiga cikin gidan ba tare da na amsa mata ba, da ace Abiey be bani labarin nan ba wata kila da yanzu ina da labarai da yawa da zan bata, a yanzu kam ya katse duk wani hanzari nawa tunanina ya tsaya cak.
“Lafiya kika kuka? Miya faru?”
Ta tambaya bayan ta yi arba da hawayena. Sai na sauke kaina kasa ina rike da hannayena.
“Mama Abiey ya fada min wata magana a game da abun da ya faru ina son na tabbatar ta ina son na san gaskiya, amman ban san ta ina zan fara ba”
Mama ta dafa ni domin ta fahimci akwai damuwa sosai a tare da ni.
“Ina kika hadu da Abiey? Me ya fada miki?”
“Gidan Su Hajiya Jamila”
“Shiga ciki ki zauna”
Na nufi dakin da nake kwana ita kuma ta rufe gidan, ko da ta shigo dakin ni har na kai zaune ina hawaye, sai ta zauna kusa da ni.
“Miya faru Zahra”
Maimakon na fada mata sai kawai na fashe da kuka na kwanta a kafarta.
“Ki fada min abun da ya faru mana, ya akai ya same ki a can? Ko kin fada masa abun da yake faruwa ne?”
“Aa ban san yadda aka yi ya ji ina gidan ba kawai ya same ni a can ne...”
Cikin kuka na fada mata abun da ya faru, sai ta cika da mamakin zuwansa gidan ni kuma zuciyarta tana cike da damuwar abun da Abiey ya fada min.
“Wata kila yana da alaka da mutanen gidan ne shiyasa har ya san da haka, da ace ya san da wani abun bayan wannan da yanzu yayi miki magana, ki kwantar da hankalinki be san komai ba”
“Amman Mama da gaske Deen ya aikata abun da Abiey ya fada min?”
Na tambaya ina kallonta domin shi ne abun da na fi damuna.
“Akwai kamshin gaskiya a ciki amman ba zamu tabbatar ba har sai kun yi bincike”
Na mike tsaye da sauri ina tambayar Mama wayarta, ji nake kamar ba zan iya kwana ba sai na yi magana da Hajiya.
“Me zaki yi da wayata?”
“Hajiya zan kira ina son na tambaye ta”
“Ko da ace ta sani ai ba zata fada miki gaskiya ba, balle kuma be zama lallai ace ya aikata hakan da saninta ba”
“Mama ina son na ji ta bakin Hajiya, Deen ba shi da abokin shawara sai Hajiya indai har da gaske ne mahaifiyarsa zata sani”
“Ko ta sani be zama lallai ta fada miki ba”
Na koma na zauna ba dan na gamsu ba, sai dan bana son musawa Mama a yanzu.
“Idan har da gaske ne, Deen ya cutar da ni kuma ya cutar da Abiey ya kuma saka na cutar da Abiey...”
Sai kuma na kalli Mama da sauri zuciyata na karyata abun da Abiey ya fada min.
“Allah yasa ba gaskiya ba ne Mama Deen ba shi da mugun hali har haka”
“Ameen”
Ta amsa sai na hau saman gadon da Hijab na kwanta na nade guri daya ina jin wani sanyi na taso min, bachin da ban yi ba kenan har safe kuma daren yafi ko wane dare yi min tsawo a rayuwata. Kamar ko yaushe Mama ta shirya min ruwan wanka ta dama min kunu sannan ta dumama tuwon jiya ta kawo min, sai da na fara yin wanka sannan na dauki kunun na sha kadan shi kam dumame ban iya ci ba, har zuwa yanzu kuma ban labartawa Mama wulakancin da Hajiya Jamila ta yi min ba, haka ma ban fada mata cewar mijinta ne mutumen da na taimakawa lokacin da hadarin jirgin nan ya faru ba, jiya ma labarin zuwan Abiey a gidan kawai na fada mata domin hankalina baya gurin gaba daya, natsuwata da muradina yana gurin abun da Abiey ya fada min, ina son na dauki permission gurin Mama na fita amman na san ba zata bari ba.
Ina cikin wannan halin muka ji sallama kofar gida muryar namiji ne da zan iya kira magidanci duk kuwa da kasancewar ban ga fuskarsa ba. Mama ce ta amsa sannan ta tambaya waye.
“Dahiru ne, Ammy ce ta aiko ni Mahaifiyar Abiey tace na zo na dauki Zahra tana son magana da ita”
Mutumen ya amsa daga can wajen da yake, a take gabana ya fadi faduwar da ban san ta minene ba. Taso na yi na fito waje na kalli Mama dake aikin gyara tsintsiya.
“Allah yasa lafiya”
“Ameen, lafiya zan yi?”
Na tambaya sai ta daga min kai.
“Eh ai ki tafi kiji dalilin nemanki da take”
Na juya na koma ciki na canja hijab din jikina na saka takalmi na fito ina jin sallamar Yaya Maryam Mama dake tsakar gidan ta amsa mata, ni kuma na sauke kaina kasa ina jin kunyar hada ido da ita.
“Masu jego ina zuwa”
Ta fada tana kunno kai cikin gidan, yayinda ni kuma na ke kokarin fita, sai Mama ta amsa mata.
“Zahra”
Ta kira bayan Mama ta fada mata inda zan je, sai na juyo sai ban kalleta ba.