← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 127

Sashe 47

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, zama be gan mu ba”

Ta fada tana dora hannu saman kai har lokacin kuka take, kan kace kwabo makota sun cika gidanmu suna ta jajatawa Mama, tana ta kiran mutane a waya tana fada musu, ciki har da Hajiya. Babban tashin hankali Mama na rashin sanin inda za a kai shi ko suka tafi da shi.

“Zahra ki kira Abiey ki yi magana da shi dan Allah ko kuma ki kira shi sai ki ba ni wayar”

“Toh”

Na amsa mata ba dan komai ba sai dan bana son musa ba, amman ba dan haka ba da ba zan kira shi din ba domin ni yayi min daidai. Wayarta na karba na koma ďakin da nake kwana na nemo number Abiey a call list na kira shi sai da wayar ta kusa yankewa sannan yayi picking.

“Hello”

“Hey Beautiful”

Na yi murmushi kamar yana gabana.

“Mama tace na tambaye ka mutanen da saka su tafi da Baba ina, za su kai shi?”

Sai yayi shiru kamar be fahimci tambayar tawa ba, wata kila kuma ni din ce ban fada da sigar da zai fahimce ni ba.

“Abiey”

“Hiayatee tambayar shi kawai za su yi su dawo da shi”

“Kamar ya tambayarshi? Kana ina?”

“Gida”

Na zauna ina ambatar sunanshi.

“Abiey idan wani abu ya samu Baba ba zamu ji dadi ba, domin yana a matsayin uba ne a gare ne, kuma. Mijin mahaifiyata ita kanta ba zata so wani abu ya faru ba, yanzu haka kuka take ta yi”

“Mama?”

“Ba ki fada mata abun da yayi ba?”

“Na fada mata, har korar mu ma yayi saboda zuwanka amman duk da haka hankalinta a tashe yake sai kuka take ita ce ma ta ce na kiraka na yi magana da kai ko kuma na bata ta yi magana”

“Zan saka su kawo shi”

“Amman kar su mishi wani abu dan Allah”

“Okay”

Ya amsa min muryarshi kasa kasa kana jinshi ka san ranshi a bace yake.

ABIEY POV.

A fusace ya fita daga unguwar irin fusatar da ace za a tara mashi Baba a gaban mota zai taka shi ne ya wuce, hakan ya saka be tafi gurin Ammy ba sai kawai ya nufi Masarauta gurin Anty Amarya, har daf da entrance din kofar falonta yayi parking ya fito yana jin wani zafin azaba da zuciyarsa ke masa saboda bacin rai, har wani huci yake a lokacin da ya shigo falon. Aisha da Siyama yar Hajiya Lami dake zaune a kujera ďaya suna duba wani lace suka masa sannu da zuwa amman be amsa musu ba sai ya zauna ya daga kanshi sama, sai kuma ya saka hannunshi aljihu ya ciro wayarshi, contact list dinshi ya shiga rabon da ya kira babban Yayanshi su gaisa har ya manta wani lokacin ma har shi yayan ke kiranshi su gaisa idan aka dauki lokaci domin ya san halin kanenshi. Amman a yau ya ji yana bukatarshi domin shi ne kawai zai yaye mashi damuwar da yake ciki a yanzu, ya san idan ya fadawa Mai Martaba wata kila zai masa fada ne idan kuma be mashi fadan ba zai saka bakinsa a ciki ba, wayar bata dade tana ringing ba yayi picking cikin barkwanci kamar yadda suka saba.

“A.B yau ka tuna da ni”

“Kanal dole ce ta saka wani abu bake son ka saka yaranka su yi wani aiki a nan”

“Kana magana kamar kana bani umarni who's the elder?”

“Come on Bro I'm not in the moon mutumen ya bata min rai over”

“Yayi maka?”

Abiey ya gyara zamanshi ya busar da iskar bakinshi, Aisha da Siyama sai kallonshi suke ba ma kamar Siyama da ta samu abun labartawa Mahaifiyarta, Aisha kuma na damuwa da halin da ďan'uwanta yake ciki ne domin ta lura da hakan tun farkon shigowarshi. Kamar mai rubuta labari haka Abiey ya fada ma Yayanshi abun da ya faru, kasa kasa Aisha ke satar kallon Siyama da idonta yake kan Abiey kamar zai fado tsabar gulma da maida hankali tana saurarenshi. Abiey ya busar da iskar bakinshi ya dora kafa daya kan daya.

“Darasi kawai nake son a koya masa kuma yau din nan ba sai gobe ba”

“Shikenan ka turo min address din, but ka kiyaye shiga irin area nan, that's why ba kowa namiji yake son neman aure a karamin gida ba”

“I don't care as long as ina son yarinya su waye iyayenta be dame ni ba, i will text the address”

Ya sauke wayar yana cika ma bakinshi iska, Aisha ta kalli kanwarta Siyama.

“Siyama ki tafi da lace din, idan kawo mana ni da Narjis”

“Okay”

Ta amsa sannan ta mike tsaye ta fice tana ta waigen Abiey. Aisha kuma ta tashi ta nufi ďakin Anty Amarya. Yana sauke wayar ya aika mashi da address din, sannan ya kishingida jikin kujerar ya rufe ido, ba dan Zahra ba da Allah kadai ya san yadda zai yi da mutumen nan, domin a yau ya bata mashi rai fiye da ďanshi.

“Abiey....”

Ta kira sunanshi tana saukowa stairs din da saurinta Aisha na biye da ita, gyara zamanshi yayi ya kalli Anty yana jin kamshi na sarawa.

“Me ya faru? Aisha ta ce ka shigo cikin bacin rai”

Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya labarta mata abun da ya faru.

“Da alama dai gaba dayansu ba su da mutunci”

“Ba shi ya haifi Zahra ba, ba su hada komai da shi ba sai abokantakar da yake da Babanta sai kuma auren mahaifiyarta da yake yanzu”

“Abiey ka saurare ne”

Ya juyo yana fuskantar ta.

“Ka dagawa area kafa ita kanta Zahra ka bata time na san a yanzu kuna son juna kai da ita, amman ka sani abu kadan zai iya ja maka matsala kuma kasan waye mahaifinka ya kamata ace kana barin wani abun ko dan wani”

“Babu abun da zai taba mutunci ko martaba a nan balle har ya shafi Mai Martaba, kawai dai bana son Ammy ta hana ni aikata abun da na yi niya ne shiyasa ban je gida a haka ba”

“Yana da kyau duk abun da zai zubar maka da mutunci ka kiyaye Abiey, ba dan yau ba tun ranar da ka fada min cewar Zahra ta yarda da kai ina son na yi magana da kai ya kamata ace kana tunani idan zaka yi abu”

“Anty kin san yadda nake son Zahra bana son ki fada min wata magana marar dadi akan ta please”

Ya fada ta sigar da zata fahimta ita kuma bata da wata mafita sai ta hakura ta kyaleshi domin ta fahimci ba zai gane karatun ta a yanzu ba. Mikewa yayi tsaye

“Zan tafi sai da safe”

“Allah ya ba mu alheri”

Ya amsa da Ameen sannan ya fito cikin gidan ya nufi motarshi, da fari da ya shiga motar sai ya kwantar da kujerar ya kunna motar ya kara gudun ac har lokacin ji yake kamar hukuncin da ya saka ayi ma Mahaifin Deen be wadatar ba.

“ƙut”

Yayi kwafa sannan ya tashi zaune yayi reverse ya fice daga gidan gaba daya. Kamin ya isa gidan Ammy Zahra ta kira wayarshi, sai da ya hade yawu sannan ya yi picking.

ZAHRA POV.

Haka muka kwana cikin zullumi da tunani halin da Baba yake, washe gari ana saukowa daga sallah asuba Yayan Baba ya kwankwaso mana kofar wato Baba Mani domin Mama ta kira tun cikin daren ta fadawa Matarshi sai dai be samu zuwa ba sai yau. Da ni ya fara gaisawa kasancewar ni na fara bude mashi kofar gidan ya amsa min hankali a tashe irin na dan'uwa mai damuwa da dan'uwanshi.

“Ina Maman ta ki take?”

“Tana ciki”

Na amsa mashi sannan na nufi dakin Mama kamin na karaso sai gata ta fito sanye da Hijab idonta a kumbure carji na rike a hannunta.

“Yaya Mani ne?”

“Eh an tashi lafiya”

“Alhamdulillah Ammy Bismillah”

Gaba dayan mu muka dunguma muka shiga dakin, ni na zauna a kasa ita kuma ta zauna kan gadon Baba Mana ma kasa ya zauna kasancewar babu wani abun zama kuma ba zai yiyu ya zauna kusa da Mama ba.

“Jiya ko da kika kira ji ina hanyar dawowa daga Kwarzo, kuma ban shigo da wuri ba shiyasa ban samu na zo ba”

Mama na matsar kwalla ta labarta mashi abun da ya faru, sai ya girgiza kai yana.

“Subhanallahi abu be yi dadi ba, Shi ma dai ai ba a haka talaka ma ba zaka taba wani ba ka zauna lafiya balle masu gari, yanzu ga abun da ake gudu kenan ai”

“Kuma ba abun da ya fi daga min hankali kamar rashin sanin inda aka kai shi”

“Shi yanzu mutumen ina za a ganshi? Sai a bashi hakuri ko zai ji ya hakura ko kuma ki yi mashi magana Zahra”

Ya karasa yana kallona. Sai na dago na kalleshi for the first time a yanzu na ji rashin kyautarwar abun da Abiey yayi domin Mama na ta damu kuma na san sauran yan'uwanshi ma za su damu, kuma kowa laifina zai gani domin a dalilina komai ya faru. Kamar Baba Mani ya san tunanin da nake kenan sai na jinkayo muryarshi yana fadar

“Amman tsakani da Allah Zahra bata yi dadewar da za a ce ta fara kula maza ba a yanzu, kuma indai a kan haka ne yayi magana yana da gaskiya domin Zahra ni kaina ya ce a gurina balle kuma shi, ya kamata Mutumen nan ya girmama shi a matsayinshi na magabacin Zahra”

Na sauke kaina kasa, Mama ta kasa cewa komai sai dai ina karantar kunnar ranta da ya nuna a fuskarta, lokaci daya muka mike tsaye cikin tashin hankali kowa da kalar salatin da yake ni kuma na dora hannu saman kai na duke kasa saboda mugun karar da na sake ji mai kamar jirgi ya fado.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”

Mama ta fada sannan ta riko hannuna muka fito daga ďakin, sai muka tsinci kam mu a tsakar mai kamar da tsakar fili, domin an rushe katangar dake gaban mu wanda ta tare da kofar gidanmu, an kuma rushe wanda ke gefen gidanmu.

“Su waye wadannan? Me muka musu?”
Chapter 47 · 0% Book details