Sashe 35
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya furta sannan ya aje daga kai yana kallon harabar gidan tare da kurba ruwan, ajiyar zuciya ya sauke ya sunkuya ya aje ruwan ya dauki keys dinsa dake kan mini center tebur dake gurin ya juyo ya fito daga backyard din ya dawo cikin dakinsa, kai tsaye ya zarce zuwa kofar fita dakin kamar an korashi haka ya sauko stair ba karamin dadi ya ji ba ganin falon ba kowa, balle ya tsaya amsa tambayayiyin Ammy na ina zai je. Yana isa gurin kofar falon ya bude ya fita be san key din wace motar ce a hannunsa ba har sai da ya latsa key din wata kafirar BMW ta yi kara, sai ya zagaya tsakamin motocin ya nufi inda take ya bude ya shiga yana reverse ya kunna kai daman masu kula da shiga da ficen gidan tuni suka wangale masa gate. Driving kawai yake yana tunanin yadda zai wanke Zahra a gurin Ammy da Anty, musamman ma Anty da yake ganin ta fi kowa daukar abun da zafi.
In 35min ya iso kofar gidansu Yasmin horn yayi aka bude masa sai ya samu guri a harabar gidan ya faka, hakan nan kawai yake jin baya bukatar shiga ciki daman ba gurin Momy ya zo ba balle yace zai shiga ya gaishe ta, wannan zuwan na Yasmin ne kawai, wayarsa ya ciro dake aljihu ya kiran number Yasmin kamar ba zata dauka ba sai kuma ta yi picking.
“Fito gani nan waje”
Jimmm ta yi kamar ba ta ji abun da ya fada mata ba.
“Toh”
Ta amsa ya yanke sannan ya maida dubansa gurin kofar falon yana jiran fitowar Yasmin. After like ten min aka bude kofar ta fito tana sanye da doguwar rigar atamta sai mayafin da ta rufe jikin, bude motar yayi ya fito yana jiran karasowarta ita kam bata yarda ta kalleshi ba har ta iso inda yake tsaye.
“Barka da dare”
“How are you?”
Ya bukata kamar an masa dole sai a lokacin da kalleshi hawaye na sauko mata wasu kuma na taruwa a idonta.
“I'm not fine”
“Me too”
Ya furta yana dauke kansa ya kalli sararin samaniya da iskar hadari ke kadawa.
“Na zo na yi magana da ke ne akan maganar mu shiyasa ban shiga ciki na gaisa da Momy ba”
Yana maganar tana masa wani irin kallo kamar ta hade shi.
“Na yi magana da Abbah Musa na fada masa ina son a fasa zancen baiko...”
Sai kuma ta yi shiru, Abiey ya tattara dukan hankalinsa da natsuwarsa ya mika mata zuciyarsa na wani bugawar dadi.
“Ahen... Ina jinki”
“Ya ce ba zan raina musu hankali ba, ban isa na zubar musu da mutunci ba, miyasa ban fadi haka tun kamin su amsawa Mai Martaba ba, sai bayan sun amsa zan taso musu da wata maganar, wai ban isa na maida su kananan mutane ba, ba za su yarda matsala ta taso daga garesu ba, kuma babu fashin aure sai idan kai kace ka fasa....”
A take annashuwa da farincikin dake tare da Abiey suka gushe.
“What...! What do you mean? Yasmin ya zaki saka ni a matsala... Ya salam.. ”
Ya fada yana juyawa ya daki motar da mugun karfi, kana ya juyo ya rika hade kafadunta yana jijjigata da karfi.
“Yasmin ya zaki min haka? Tun abun na sabo da kin yi abun da na fada miki da yanzu haka be faru ba! Miyasa zaki saka mi a matsala?”
Sai ta amsa masa cikin kuka.
“Kai ka saka kanka a matsala Abiey, miyasa zaka saka zobe a yatsan da ka san idan har za a cire shi sai dai a gutsure shi? Miyasa zaka ambaci sunana a bagirin da zuciyata ta dade tana nema? Na sani ba zaka taba so ba Abiey ni kuma ban isa na bude zuciyata na cire soyayyarka ba....!”
Sakinta yayi ya matsa baya ya nuna kansa with shock, sai ta daga masa kai ta saka hannayenta biyu ta rufe fuskarta ta fashe da kuka. Baya baya Abiey yayi har sai da ya jingina da motarsa ya dafe kanshi ya duka a gurin yana jin wani zazzabi na taso mashi.
“Na shiga uku... Yau na ga Idi zigidir”
Sai kuma ya mike tsaye yana girgiza mata kai.
“Yasmin ba zaki iya zama da ni”
Ta cire hannayenta daga fuskarta tana kuka.
“Zan iya”
“Zuciyata babu wanda take so sai Zahra da Zahra ita kadai...”
“Zan roka maka Allah ya sassautawa maka son Zahra Abiey”
Addu'ar da tace zata yi ta yi farraku tsakaninsa da Zahra sai ya saka a take ya ji ya fara tsanarta.
“Amadadin kin min addu'a ki raba ni da Zahra, me zai hana ki yi ma kanki addu'a so na ya fita daga zuciyarki?”
“Kamin yau... Na roka a dare mabanbanta, ka min a kawo yanzu na roka amman ba a amsa min ba sai ma aka kara kawo kusanci a tsakanina da kai ta inda ban zata ba”
“Yasmin indai kina so so na hakika to ba zaki so na shiga matsala ba, kuma zaki so abun da na ke so”
“Indai har da gaske kana son Zahra to zaka fi kowa fahimtar halin da nake ciki, Ciwon So masifa ne Abiey da ace ina da iko da ban bari Son ka ya shiga zuciyata ba”
Ta fadi durkushe kasan guiwoyinta tana kuka, ita kadai ta san abun da take ji, ita kadai ta san halin da take ciki akan Abiey kuma tabbas da zata iya da ta cire soyayyarsa a zuciyarsa, gana daya sai jikin Abiey yayi sanyi, durkusawa yayi kasa ya rika hannunta sannan ya matsa kusa da ita sosai ya rumgume ta a hankali.
“I'm sorry....”
Lumshe ido ta yi tana jin kamar ta saka wuka ta tsaka kirjinsa ta shiga cikin jininsa ta kwanta, sai da ya tabbatar ta samu natsuwa sannan ya mike tare da ita tsaye.
“Ki shiga ciki ki huta zamu yi magana daga baya okay”
Dagowa kai ta yi ta kalleshi sannan ta daga da ga jikinshi tana jin kamar ta rayu a kirjinsa rayuwa ta har abada.
“Ka yi hakuri idan na bata maka rai...”
Ya hade yawun bakinsa.
“No dukanmu ba ma iya sakawa junanmu abu kuma ba ma iya cirewa, ko wace zuciyata tana juyawa bisa ga ikon da Ubangiji ya bata, da ace dan adam zai iya wani abu, na tabbatar da yanzu Zahra ta cire so na a zuciyarta, amman ta kasa saboda bata da iko akan komai, abun da ta yi min dazun yanzu ya kara tabbatar da da har gobe Zahra tana kaunata”
Yasmin ta yi murmushi irin murmushin nan da hausawa ke cewa ya fi kuka ciwo.
“Zahra ta yi dace Abiey ka rayu da soyayyarta na tsawon lokaci”
“Yasmin.... Zahra ta so ni ba dan wani abu nawa ba, ni da ita mun kamu da kaunar junanmu ba tare da mun sani ba, sannan Zahra ta cika duk wani sharadi da na ke so a mace, ko kadan bana son na auri mace da ita take so na ni bana son ta, saboda zan iya cutar da ita, Yasmin na shiga a zuciyar Zahra na nuna mata kauna kamin abubuwa su canja mana, ba zan manta lokacin data durkusa har masa tana rokon kar na fasa aurenta ba amman ban iya yin komai ba saboda Deen ya shiryar mana gadar zare, wannan ce damar da nake da ita wanda zan nuna Zahra cewar ina kaunarta irin kaunar da babu wanda ya taba yi mata irinta, ina son na rayu da Zahra fiye da yadda kike jin kina son rayuwa da ni....!”
Yana kaiwa nan ya bude motarsa ya shiga ya yi mata key ya bar Yasmin a tsaye ta bishi da kallo.
“Ciwon so yana dawainiya da kai Abiey, ni kuma be bar ni ba, ‘So’ baka kyauta mana ba”
Yasmin ta fada tana hawaye jikinta sai kamshin turaren masoyinta yake.
*** *** ****
Tuki kawai yake yana jin kamar bata son komawa gida, kuma be san inda zai je ba da ma ace irin da ne da Sauban be yi aure da a gurinsa zai tare.
“Miyasa abubuwa suke tasowa su shiga tsakanina da ke Zahra! Why why...”
Ya buga sitiyarin motar da mugun karfi.
“And kullum daga gurina matsalar nan take tasowa why me?”
Kamar mahaukaci haka yake fada da kanshi tana jin wani kalar bakinciki marar misaltuwa. Daker ya kalli wayarsa dake ringing ba dan Sauban ne mai kiran ba da ba zai taba dagawa ba.
“Miye?”
Shi ne abun da ya fada bayan ya amsa kiran.
“Are okay”
“I'm not”
“Okay maybe later”
“Fada min yanzu minene?”
“Nuratu ce tace min ta ga Zahra a gidan yayarta wai an gabatar da ita a matsayin yar aiki”
Guri ya samu ya faka motar sannan ya gyara zaman wayar a kunnesa.
“Zahra tawa?”
“Eh yanzu ta dawo daga gidan take fada min”
“Zahra fa? Anya ta san Zahra da kyau kuwa?”
“Ta santa mana kasan da ita suka je yi mata gaisuwa tare da Ammy da Dr, kuma na nuna mata hotonta a waya tace min ita ce”
“Wait.. kana da hotunan Zahra a wayarka?”
“Amman dai ka san ba wani abu ke tsakanina da ita ba ko?”
“Ina aka ce maka an ganta?”
“Tace gidan yayarta ubansu daya da ita, tace tana zaune aka gabatar da Zahra a matsayin wanda zata rika kula da babyn da yayar ta haifa”
“Me Zahra ta rasa da zata je ta yi aiki a gidan wani? Ina raye?”
“Ni ma abun da nake tunani kenan, tace yanzu haka tana gidan”
“Ina ne gidan?”
“Me zaka yi?”
“I need to see her”
“No idan ma magana kake son yin da ita ka same ta a gidansu zai fi”
“Zan tabbatar ne idan ita din ce, fada min wace area ce?”
“Zan maka text din address din, maybe ma ka san shi wani Alhaji Bashir mai kudi ne sosai kwana baya ma yayi hadarin jirgi, kuma ance be taba haihuwa ba sai wannan karon”
“Ban san shi ba, amman turo min address din”
Ya sauke wayar da matukar mamaki.
“Mi zai saka Zahra aiki a wani guri?”