← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 127

Sashe 97

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Zahra kenan, wato barazana kika dauki abun da na fada miki ko? To na rantse miki da Allah zan aikata matukar baki amince da kudina ba, ki yi tunanin halin da zaki shiga da kuma wanda ďanki zai shiga, da kuma wanda zaki jefa Dr Hamid, da Jamila balle kuma Mr Bashir da mahaifiyarki, ba fa kudi nake nema a gurinki ba Zahra face amincewarki ki aurene, har na baki dama idan baki son duniya ta sani zamu iya yin abun mu a boye”

“Ba zan yi ba, ka je ka yi duk abun da zaka yi, saboda kun maida ni ba ni da kowa sai ku rika juya ni yadda kuke so”

Na karasa cikin kuka, sai ya miko min wayarsa.

“Duba wannan, ina fatar dai baki fadawa Mama komai ba, kuma baki nemi shawarar kowa ba sai zuciyarki”

Ban karbi wayar ba, hakan kuma be hana ni hango takardun gwajin jinin da aka fadada a cikin wayar ba.

“Na ki ne da na ďanki, wanda aka saka Dr Zainab ta sauya, sauran na Mr Bashir da matarsa na suna ciki, wadannan original din ne ba fake din da aka bashi ba, ita kanta Dr Zainab bata san na dauki wannan ba domin ita ma zai jefata a matsala idan har Mr Bashir ya san gaskiya”

Guiyoyina ne da suka yi sanyi suka kai kasa, idaniya na zubda hawaye na daga kai na kalli Sauban.

“Wane irin rashin imani ne wannan Sauban? Me na maka? Miyasa idonka zai rufe ka aikata kwatankwatan zalinci da Deen ya taba aikata min, me na muku? Miyasa ma na sanku?”

“Idan har Deen zai kirki komai saboda ya same ki, ya kike tunanin ni da ba kirkira zan yi ba na fashe kwan kawai zan yi? Zahra na boye miki wani abu ne kawai amman tun daga lokacin da na fara saka kafata a cikin gidan nan na saka ran batawa da Abiey domin na san ba zai lamunci min na aureki ba, amman na boye masa har sai da na samu hujojin da zan dogara da su su yi min iso gurin neman aurenki, haka yanzu haka ba ma ga maciji da Abiey saboda ke, yan'uwansa sun dauke ni a matsayin macuci shi kanshi haka yake kallona, amman na zabi na jure komai saboda na same ki, sai a yanzu da kowa ya san da komai har iyayena na sanarwa sai kuma ki ce ba zaki aure ni ba? Ke ki wanke kanki ki fita free ni kuma ki bar ni a kunya da bakinciki da nadama, wai Zahra baki yarda ina sonki ba?”

“Mai sonka baka ganin ramarka idan har so na kake zaka so farinciki ka so kwanciyar hankalina, ba zaka nemi daga min hankali ba”

“Ba daga miki hankali nake ba, mafita nake nema miki, ko dan saboda Jamila da Mr Bashir, Zahra ko da wani abu ya faru rigar aure zata kareki, domin bana jin Jamila zata kyale ki a haka idan ďanki ya girma, zata yi ta tsammanin wata rana zaki dawo ki aure mijinta ko kuma ki kwace ďanki amman aurena zai kawai da komai Zahra”

“Bayan ka fallasa komai sai me zai biyo baya? Karshenta a ce za a rufe ni gidan yari, bayan wannan sai kuma me?”

“Zaki barwa iyayenki da ďan naki da kika saida tabo da ba zai taba goguwa a zuciyarsu ba, Zahra wannan ce dama ta karshe da zan baki, kuma ina kara jadadda miki idan har baki son kowa ya san da zancen aurena da ke, ba za a sani ba, zan aure ki kuma na sallame a lokacin da kike so”

Na mike tsaye.

“Kawai ka fito fili ka ce jikina kake so”

Sai yayi saurin kawar da fuska.

“Subhanallahi, idan na nace haka ai ban yi laifi ba domin ba zina na aikata ba, kuma ba ita na neme ki ba, zaki iya jurewa maganganun mutane akan aurenmu, amman ba zaki iya jurewa na siyar da cikin da kika yi ba, saboda haka idan kin koma cikin gidan nan kawai ki amsawa Mama da cewar eh kima so na, shikenan sai na sanar da iyayen su sami naki iyayen domin bana son a dauki lokaci”

Ya bude motarsa ya shiga yayi mata key yayi reverse ya bar ni a gurin tsaye. Komai ya zo min ta hanyar da ban yi zato ba, na kasa yardar Sauban ne yayi min haka gani nake kamar a mafarki komai yake zuwa min, duk yadda zan yi Mama ta saurari uzurina na yi amman bata yi ba saboda ranta ya bace sosai. Kamar wasu abokan gaba haka muka kwanta muka tashi da safe Mama bata son magana da ni, gaishe ma da na yi bata amsa min ba, cikin damuwa da kufuwa na fito waje na share BQ din na wanke kayan da muka bata, sannan na zauna kusa da wasu fulawoyi na rafka uban tagumi, ina ta tunanin abun da zai fitar da ni.

“Ya Allah idan abun da Sauban yake nufina da shi alheri a gareni, Allah ka saukar min da natsuwar amince, ka kawar min duk wani abu da nake gani, idan kuma ba alheri bane sharine ko cutarwa a garemu Allah ka musanya min ka kawo min mafita, shi kuma ka cire masa ni a zuciyarsa”

Ashe Mama na jin addu'ar da na yi, bayan na shafa addu'a ta fito ta zauna kusa da ni tana kallona.

“Ba wai bana son aurenku da Sauban din ba ne, ina duba abun da zai zame muku mafita ne, amman na lura kina sonki kuma shi ma yana sonki, saboda ki kwantar da hankalinki zan sami dangin mahaifinki zan sanar musu sai su saka masa ranar da zai je ya same su”

Na dubeta sai hawaye suka riga kalaman bakina fita, na kasa cewa bana wannan ne kudirina ba, kamar wanda aka yi ma asari haka bakina ya rufe rub na gagara furta komai, har lokacin ban iya labarta wa Mama barazanar da Sauban yayi min ba, domin ban san abun da zai biyo baya ba idan na fada mata.
A daren ranar Ummiter ta shigo BQ rike da waya, bayan mun gaisa ta mika min wayar.

“Za'a kira ki ku gaisa”

“Wa zai kira”

“Yaya Bashir shi yace na kawo miki wayar”

A take na samu kaina na faduwar gaba, hankalina yayi matukar tashi babu abun da zuciyata take raya min sai kalaman Sauban, kamar marar gaskiya haka na karbi wayar na rike ina ta kallon hoton Amir dake gaban screen din wayar, sai tausayin yaron da mutumen da ake ikirarin mahaifinsa ne ya kamani, ba su kadai ba har da yan'uwansa da suke nunawa Amir kauna a zuwan ďan Mr Bashir ne. Ta dayan bangaren kuma na san ban kyautawa Hajiya ba da Baba domin su ma za su so ganin jikansu ko da kuwa ace Deen yana raye balle kuma ba shi da rai.
A lokaci da kiran ya shigo sai na kasa amsawa jikina ya dauki rawa kamar mazari, Mama ma da kanta sai da ta lura da haka.

“Ki dauka mana”

“Ba zan iya ba Mama”

Na amsa cikin kuka, kiran biyu Mr Bashir yayi a wayar Ummiter da nake kyautata zaton Hajiya Jamila ba ta san da kiran ba, amman na gagara amsa kiran, sai da Ummiter ta dawo ta karbi wayar tana dubawa sannan na mike tsaye da sauri na fito daga dakin.

“Baki amsa kiran ba?”

Shi ne abun da ta biyo ni tana tambaya.

“Na amsa”

Ban bari ta ga hawayena ba na bata amsa, bayan na tabbatar ta fice daga BQ din na koma cikin dakin na bude gurin tufafina na dauko wayata na fito na kunna sai ga sakwanni kala kala na samu na Sauban wasu kuma na nuna kulawa ne daga Dr Hamid, sai da na kara matsawa sannan na kira wayar Sauban.

“Me ka fadawa Mr Bashir?”

Shiru na ji yayi kamar ba zai amsa ni ba, can kuma ya yi gyaran murya ya ce.

“Me kika tsammanin zan fada masa? Kin yi zaton wasa nake? Haba Zahra ba zan yarda na yi 2-0 ba”

“Hakan be dace ba Sauban”

“Miyasa ke ba zaki aikata abun da ua dace ba? Ban fada masa ba, na so ma lasa masa zuma ne kawai a baki, amman zan fada masa matukar baki amince da kudirina ba”

Wasu hawaye masu zafi sun sauko min.

“Dan Allah ka yi hakuri Sauban karka fada masa”

“Kin amince?”

Na daga kai kamar yana gabana, na runtse ido ina wasu hawayen da ban san ranar tsayarwarsu ba.

“Kin amince zaki aure ni?”

Ya sake nanata.

“Na amince....”

Na furta daker, halshewa har wani haldewa yake maganar na rabewa min kamar mai koyon magana...

[11/26, 7:15 PM] Oum_Nuwaira🥰: 6️⃣1️⃣

A gurin na gurfana na zauna ina ta rusar kuka, domin na san na saka kaina tsaka mai wuya, ko kadan bana jin kaunar Sauban a raina kauna ce irin wanda za a iya zaman aure tsakaninka da namiji.
Na kusan awa biyu a gurin ina abu daya wato kuka sannan na share hawayena duk kuwa na san hawayena ba za su boyewa Mama cewar na yi kuka ba. Kaina a kasa na shiga dakin ban yarda na kalli gefen da Mama take ba na nufi katifa na kwanata, Mama ta lura kamar bana son magana sai ta kyale ni bata ce min komai. Na kwanta ba dan na yi bachi ba bachi kuma be tukari idona yadda na ga rana haka na ga daren, na gagara runtsawa ko kadan sai ciwon kai da raba kusa da ya sauke kayansa a gurina ya hanani ko da juya kan. Akan idona aka yi kiran sallah asubahi, kamin Mama ta yi wani yunkuri har na yi alwala na shigo dakin, sai da na fara sallah nafila raka'a biyu sannan na gabatar da farillah. Karatu kur'ane ne ya biyo bayan azkar din safe da na yi na dauki kusan awa uku ina karanta suratul Yasin idan na gama sai na maimaita har sai da na samo min bachin da na gagara yi jiya yana neman ranko a idona. Sannan na rufe kur'ane na daga hannayena na yi addu'a bayan na jadda salati ga Annabina.
Chapter 97 · 0% Book details