Sashe 102
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya juya ya fice cike da girmamawa, a nan na takarkare na cire hijabina na aje gefe daya na dora pot din da ya nuna min na zuba mai na fara gabatar da aiki, tarugu da albasa da ya nuna min na daka mai uban yawa na zuba a ciki, ina kallon ruwan ya gama tafasa har ya kashe kansa amman na ki yarda ma fada saboda ban gama girkin ba bana son ya shigo ya tararda ni a haka, na zuba gurinshi da magi a tare na zuba komai na saka indomie na ja na tsaya, ban yi minti biyu da rufe tukunyar ba na bude na saka abu na motsa miyar na lasa, wani tsabar azabar yajin da na ji ban san lokacin da na daka tsalle ba na wurgar da spoon din dake hannuna ko ni da nake mayya bana tunanin zan iya cin wannan abinci. Kofar kitchen din ta falon na rufe na dauki hijab dina na saka na bude kofar baya na fice da gudu, kamar aljana haka na isa gida ina haki, Mama da Yaya Maryam suna zaune a inda na barsu zaune suna ta hira har lokacin.
“Ke lafiya wani barakar kika yi kuma?”
Mama ta tambaya Yaya Maryam kam sai barkewa ta yi da dariya.
“Zahra ashe haka kika yi da Baba? Gaskiya dole ki sha duka hannun Deen kam”
Ni kam ban bi ta kanta ba domin na san barakar da na tafka a yanzu ta ci uban dariyar da Yaya Maryam take.
“Mama wai Antyn su Hafsat tace na tambayeki me ake sakawa a abinci idan yayi yaji sosai”
“Anya? Ko dai wani abun kika yi?”
“Aa Mama cewa fa ta yi na tambaye ki, Islamiya ma zamu wuce yanzu da Hafsat”
“To ni Wallahi ban sani ba”
“Ana saka gawayi, ance yana rage yajin amman dai ban taba gwada yi ba”
Yaya Maryam na bada amsar na mika hannu na saci dan kullin maganin da Mama tace na maza ne, na fice da sauri, sai da na bi ta gidansu Hafsat na samu gawayi domin na san ba za a samu gawayi a gidan Ammy ba su da suke amfani da gas me zai hada su da hawayi, kamar wanda ta yi sata haka na dawo cikin gidan na samu kofar a bude kamar yadda na barta, ban ko tsaya wanke gawayin ba na jefa shi haka a cikin indomie sannan na dauko soyayen naman da ya bani na saka na sake motsa taliyar yaran. A kokarin ganin na burge Abiey na bude kofin ruwan zafin na kwance maganin na zuba masa maganin na kwayar dai sai da na murje na ganyen kuma a haka na zuba masa shi, na sake kunna hitar ta sake tafasawa da yayi na zube na tace masa na dauki cup biyu na zuba dora a tray na bude kofar na fito kai tsaye na nufi dinning na dauki kalolin lipton na saka na saka suga kadan na zuba kayan kamshin da na gani sannan na nufo inda suke zaune na risina na aje musu.
“Oh Zahra sannu da kokari ai da kin bar shi kin kira ni kawai na hada”
Abun da baka saba ba, jikina har rawa yake na yi musu hidimar, Sauban ma sai yawa yake da kokarina yana tambayar taliyarsa bata yi ba.
“Ta kusa yanzu zan kawo”
“Ya naga abun yayi dark green?”
Abiey ya tambaya sai na ce.
“Na hada kalolin liptons ne maybe shiyasa”
“okay thank you duk da dai ba ko wane kalar Lipton nake sha ba”
Ina jin lokacin da Sauban din yake ce masa.
“Kar dai ka gasale ta ka daure kawai ka sha”
Ni dai ban bi ta kansu ba na dawo kitchen din na cigaba da kula da indomie da ruwan cikin ma yayi mata yawa kuma yajin be rage ba sai ma baki da abincin ya dan yi wani bangare, sai na na sauke tukunyar na tsame rabin naman ciki na wanke a ruwa na cinye, sannan na rage ruwan dahuwar indomie na zuba magudanar ruwa da na gani a kitchen din na dauko plate na zuba musu na saka spoon biyu, na bude kofar kitchen din na fito sai na samu Abiey a tsaye yana ta wani abu mai kama da shillo yana kallon sama, Sauban kuma yana zaune a kasa da rabin kofin tea ya dafe kai, Abiey kam gaba daya ya shanye. A gaban Sauban na aje plate din indomie.
“Gashi nan”
Sauban ya dago daker ya kalleni sai kuma ya kalli indomie.
“Me kika saka a shayin nan?”
“Ban saka komai ba”
Na amsa ina dan natsawa baya cike da tsoro.
“Miyasa nake juyawa? Miyasa komai yake juyawa?”
“Yunwa ce ka ci abincin gashi nan na dafa maka”
Kitchen din na koma na dauko wani plate ina fifita nasa saboda abincib ya sha iska, har lokacin Abiey na tsaye sai gidaya yake da hannu.
“Ka ci ta sha iska”
Kamar mai jiran umarnina sai ya bude kafafuwa ya fara auna abinci soma daya ya daki kansa ya tande baki.
“Wai mutuwa.... Minenen wannan kuma”
Ya sake aika cibi na biyu, ni dai ina ta kallonsa ina jinjina kokarinsa har ya cinye rabin plate wata kila dai saboda yana jin yunwa ne, sai dai ina ganin wani abu mai kama da fitar hayyaci a tare da su, musamman Abiey da ya gagara zama sai kallon sama yake kamin na koma kallon cushion din gidan. Tashi na yi na isa gabansa na tsaya ina kallonsa.
“Abiey Lafiya?”
“Ina fa lafiya? Baki ne duk sun cika mana gida, ga su nan zai shigowa suke”
Na juya gabas da yamma kudu da arewa ban ga kowa ba, amman Abiey sai sannu da zuwa yake musu sai kuma ya dafe kansa yana lumshe ido.
“Ya salam, wadannan bakin da muke biki ake ne?”
Na waiga na kalli Sauban dake ta shan yaji yana son mikewa, amman ya kasa sai juya kai yake yana wani zazzago halshe kamar maye. Zuciyata bata raya min cewar abun da na zuba musu a tea ne ya saka su wannan abun ba, domin Mama ta fada min cewar maganin maza ne, ba na maye ba wata kila dai lokacin na shiga Kitchen wasu aljannu suka shigo cikin gidan suka shafe su, musamnan ma Abiey da baya cikin hayyacinsa gaba daya. A dole na rika shi ina kokarin zaunarwa ya ki ya zauna sai cewa yake wai bana ganin falon ya cika da jama'a, sai ya fara safa da marwa cikin falon kamar mai rafeti. Tsaye na yi cikin falon ina kallon ikon Allah, Sauban ya zama kamar dan maye yana ta aikin shan yaji yana shafa jikinsa da kansa, ban san lokacin da na fashe da kuka ba na nufi jakata na dauka na rumgume.
“Ni dai na shiga uku ban san kuma abun da ya faru ba, miyasa suke yin layi?”
Na tashi na karasa kusa da Abiey na bude qur'ane na fara binsa ina karanta masa ina tofawa, idan na yi kamar aya goma sai na dawo gurin abokinsa Sauban na karanta masa shi ma na tofa masa, amman ba wani canj, Sauban din sai bin kujeru yake yana son ya tashi tsaye ya kasa.
“Wayyo Jama'a a kai ni gida”
Jin haka yasa na rufe kur'ane na maida a cikin jakata na aje jakar a gefen kujera na nufi inda suka aje keys din motar wato kan hannun kujera na nufi kofar na bude na fita na nufi motar da suka zo na saka key din ina da murdawa daker na samu kofar ta bude sai na bude ganbu na dawo falon na rika Sauban daya gagara mikewa sai cewa yake a kai shi gida.
“Wacece ke?”
“Zahra”
“Zahra wa?”
“Fatima Zahra”
“A ina nake?”
“A idan Ammy”
“Wacece Ammy?”
“Mahaifiyar abokinka Abiey?”
“Minene kuma Abii?”
Yanzu kam ban san kalar amsar da zan bashi ba, sai dai na yi iya kokarina na ganin na mikar da shi tsaye amman na kasa, domin ni babu karfi shi ma kuma sai shan yaji yake yana lasar baki kamar tsohon maye.
“Ina Matata?”
“Ina zan sani ni, kana da mata ne?”
“Na dauka ina da ita, to Ina Mamata ko ita ba ba ni da ita? Kin san gidanmu? Ina ne nan?”
“Ban sani ba ni dai dan Allah ka yi shiru”
Ya ki yayi shiru sai tambayoyi yake sako min kala kala da ban san amsarsu ba, Abiey kuma ya ki ya zauna sai zagaye falon yake yana ta yi ma bakin da ban san su waye ba maraba da zuwa, cikin iya Allah na rika Sauban na mika mike tsaye sai ya sako min nauyinsa ni da shi mika fadi a kasa, sai na yi saurin tashi ina rika shi.
“Dan Allah ki kai ni gida”
“To ai shi ne nake son ka shiga motar sai na tuka ka tafi gida, ni ina zan san gidanku”
“Ta can ake bi, sai abi nan sai abi can”
Ya nuna min kofar kitchen, jin kamar tsayawar mota yasa na sake shi da sauri na nufi inda na aje talkamina na dauka na dauki jakata na nufi kofar kitchen na bude na tsaya a kitchen din har sai da na ji shigowar Ammy, salati ta saka ita da Anty Zainab tana tambayar lafiya, amman babu mai amsa mata a cikinsu Sauban din sai kiran a kai shi gida yake, Abiey kuma yana fadin gidan da baki babu gurin zama.
“Allah yasa ba wani sammun aka yi masa ba, matan uban nan sun saka shi gaba ga kuma makiya abokan wasansa”