← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 127

Sashe 46

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Wai Abiey yace yana sallama da Zahra a waje”

Yaron na kai aya Baba ya kwala min kira, sai na dora hannu na toshe kunnuwana ina jin kamar kar na amsa domin yanayin yadda ya fisgi murya gurin kirana kadai ya isa ya sanar min da bacin ranshi.

“Na'am”

Na amsa gabana na faduwa ina ta sake saken abun da zan ce mashi, ina fitowa ďakin tun kamin na karaso inda yake ya jefeni da tambayar da ban san ta ina zan amsa ta ba.

“Ban fada miki kar yaron ya sake zuwa ba? Ko ban fada miki ba”

“Ka fada min Baba amman....”

Sai maganar ta makale ko me zan ce ma oho gaba daya ji anke kamar kalmomina sun kare.

“Amman saboda kin raina ni shi ne zaki bari ya sake zuwa ko? To bari na fita na mashi magana da kaina”

Ya fada yana kokarin mikewa tsaye, sai Mama ta ce.

“Haba Malam wannan ba mutuncinka ba ne, be dace ba ko da ba Abiey ba ne balle kuma ace shi? Kamar baka san su ke da garin nan ba?”

Wani uban tsaki yaja ya mike tsaye sai na yi sauri na karasa na rike rigarshi.

“Baba dan Allah karka yi, bari na yi magana da shi zan fada masa kar ya sake zuwa”

Ganin yayi shiru be ce min komai ba ya saka na juya na koma daki na dauko Hijab na fice, a gaban wani gida dake fuskantar na mu da ake gyara ya faka motarshi, yana ganin na fito ya bude motarsa ya fito yana shouting.

“I knew it...”

Na karasa kusa da shi tashin hankali dake tare da ni yana kara bayyana a fuskata.

“Abiey dan Allah ka daina zuwa a nan idan ma ka matsa kana son ganina zamu iya haduwa a wani gurin amman ba a nan ba”

Ya matso kusa da ni sosai yana kallon fuskata sai ka rantse da Allah be taba ganin kyakkyawar mace irina ba, murya can kasa kasa irin ta masu neman kwantar da hankalin yaro ya ce.

“Okay, amman ki daina daukar lokaci mai tsawo ban saka ki a ido ba Zahra, ji nake kamar na sace ki na gudu Wallahi”

“Na ji yanzu ka tafi”

Ya daga min kai yana yawo da idonsa a kan fuskata, juyawa na yi na kalli kofar gidanmu sai kuwa na juya a daidai domin Baba ne ya fito ya nufo inda muke tsaye, juyowa na yi da sauri na kalli Abiey dake ta kallona kamar zai lashe.

“Abiey ka tafi yanzu”

A maimakon ya amsa min sai ya daga kai yana kallon Baba da ya doso mu gadangadan, baya bukatar na fada masa matsayin Baba a gurin, haka zalika ya san Baba ne mahaifin Deen tun kamin Deen ya aureni. Baba na isowa yayi masa sallama Abiey be amsa ba kuma be daina kallonshi ba.

“Malam dan Allah ka kama mutuncin ka bana son ganin kowa a yana zuwa sallama da Zahra”

Na juyo da sauri na tari numfashi Baba.

“Baba dan Allah...”

“Rufe min baki fitsarariyar yarinya”

“Please control your tongue, at least ya kamata ka yi magana da girmamawa ka san waye ni?”

“Ina ruwana da waye kai? Kudinka ko sarautarka bata dame ni ba, kaje can ka yi shashanci ba kofar gidana ba, dan haka ya zama karo na karshe da zan sake ganinka a nan”

Baba ya fada cikin daga muryar dake kokarin tara mana jama'a, Abiey ya saka hannayenshi aljihu yana kallon Baba da murmushin takaici a fuskarshi.

“Kamar kumbo kamar korenta...”

“Abiey dan Allah ka tafi”

Na roka ina hawaye.

“Zan tafi Zahra amman ki fada masa gobe zan dawo jibi ma zan dawo”

“Aa Dan Allah kai baka gane ba ne, Baba baya son zuwanka ya min gargadi akan idan ka sake zuwa na fita zai koreni dan Allah ka tafi Abiey...”

Abiey ya kalleni sannan ya kalli Baba har ya juya sai kuma ya juyo sakamakon wadansu kalamai da Baba yake fada marasa dadi

“Idan ba iska ce yarinya ko arba'in bata yi ba ka fara zuwa kana mata sallama, kowa ya ga Zahra ya ganka ya san ba aurenta zaka yi ba, dan haka kar na sake ganinka kofar gidana”

A yadda na lura kamar da gayya Baba yayi maganar cikin daga murya saboda hankalin mutane ya dawo kan mu, kuma ya samu domin tuni daidaikun mutane da suke nan suka fara kallon inda muke tsaye.

“Baba dan Allah ka bari dan Allah”

Ina rufe baki ya wanke min fuska da mari mai kyau.

“Ai duk ke kika ja min ba a taba jina da kowa ba unguwar nan sai yau, da baki kula shi ba da be samu wannan damar ba, kuma na fada miki idan ya sake zuwa nan sai dai ki bishi”

Wani abokin Baba ne ya zo yana ba shi hakuri, mamaki ya fara kama mutane ganin cewa Abiey wanda fuskarshi sananniya ce, kuma Baba yayi ne saboda ya tozarta shi da ni.

“Simple...”

Abiey ya fada naman fuskarshi na rawa alamar ranshi ya bace sosai. Ni kuma na dafe fuskar na juya da gudu na shiga cikin gida ina kuka...
[11/1, 7:25 PM] Oum_Nuwaira🥰: 3️⃣4️⃣

Da kuka na shigo gida na fada jikin Mama ina labarta mata abun da Baba yayi min, mikewa ta yi tsaye kamin Baba ya shigo cikin gida har ta kagara. Be shigo da sallama ba, ahasali ma yana shigowa ya hau Mama da fada.

“Na fada miki bana son ganin kowa kofar gidan nan ko?”

“Gaskiya Malam abun da kake yi be dace ba, na san kai uba ne a gurinsu amman kana wuce gona da iri, Zahra ko yar makota ce ta zo ta tsaya kofar gidanka be kamata ka yi mata wannan cin mutuncin ba balle kuma ace yarka”

“Aa ni ba yata ba ce da yata ce ai da ta ji magana ta, da bata tsallake sharadin da gindaya mata ba, kuma ke ma da baki tsaya a gabana kina sa'insa da ni ba akan ta”

“Wallahi ko ban san inda Zahra ta fito ba, dole na yi magana balle kuma ace tana yata, mutumen da ya zo gurinta ba mutumen banza ba ne balle ka ci mutuncinta saboda shi, har kana neman tara mata jama'a, wannan abun sam be dace ba”

“Oh yanzu ko kunya baki ji ace yarki na fita waje tana magana da maza? Yaushe mijinta ya rasu? Kuma yaushe ta haihu? Da har zata fara kula su? Kuma mutanen arziki ne za su kula mace mai biki?”

“Malam kana abu kamar baka san waye Abiey ba!”

“Toh waye shi? Dan yana ďan sarki? Ko kuma ďan yana da kudi? Sai aka yi me? Kofar gidana ya zo ba ni naje gidanshi saboda ina da ikon nace bana bukatar ganinsa a gidana, kuma daman na fada miki idan Zahra bata ta sake kula shi zata fitar min a gida, yau ma na sake nanatawa kar na sake ganinsa a karo na uku”

“Wannan dokar ta yi tsanani Malam”

“Idan ta mata tsanani ai sai ta san inda dare ya mata tun wuri, kin ga ba kare bin damo, daman ta saka kin fara sa'insa da ni a gabanta, nan gaba kuma ban san iya inda abun zai kai ba”

Yana rufe baki na mike tsaye ina mashi wani kallo mai kamada da harara.

“Ko a gidan nan aka halittoni Baba ba zan kwana a cikinshi ba yau”

“Zahra.... Babu ruwanki a wannan maganar”

Mama ta fada min cikin tsawa.

“Mama ba zan zauna a gidan nan ba, korata yake duk abun da yake yana yi min ne saboda na takura”

“Rufe min baki wuce ki shiga ďaki”

“Aa kar ta shigar min ďaki sai idan kayanta zata kwaso domin ba zata kwanar min a gida ba, ni zaki nunawa fitsara?”

“Zahra ba zata je ko'ina ba Malam, idan har Zahra zata bar gidan nan sai dai mu tafi tare”

“To saka mayafi ki bita, daman ai ke kike daure mata gindi tana yadda take so”

Mama ta kalleshi tana girgiza kai kamin ta ce komai muka ji an banko kofar gidan da mugun karfi kamar za a balla kofar manyan zaratan sojoji ne kusan su shida suka shigo cikin gidan, ni dai faduwa na yi durkushe jikina na rawa zuciyata kuwa kamar zata fasa kirjina ta fito saboda tsoro, Mama nata nanata Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, Baba kuma ya ranta a na kare sai ďakin Mama, aiko sojojin suka bishi da gudunsu har cikin ďakin suka kamo shi kamar wata bankarariyar kaza haka suka fito da shi kafafuwanshi na lilo, sai kuka yake yana ba su hakuri.

“Ku yi min rai, ku yafe min dan Allah, me na muku? Ku tausaya min ina neman abun da na ci”

Mama ma ta shiga ba su hakuri tana hadda hannayenta biyu guri daya, ni kuwa da na lura ba gurin kowa suka zo ba sai Baba sai na hankali ya dan kwanta daman na san za a riba daman can kare yana da haushin kura balle kuma yanzu da Baba ya ci mutuncin Abiey. Wani mahaukacin mari da suka mashi sai ya saki fitsari ni kuma na dafe kuncina biyu ina jin kamar ni aka mara, ganin suna kokarin fita da shi ya saka Mama ta bisu tana tambayar

“Ina zaku je da shi? Dan girman Allah ku yi hakuri”

Ko kula ta ba su ba suka fice da shi, ba dan hawayen da na ga yana zuba a idon Mama ba da sai na zuba ruwa kasa na sha domin murna. Ko ba a fada min ba na san Abiey ne ya aiko a tafi da shi hakan kuma yayi min daidai domin maganin biri karen maguzawa.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, abun da nake ta nunawa Malam kenan ya ki ya gane, wani talakan ma ba a taba shi a zauna lafiya balle kuma ďan sarauta ina dadin haka?”

“Mama mu ai babu ruwanmu korar mu ma yayi a gidan ai”

“Ke da yake baki da hankali ba, ai idan wani abun ya sake shi ta dalilinki za a ce, gashi kuma sojoji basa da imani kar su je su kashe shi nake tsoro”

“Ko ma me aka mashi Mama ai shi yaja wa kanshi”
Chapter 46 · 0% Book details