← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 127

Sashe 10

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Idan bata ra'ayi sai ta bi ta hanyar lalaba a rabu lafiya, ba wai ta rika nuna kamar ta fi karfin ayi mata haka ba, har fa ikirari take idai sai ta aure shi to sai dai Mai Martaba ya koreta wannan magana? Su su yi min, sannan yanzu kuma ita ina kokarin taro ta tana subucewa”

“Yes da na auri zuri'ar Lami kara na mutu ban yi aure ba, kara Mai Martaba ya koreni ba zan taba hada jini wannan Azzalumar matar ba”

Aisha ta fada da iyakar gaskiyarta domin ta tsani abokan zaman mahaifiyarta.

“Yanzu ki gabatar min da wanda kike so, idan na yi bincike na ga ya cancanta zan gabatar da shi gurin Mai Martaba”

Abiey ya fada mata sannan ya kalli Anty ya ce.

“Anty yanzu an daina zancen auren dole, please ki kyale su su zabi wanda suke so mana”

Ya saki kofar dakin ya juyo zuwa dakinsa yana fadin.

“Shiyasa bana son zuwa gidan nan kullum da kalar matsalar da take bullowa”

Wani kamshin dadi mai kwantar da hankalin mai shakarsa dakin yake saboda turaren da Anty ta saka, saboda ta san danta mai son kamshi ne sosai. Sai da yayi wanka ya fito ya shirya kansa ya sannan ya hau saman gadon ya kwanta ya dauki wayarsa ya kira Sauban suka gaisa, sannan ya kashe ya kira yayarshi Dr Zainab yana tambayar ko sun ce gaisuwa.

“Mun je mun kai mata abinci Ammy kuma ta bata kudi”

“How is she?”

“Lafiya kalau, amman ta so fada min magana.....”

Murmushi yayi lokacin da Dr ta fada masa abun da Zahra ta yi masa.

“Za ta yi saurin yafe mana ba, i hope dai baki fada mata wata maganar marar dadi ba?”

Ta hade yawun bakinta.

“Ban fada mata ba”

“Thank You”

Ya sauke wayar yana murmushi babu abun da idonsa suke nuna masa sai fuskar Zahra. Bayan Sallah La'asar ya shigo bangaren Anty ya shiga har dakinta ya zauna a saman kujera yayinda take zaune kasa tana cin abincin da bata samu ci ba da rana.

“Mai Martaba zai dawo da wuri yau?”

“Wallahi ban sani ba, da dai ka shiga bangaren Mama Lami ka bincika domin ita ke da girki yau”

“Anty ke ma kin san ba zan shiga 6angarenta na tambaya ba, ina son magana da shi ne face to face”

“To yau da gobe duka girkinta ne, kuma yau ina tunanin suna da wani taro da za'ayi na masu cutar shanyewar jiki da kungiyar unicef ta shirya har da Governor na ji ance zai je gurin”

“Okay, zan tafi gurin Ammy Maybe gobe na shigo da wuri sai na yi magana da shi”

Ya fada yana Mikewa tsaye.

“Abiey karka aikata abun da zai bata tsakaninka da mahaifinka, Mama Lami tana shirya komai ne saboda tana son a samu matsala na fahimci shiyasa na so ku bi abun a hannu, idan ma yaron ya zo ta nuna masa bata sonsa a fuska in dai yana da hankali ai ba zai dawo ba”

“Amman kika san abun da aka shirya a tsakaninsu? Ba lallai idan ta nuna masa yar fuska ya guje mata ba, ke dai kin Mama Lami ba zata aura mata kenanta haka nan kawai ba dan Aisha ta jidadi sai dai idan kanen ba mutumen kwarai ba ne ko kuma akwai abun da take hari”

“Duk da haka dai ku bi abun a sannu, sun san yadda suke su gyara kansu gurin Mai Martaba hakan ya saka basa taba laifi a gurinsa, makirci sun iya shi har sun gaji, dan haka ku bi a sannu”

“Inshallah”

Ya fada sannan ya fice daga dakin, dakinsa ya shiga ya dauki keys dinsa ya sauko da kuzarinsa yana dialing number Sauban. Yana fita falon Sauban na picking call din.

“Ya....”

“Gida nake son a samo min?”

“Gida kuma? Wane iri?”

Sauban ya tambaya with confused din da ya bayyana har a muryarsa.

“Irin wanda zan iya zama, gidan dake kusa da na iyayen Zahra, but don't let any body knows ni na siya gidan, idan ma babu babban gida a gurin ka siya min kanana sai a rushe su a gina upstairs ta yadda zan a iya hangen cikin gidansu”

“Wait... Abiey mi zaka yi?”

“Zama mana”

“Why?”

“Why? Idan ana maganar Zahra har kana tambayar dalilina na aikata abu? Kai kana ganin yanzu zan iya yin wasa na bari ta subuce min? No”

Ya fada yana yi ma motar keys da hannunsa daya.

“To amfanin me siyen gida a gurin zai maka?”

“I want Zahra to be last thing da zan gani kamin na yi bachi, kuma i want her to be first da zan haifa fara gani idan na farka, duk yadda zan fada maka ina son Zahra ba zaka gane ba, Sauban ina son Zahra wani irin da wata kila nan gaba sai ka rabu da ni akanta, ni kaina ban san wane irin so ba ne”

“Toh Aĺlah ya kawo maka sauki yasa Zahra alheri ce a rayuwarka, kuma ya baka ita yasa ta fahinceka”

“Ameen Sauban baka taba burgeni irin yau ba thank you Dude”

Ya sauke wayar tare da danna horn, wa motar dake gabanshi.

“I can't wait Zahra na labarta mayuyacin halin da na shiga bayan rashinki i will tell you all about it, i love you more than i did before, i miss you just because i don't ses your face nothing change no one can take your place”

Ya kai hannu ya shafa fadaddan kirjinsa yana murmushi.

ZAHRA POV.

A gidan na kwana sai na fi jin dadi bachi ma fiye da gida, domin a gadon karfe na kwana mai lilo, bayan na yi sallah na sake komawa bachi mai kama da na wahala, ban farka har sai da Hafsat ta tashi ni da kanta na sauko ina tambayarta inda zan samu brush da man goge baki sai ta kira wani yaro ta ba shi kudi ya siyo min na wanke bakina na wanke fuska na dawo dakin Inna na sha kuku na dora da dumame, duk abun da nake hankalina yana gurin su Mama, ko a wane hali suke yanzu? Sai dai idan na tuna dalilina na guduwa sai na ji kamar na tsira. Misalin tara muka kama hanyar gona ni da ita muna ta tafiya a hankali saboda cikin dake jikin Inna ma sai da ta so ta hana ni zuwa sai dai ganin na dage akan ina son zuwa da kuma Hafsat da ta saka baki ya saka ta bar ni muka tafi. Wadanda suke zuwa tare tuni sun yi gaba domin sun bakwai wasu takwas ba safe suka tafi ita ma saboda jira na ne ya saka bata yi sauri ba.
Ba mu yi wata tafiya mai nisa ba na samu gurin na zauna ina hutawa sai wai na ke fadi saboda gajiya.

“Anya kuwa zamu iya tafiyar nan dake Uwani?”

“Akwai nisa sosai?”

“Da dai mun fita da wuri da sai mu je gonar kusa amman yanzu kan sai mun yo yar tafiya kamin mu isa na san gonar dan Ali an cika ta yanzu sai dai mu tafi ta Idi dan bana son gonar da aka yi ma taro”

“Amman dai ki rika min ruwa kar muje na fara jin kishin ruwa”

“Bari na koma na siyo miki na leda”

Ina zaune a gurin ta koma ta siyo min ruwa ta dawo sannan muka kama hanya, muna tafe ina mata labarin yadda komai ya faru har muka isa, ita kanta da nake ba labarin hawaye take balle kuma ni mai bada labari domin abun sai ya dawo min sabo na samu guri na zauna ina ta rusar kuka.

“Ki yi hakuri Uwani, kuma ki zauna a nan har ki haihu amman kinsan mutanen karka ba kamar na birni ba ne, dole za ayi gulma duk da ba su sanki ba ace kin zo kin haihu a nan, kuma kin san idan ana takaba ba a kwaliya ba a zuwa ko'ina sannan zaki bar su Mama cikin tashin hankali da tunanin inda kike”

“Na sani, wannan ma lalura ce ni dai idan zan tsira da abun da yake cikina ban zan damu da maganar mutanen gari ba”

“Amman idan zaki bi shawarata ki samu wata wayar sai ki aika musu sako cewar kina cikin koshin lafiya kar su damu”

Na daga mata kai ba dan na gamsu ba, domin asiri zai iya tonuwa idan na yi haka za a iya gane inda na ke. Mun yi tafiyar da ban zata ba sannan muka isa cikin katuwar gonar da ni dai ban ga iyakarta ba, karkashin wani ice na shimfida dankwalina na zauna ita ta kallon yadda suke aikin gonar ita da sauran matan da suke gonar, rayuwar karkara tana da matukar burgewa suna ta aikinsu suna hira kamar babu damuwa a tare da su suna cikin farinciki abu kadan sai dariya ga kokari ko wace mace na iya kokarinta dan kar wata ta fi wata, akwai rijiyoyi da yawa a gonar inda ake debo ruwa ga mai bukatar sha ko yin wani abu da su, sai dai rijiyoyin ba su da marafe a sake suke.

ABIEY POV.
Chapter 10 · 0% Book details