Sashe 72
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A nan na gane ba ni da wani iko sai na mika hannu aka daura min rowa aka dauki jini ina kuka sosai, wata kila Dr Zainab da shi mijin Jamila su zata kukan daukar jinin nake sai dai ni kukan watan tonon asirina da ya kama ne nake yi, gashi ya biyo mana ta hanyar da ba mu yi zato ba, yace zamu je asibiti ashe zuwa zata yi gidan kuma tun da asubar fari kuma har da na matarshi aka dauka bayan na danshi.
“I trust You Dr Zainab”
Ya fada mata bayan ta dauki jini ta yi mana sallama, ita kuma ta daga mashi kai tsaye na yi ina kallonsu har suka fice daga BQ din ina jin kamar na bita na roke ta kar ta auna jinin ko kuma idan ta auna ta boye result din. Bayan mun shigo dakin tare da Mama na ji wani sabon kuka ya sake rufe ni
“Mama ko dai na tafi gidan Dr Zainab na roke ta kar ta tona mana asiri”
“Karki kuskura ki dai ki mikawa Allah komai ki yi ta addu'a kawai, Allah ya dubi zuciyarmu ya rufa mana asiri ba mu yi haka dan mu cutar da kowa ba, Allah ka da ka kunyata mu a cikin makiya ya Allah”
Mama ta rufe da addu'a ita ma tana hawayen domin ni da ita duk tsoron abun da zai biyo baya ya gama cinye mu.
ABIEY POV.
6pm
Abiey na zaune bayan motarshi Sauban na jingine da motar yana kallon wani gurin fuskarshi da murmushi bayan ya gama labarta mashi yadda suke yi da Zahra a jiya da dare har yanzu abun be daina saka shi dariya ba, abun da be sani ba Abiey na tsare da shi da ido yana karantar yanayinshi da nishadin dake bayyana a fuskarshi tun kamin ya zo a yau ya labarta mashi abun da ya faru Abiey ya ji komai a waya, code da ya saka a wayar Sauban duk wani kira da Sauban zai yi tsakaninshi da Zahra zai ji sai dai shi Sauban be san da wannan ba. Abiey tun jiya zuciyarshi ke tafasa daman can idan ya saurari wayar da Sauban yake da ita ko kuma Sauban ya bashi labarin cewa ya tafi gurin Zahra Abiey sai yayi da gaske yake iya cin abinci saboda wani bakin ciki da ke rufe, a jiya zuciyarshi tafasa take a yanzu kuma soyuwa take na ganin murmushi a fuskar abokinshi sanin silar murmushin na shi. Sauban ya juyo still yana murmushi ya kalli Abiey ya ce
“Zahra tana da wauta sosai some time the way she act tana burge ni”
Abiey ya watsa mashi wani kallo yana jin wutar kishi ya azalzalarshi.
“Sauban control your tongue taya zaka fada min acting din Zahra na burge ka? Remember aikinka kawai ka dauki hankalinta har ta aminta ta aure ka ba wai ta burge ka ba ko kuma ka so ta”
“Subhanallahi Abiey ba zan iya tarayya da kai a soyayya ba kar Allah ya nuna min wannan ranar, saboda na ce acting dinta na burge ni ba shi ke nuna ina son Zahra”
“I think ya kamata ka daga mata kafa for now ka daina zuwa gurinta har sai na bukata”
Har Sauban ya bude baki yayi magana sai kuma wata zuciyar ta hana shi ganin ran Abiey a bace, sai kawai ya nufi motarshi ya bude ya shiga yayi mata key da wani kallo Mai Kama da harara Abiey ya bishi haka kawai yake ta jin haushin shi kamar ba shi ya shirya masa neman kusanci da Zahra ba.
“Mtswwwww”
Yaja wani dogon tsaki zuciyarshi na buga da mugun karfi har saman T-shirt din dake jikinshi ana gani, da ace na Sauban ne yayi masa wannan maganar ba da mai raba shi da wanda zai kalli tsabar idonshi yace Zahra na burge shi sai Allah, yana jin wayarshi na ringing amman bacin rai ya hana shi saka hannu aljihu ya dauko wayar ma balle har ya iya amsawa, sai tsaki yake ta yi sai da ya gaji da zama a harabar gidan sannan ya sauka baya motar ya nufo cikin gidan ko kadan bs damu daya duba mai jero mashi kiran ba haka ya shiga falon mahaifiyarshi fuska babu annuri, Ammy dake kokarin tashi jin an fara kiran sallah a masallacin gidan ta kalleshi sai kuma ta yi saurin dauke kai domin bata son su hada ido a yanzu tana matukar jin kunyar shi.
“Aliyu Dr ta kira ni tace ta kira wayarka baka daga ba”
Abiey dake kara bata fuska yana jin kamar Ammy ta kara mashi bacin rai ne ya ce
“Ni ta bar ni da abun da ya ke damuna ni”
Ammy ta bishi da kallo har ya fara taka stairs din.
“Aliyu”
Ya juyo ya kalleta, sai dan sauke idonta daga barin kallonshi.
“Akwai abun da yake damunka ne? Na ga ranka a bace kuma gashi har ka furta abar ka da abun da yake damunka? Me ke damunka?”
Kokarin kirkiro murmushi yayi.
“Ahh.. Ba komai Ammy bari na yi alwala an fara kiran sallah”
Ya juya da sauri ya haye sama gaba, ko da ya sauko Ammy bata falon yana sauke nadin hannun rigarshi ya nufi kofar fita da kuzarinshi, yana daf da isa kofar masallaci Dr ta sake kiranshi haka ya amsa kiran kamar na mashi dole.
“Haba Dr tun da har kika kira ni ban daga ba ai kin san bana cikin yanayin amsa kiran ne kuma yanzu masallaci zan shiga”
“Wani abu na gani mai matukar daga hankali da tausayi Abiey”
“A ina?”
“Zahra ta aikata ta jafa kanka ciki mawuyacin hali mai fitar da ita a yanzu kuma sai Allah”
Abiey ya tsaya cak tun daga lokacin da sunan Zahra ya daki dodon kunnenshi.
“Miya faru da ita”
“Ba magana ce da zamu yi a waya ba, idan ka gama sallah ka same ni a gida kamin Abbansu ya dawo”
Abiey ya sauke wayar yana kallon ma'aikatan gidan dake shiga masallacin sai dai a badini zuciyarshi tana can gurin tunanin maganar Dr Zainab ta fada mashi.
“Miya samu Zahra?”
Ya tambayi kanshi gabanshi na faduwa domin baya son abun da zai daga hankalin masoyiyarshi a yanzu balle har ya taba ta.
‘Ko saboda zuwan Sauban ne?’
Wani bangare na zuciyarshi ya raya mashi, kamin ya sake jefawa kanshi wata tambayar.
“Ko wani abun suka mata? This time around idan mutanen nan suka taba ta ba zan kyale su ba, and if aka sake shirya wani makircin i will face Siyama kai tsaye”
Ya fada yana tuna maganar da Aisha ta yi mashi cewar tana ganin kamar Siyama ce ta fada ma Hajiya Kilishi da Mama Lami har aka shirya rushe musu gida da sunan shi ya aikata, sai da ya yaki shaidan da zuciyarshi sannan ya shiga masallacin ya fuskanci alkibla tare da mamu ya bi jam'i aka gabatar da sallah Magariba tare da shi. Ana sallame sallah shi ne mutum na farko daya fara fita masallaci cikin gaggauwa abun da be saba ba, domin idan an gama sallah ya kan tsaya har sai yayi tasbihi yayi addu'o'i sannan ya fita. A uzure ya shigo falon Ammy ya har zai nufi upstairs sai idonshi suka kai gurin key motarta dake aje a inda ta zauna dazun da sauri ya dauki key din ya juya ya fice, tun kamin ya isa gurin motar ya daga murya yana cewa masu gadin da suka fito masallaci a yanzu su bude mashi gate, kamar wanda aka cewa ga Zahra can zata mutu haka ya shiga motar yayi mata key ya fisgeta da karfi ya fice daga gidan daman tuni suka karasa gate din da gudu suka bude mashi, kamin ya isa gidan yar'uwarshi har jin yake kamar ya kirata a waya ta fada mashi ko minene daker ya daurewa zuciyarshi ya karasa gidan, gudun kar mai gadin gidan ya bata mashi lokaci ya saka shi fakin a bakin gate din gidan ya yi knocking din karamar kofar gate din gidan Mai Gadin ya leko ta yar karamar hanyar ido domin duba ko waye yana ganin Abiey ya bude kofar da sauri yana mashi barka da zuwa.
“Yauwa sannu”
Ya amsa sama sama sai zuba sauri yake, entrance din kofar falon da kamar gudu ya hau shi ya kwankwasa kofar ya danna door bell at the same time. Yarta ce ta bude mashi ta tarbe shi da murna tana.
“Uncle Welcome”
“Thank You where is your Momma?”
“Tana dakinta”
“Je ki fada mata na zo”
“Okay Uncle”
Yarinyar ta zuba da gudu zuwa dakin Dr Zainab, kanenta suka taso da murna suna mashi welcome sai ya mika musu hannunshi yana shafa kansu yana murmushi.
“Sorry ban zo da chocolate ba”
“Uncle Momma tace ka shigo”
Ya saki hannun yaran da sauri ya nufi dakin da yarinyar Dr Zainab ta fito yana isa ya tura kofar dakin ya shiga, zaune ya same ta kan carpet sanye da Hijab da alama yanzu ta gama sallah Magariba domin tasbihi take har ya samu guri ya zauna yana kallon fuskarta dake dauke da damuwa.
“What happen?”
Ta mike tsaye ta cire Hijab dinta ta aje gefe ta nufi gurin da jakarta take aje ta dauko wasu takardu da suke hade gudu biyu ta mika mashi, kallon takardun ya rika yi kamin ya mika hannu ya karba.
“Miye a ciki?”
“Gwajin jini ne da Alhaji Bashir ya saka na yi na shi da na ďanshi da na matarshi da kuma na Zahra”
“You mean mutumen da Zahra take zaune gidanshi?”
“Eh wannan na Zahra da ďanshi ne”
Abiey ya bude takardun da sauri yana dubawa, ba shiri ya mike tsaye yana kara karantawa.
“What this mean?”
Ya tambaya domin karanta tabbatarwa ba dan be fahimci turancin dake jikin takardar ba.
“Jinin Zahra da yaron nan Amir daya ne, kuma jinin yaron da na mahaifinshi da mahaifiyarshi ya banbanta”
Ta sake nufar jakarta ta dauko wasu takardu ta mika mashi, ya karba da sauri yana dubawa.
“Taya kika gano haka?”
Ya matsa baya ta zauna saman gadonta.