Sashe 57
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na amsa gabana sai faduwa yake ina jin kamar na fita motar na yi tafiyata. Ina ji ina gani ya fice shi kanshi waigena yake. Ban san kalar maganar da yayi da Abiey ba, ina jiran na ga fitowar Abiey sai na hango Sauban ya fito ya bude motar da nake zaune.
“Zahra Ammy ta ce ki shigo”
Gabana yayi dukan uku uku, taya Ammy da kanta zata ce na shigo?
“Aa ni ba zan shiga ba, dan Allah Sauban ka maida ni gurin da ka dauko ni”
Na fada muryata na rawa domin tsoro ne ya kama ni a lokacin, ni kaina na san wani lokacin bana tunani idan zan aikawatar da abu, da tun farko ban biyo shi na shigo cikin gidan ba.
“Abiey ne ba zai iya fitowa ba, shiyasa tace ki shigo”
“Ba shi da lafiya ne sosai?”
“Eh, kuma Ammy ba da wata manufar tace ki shigo ba”
Ban san lokacin da na sauko da Kafafuwana daga cikin motar ba na fito jin cewar masoyina babu lafiya, daman can gidan Ammy ba bakona ba ne, sai dai a yanzu da abubuwa suka faru marasa dadi. Bayan na fito ya rufe motar sannan ya wuce gaba ina bayanshi kafafuwana sai hadewa suke ina tafiya kamar zan fadi zaune. Sai da ya fara shiga cikin falon sannan na mika kafata ni ma ba shiga, babu kowa a falon ko tv da ake bari a kunne a yau kashe na same shi.
“Zauna bari na yi magana da Ammy”
Na zauna ba dan na so ba, sai dai babu yadda zan yi domin ni na kawo kaina, idanuwana na kasa har sai da na ji motsin saukowar mutum a stairs, sannan na dago ina kallon Ammy dake saukowa da kuzarinta, ba zan ce ranta a bace yake ba haka kuma ba zan ce tana murna da ganin ba, sai dai na lura da damuwa karara a fuskarta, mikewa na yi tsaye ina kallonta har ta sauko ta nufo inda nake.
“Ban gargade ki akan Aliyu ba Zahra? Ban fada miki cewar Mai Martaba yayi mashi mata ba? So kike ya tsabawa umarninmu? To idan har Aliyu ya zabi cigaba da zama dake ko kuma ya dage akan sai ya aureki to sai dai ya zaba tsakanin mu da ke, na fada miki a baya kuma a yanzu zan fada miki babu ke babu ďana har abada...!”
Magana take hawaye nake ina jin kamar kafafuwana ba za su iya daukata ba, Abiey ne ya fara saukowa da saurinshi Sauban na bayanshi.
“Ammy dan Allah ki yi hakuri....”
Kamin na karasa fadar abun da zan fada Ammy ta dauke ni da mari.
“Munafuka, na yi nadamar saninki da na yi Zahra kuma na yi nadamar fada miki sirrina, tsintacciyar mage ada can na yi tunani ke yarinyar mai kirki da zata iya rike min sirri ta ji tausayin ďana amman kalle ki saboda ke komai ya lalace, Mai Martaba ya saka auren Aliyu da Yasmin nan da wata uku saboda haka ina gargadinki da ki rabu da ďana tun wuri”
Abiey zuwa yayi ya shiga tsakiyarmu ya tare ni daga kalaman da Ammy take min.
“Haba Ammy haba”
“Ki yi hakuri ko yafe min na miki alkawari hakan ba zai sake faruwa ba”
Na fada sannan na juya sai Abiey ya sha gabana.
“Ina zaki je?”
Na kasa amsawa saboda kukan da ya ci karfina.
“Zahra miyasa kika zo a yanzu?”
“Ni na cilasta ta zo i just wanted to surprised you ban yi zaton abun da zai faru kenan ba”
Sauban ya fada cikin damuwa da rashin jindadin abun da Ammy ta yi, ni dai ban iya sake furta komai ba na nufi kofar na bude na fita sai Abiey ya biyo bayana yana min magana kamin ya sha gabana.
“Zahra ki saurare ni mana”
“Abiey...”
“Na'am”
Ya amsa tare da saka hannayenshi biyu ya tallafo fuskata.
“Ba zan yarda na zama silar lalata alakarka da Mai Martaba ba, ba zan bari ya kai mu ga zabe tsakanin ni da iyeyenka ba”
Ya fara share min hawayen da ba su gama sauko min ba, ban kuma san ranar da za su gama ba.
“Ammy ta fusata ne kawai amman zata sauko kin ji zan yi magana da ita”
“Wannan ba abu ne da yake tsakanin ni da kai kadai ba, a tsakaninmu ne mu duka Abiey, ni ma Iyayen sun samu matsala saboda ni ba zan bari ka samu matsala da iyayenka saboda ni ba, ba zan iya daukar nauyin ba, kuma ba zan iya bari ka tsaba ma umarnin Mai Martaba ba, magana ce ta gaskiya da gaskiya Abiey dan Allah ka nuna min kaunar da kake min kuma ka tabbatar min da ita ta hanyar hakura da ni a rayuwarka, inda har son da kake min na gaskiya ne to ka auri Yasmin kuma ka bi umarnin Ammy da Mai Martaba ta haka zan tabbatar da kaunar da kake min ta gaskiya ce”
Lokaci daya ya dauke hannayenshi daga fuskata yana kallon kwayar idona dake yawo cikin tashi.
“Komai zai daidaita Zahra”
“Komai zai daidaita idan muka hakura da junanmu, ba ko wace soyayya ce take nufin aure da kasancewa a tare ba Abiey, kuma ba duka masoya ne suke samun cikar buri ba, ka nuna min kauna na sani amman hakan ba zai gamsar da ni ba har sai ka bi umarnin Ammy, ina son ka Abiey amman soyayyarka bata yi tasirin da zata hana ni bin umarnin iyayena ba, iyayenka da nawa sun samu matsala saboda mu miyasa ba za mu hakura mu so farin cikinki su ba Abiey”
Na durkusa kasa na hade hannayena ina rokonshi.
“Ka dubi girman Allah ka tabbatar min da kaunar da kake min ta hanyar kaurawa min, ina nufin kauracewa ta har abada...!”
Ya dukoso ina kallona hawaye na gani suka sauko a kyakkyawar fuskarshi.
“Hakan zai tabbatar miki da ina kaunarki Zahra?”
Na daga mishi kai ina jin zuciyata kamar zata fado saboda bakin ciki da kuka da yake cina, mikewa yayi tsaye ya fara tafiya sai ni ma na tashi tsaye na juya ina kallonshi.
“Abiey kai ka saka aka rushe mana gida”
Tsayawa yayi cak ya juyo ya kalleni.
“Ba ni ba ne, amman zan nema miki gurin da za ku zauna a duk inda kike so”
“Bana son ko tsinke daga gareka, kawai ina son na ji daga bakinka ne saboda zuciyata ta kasa yarda kai ka aikata”
Na juya na cigaba da tafiya.
“Tafiya zaki yi Zahra”
Ban juyo ba, kuma ban fasa tafiyar da nake ba har na fice daga gidan. Sai da na yi nisa da tafiya sannan na duke kasa ina kuka kamar marar gata, sautin takunshi na ji a bayana da kuma kuma kamshin turarenshi.
“Miyasa zaki cilasatawa kanki abun da ba zaki iya ba? Taya kike kokarin raba zuciyarki da abun da idan babu shi ba zata rayu ba”
Na mike tsaye na kalleshi a fusace na ce
“Karya zuciyata take Abiey tace idan babu kai ba zan rayu ba, kamin na san da kai nake rayuwa kuma zan cigaba da rayuwa ko bayan babu kai, karya so yake yace zai tsaka ka tsaba umarnin iyayenka ko kuma ni na tsabawa nawa babu wannan ranar Abiey, kuma karya so kake min idan har ba zaka iya aiwatar min da abun da na roka ba. Hakan na nufin ba zan taba iya banbance soyayyar gaskiya da ta karya ba, ba zan iya banbance tsakanin kai da Deen ba dukanku kanku kawai suka sani ne kuma kuke so...”
Na juya tare da share hawayen da karfin tsiya na fara tafiya, sai na ji ya rumgume ni ta baya.
“Zan bi umarnin Mai Martaba Zahra kuma zan bi umarnin Ammy, zan tabbatar miki da cewar ina kaunarki irin kaunar da wani ďa be taba yi miki ba, amman hakan ba yana nufin na rabu da ke rabuwa ta har abada ba...! Ina mamakin yadda zuciya take iya bari bakinki ya furta min kalma rabuwa Zahra ba san yadda nake ji a zuciyata ba ba kuma zaki taba sani ba”
Ya sumbanci gefen fuskata.
“Na riga da na sani Deen ya yaye miki kaunata a zuciyarki Zahra, amman har gobe ina kaunarki i want to you haka kuma ina farinciki da ke Zahra, maybe today is the last of our lives or our memories, ina son ki sani a kusa ko a nesa ina tare da ke, idan kina bukatar tsaro ko taimako ki fada min i will be right beside you i still love you Zahra ki saka wannan a zuciyarki if you ever need save just called me”
Ya sake ji ya juyo da ni ya kama duka hannayena ya sumbanta sannan ya kai hannunshi ya taba fuskata, dayan hannuna kuma ya shafi fuskarshi a fuskarshi har cikin zuciyata nake jin sanyin hawayenshi da hannuna ke tabawa ya sumbaci cikin hannuna sannan ya saki hannayen nawa ya juya ya fara tafiya ba tare da ya juyo ba.
[11/7, 8:11 PM] Oum_Nuwaira🥰: 4️⃣0️⃣
Ban iya tafiya gidan Baba ba sai nufo gida cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara zuciyata kamar zata cire, kirji na wani irin zafi kamar an saka min garwarshin wuta. Daidai gurin da Sauban ya dauke ni a gurin mai napep ya aje ni sai na fita na mika mashi duka kudin da ke hannuna ba tare da na ce komai ba na juyo ina tafiya sai ya kira.
“Malama ga kudinki”