Sashe 125
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Ya sumbanci ni cike da kulawa, yadda ya fada haka muka yi, shi ya dauko min tufafi ya taimaka min na saka sannan muka fito ya saka ni a mota ya dauki hanyar gidansu yar'uwarsa. Kusan mu muka tashe su daga bachi ta taba jikin nawa ta rubuta masa maganin da zai siyo min sannan ta shirya mana abun karyawa, ba dan na so ba na ci kadan sannan na sha maganin na kwanta. Ko da na farka Abiey ba shi a gidan, sai wayata ya kira yayi min ya jiki bayan na gama karanta sakonsa. Sai da azahar ya dawo a gidan muka wuni a nan har dare a lokacin da yace zai dauke ni ya maida ni gida sai Labari ya canja domin bana bukatar zama a gidan a yanzu kasancewar ba shi a ciki. A dole ya hakura ya bar na kwana a gidan bayan Dr ta cilasta masa yin haka saboda tsoron kar na je can zazzabin ya sake dawowa.
Ba laifi na samu bachi a nan domin mun dade muna hira da Dr ta rage min kewar mijina har sai da na fara jin bachi sannan na shiga daki na kwanta, the following day na koma gidan Ammy da zama bayan Dr ta fada mata abun da yake faruwa, sai dai zama a gidan Ammy sai ya fi min bakinciki fiye da zama a gidana domin sauran bakin da suka rage na biki da ba su tafi ba idan Abiey ya shigo sukan tsokane shi su ce masa ango hakan kuma yana min zafi sai nake ganin kamar da gayya suke min.
Duk yadda Abiey ya zo na koma na cigaba da zama a gidan Ammy bata yarje masa ba, nima kuma hakan yayi min dadi domin bayan tafiyar bakin sai ya rage daga ni sai Ammy sai mai aikinta Jummai ne a gidan, idan zata yi girki ta kan kira ni na taya tana nuna min wasu abubuwan, tana fada min abubuwan da Abiey yake so da wandanda baya so, da kuma kalar abincin da mijina ya fi so, a dan zaman da na yi a gidan na kara karantar halin Ammy mace ce mai matukar saukin kai da kuma son zaman lafiya, domin a duk hirar da zamu yi zata ba ni labarin irin zaman lafiyar da suka yi da mahaifiyar Yasmin ne, da kuma yadda zan kwantar da hankalina kuma na nuna wa mijina yadda zai kwatanta adalci ko da ya kasa yin haka.
A cikin abubuwan da Ammy take yawan nanata min akwai koyon girki da kuma rage yawan kukan da nake da duk wani abu da zai daga hankalin mijina, ta fada min da iya girki ta kara kwance Mai Martaba a lokacin da ta zauna a gidansa, hakan ya saka na darsa a zuciyata cewar ni ma zan koya ko da na kara samun damar murza kambuna na cikakkiyar mace, sannan ta fada min na rike kamshi daya, wanda zai rika tunawa mijina da ni a duk inda zai ji mai irin kamshi, har ya zamana ba shi dadin kamshi wani turaren mata sai nawa.