← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 127

Sashe 67

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Aliyu karka tambaye ni abun da ba zan iya amsa maka baki da baki ba, karka kalleni da abun da Zahra ta fada maka, na aikata abun da na aikata ne saboda juya min baya da Mai Martaba yayi a wacan lokacin saboda shiga tsakanina da shi da kai, miyasa ka dame kanka har ka san abun da ba zai amfana maka komai ba sai dai ya haifar maka da damuwa da bakinciki, ni ma kuma ya haifar min ka san irin zafin da nake ji idan na tuna abun da ya faru tun kana karami balle kuma a yanzu da ka girma? Mai Martaba ya barranta kanshi da ni irin barrantawar da har abada ba zamu sake kasancewa tare ba, ba dan babu aure a tsakaninmu ba sai dan abubuwa da suka faru, na rai ne ka tun daga haihuwarka har zuwa girmanka ni kadai Aliyu, hakan ya haifar da zargi da yawa a zuciyar mutane amman na gode da Allah a yanzu hankalin Mai Martaba ya karkato gareka ya fara nuna maka kauna kamar sauran yayan da ya haifa, shiyasa ba na son wani abu ya shiga tsakaninka da shi da zai lalata mu'amalarku, domin abun zai fi yi maka zafi a yanzu fiye da rasa Zahra”

Kamin Ammy ta gama fadar kalaman da ta kumsa a bakinta hawaye da ya zuba a fuskarta ya fi a kirga kana kallonta ka san tana cikin wani irin magagi na bakinciki marar misaltuwa..

“Ashe da gaske tsanar da Mai Martaba yayi min ba ta asiri ba ce kawai tana da dalili”

Ya lumshe idonshi da suka cika da hawaye ya bude.

“Na bude ido ina kallon Mai Martaba a matsayin mahaifina sai dai tsanar da yake nuna min wani abun tambaya ne da na dade ina yi ma kaina, kuma. Zuciyata ta kasa natsuwa da shi Ammy miyasa kika boye min wannan?”

“Saboda alkawari ne da muka yi tsakanin ni da shi cewar babu wanda zai taba sani komai har kasa ta rufe Idon mu, hakan kuma be canja komai daga kasancewarka ďanshi ba domin har gobe kai jininshi ne...”

Abiey ya mike tsaye cikin wani irin yanayi na mamaki da bugawar zuciya yana kallon Ammy duk wata maganar da ya furta a yanzu ya furta ne kawai saboda ya samu amsar tambayar dake mashi yawo a zuciya a yanzu kuma ya samu ta inda be yi zato ba a take hawaye na wanke mashi fuska.

#Team Abiey
#Team Hamid
#Team Deen
#Team Bashir
#Team Yasmin
#Team Zahra
[11/12, 3:11 PM] Oum_Nuwaira🥰: 4️⃣5️⃣

“Na rayu a gidan Mahaifinka irin rayuwar da babu wata mace a duniyar nan da zata gwada min gata a gurin miji, ni ce mace mafi soyuwa a gurin Mai Martaba irin soyayyar da baya iya yin adalci a tsakanina da abokan zamana, wannan abun ya tsokane musu ido ciki har da yan'uwan mahaifinka da iyayenshi, akan ce na yi magani na mallake shi alhalin ban taba kai nera biyar gurin wani na ce yayi min magani na mallake Mai Martaba ba, ni na san babu wata mace da zata rayu a zuciyar Mai Martaba ya nuna mata kauna kamar yadda ya nuna min, wannan soyayyar da ya nuna min ita ta cutar da ni ita ta haifar da duk abun da ya faru a yanzu, duk wata hanya da za a bi a raba ji da mijina sai da aka bi kuma aka yi nasara, sherin kishiyoyi be bar ni na zauna lafiya ba, zaman da na yi a gidan na shekara daya ne kawai saki daya ya gagara gyaruwa a tsakanina da shi, na dawo na zauna a gidan nan na rayu da kai da sauran yarana har zuwa yanzu ban sake sha'awar sake yin aure ba, saboda mahaifinka ya maye gurbina ya auri Zuwaira (Anty Amarya) kuma na san har yanzu bata iya maye gurbin nawa ba, mahaifinka ya nunawa Zainab kauna irim wanda be taba nunawa yayan shi ba duk da kasancewarta agola amman yana sonta saboda kasancewar yata...”

Abiey ya koma ya zauna yana kallon Ammy dake kuka kamar ranta zai fita, be ce mata komai ba ita ma kuma bata sake furta wata kalmar ba sai sharar hawaye take kamin ta mike tsaye ta nufi upstairs da kallo ya bita har ta haye sannan ya saka hannu ya share na shi hawayen ya mike tsaye ya fita falon, bakin kofar ya tsaya yana kallon harabar gidan.

“Ba zan yi irin kuskuren da kuka yi ba, ba zan tsufa na kasa samawa zuciyata abun da yake so ba, Zahra is my destiny and she's here in my heart nothing can keep us apart”

Magana yake da kanshi yana taba sautin inda zuciyarshi take, ya saka hannunshi aljuhu ya ciro wayarshi ya kira Yasmin buga daya ta daga muryarta a sanyaye.

“Hello”

“Yasmin kina gida?”

“Eh”

“Gani nan zuwa”

Ta yi shuru tana saurare har ya kashe waya bata sake cewa komai ba, a tunaninta zai zo ne saboda wata maganar ko wani abun kamar yadda ya saba, tana dauke wayar daga kunnenta ta sanar da mahaifiyarta cewar Abiey yace zai zo.

“To tashi ki shirya mashi wani abun ke ma kuma ki gyara”

Ta kalli Momy da ta yi maganar ta ce.

“Ina tunanin akwai abun da zai kawo shi ba zuwa ne gurina kai tsaye ba kawai”

“Duk da haka dai ki shirya ya same ki cikin kwaliya shi ya fi”

“Toh”

Ta amsa sannan ta tashi ta fice daga dakin zuwa dakinta wanka ta fara yi tana fara shafa mai ya sake kiran wayarta jiki na rawa ta yi picking.

“Hello”

“Hey Beauty ina waje”

She take a deep breath kamin ta dauke wayar daga kunnenta ta kalli sunan Abiey dake rubuce a wayarta ta sake maida a kunnenta tana ganin kamar ba shi ya kira ta da suna mai dadi like ‘Beauty’ ba wani ne mai irin muryarshi kuma mai kama da shi.

“Ka dan jira ni kadan gani nan zuwa, ko kuma ka zauna a....”

Kamin ta gama ya tari numfashinta.

“No zan jira ki a mota”

“Okay”

Ta sauke wayar tana ji sani abu mai kama da faduwar gaba da sanyi jiki saboda kiranta da Beauty da Abiey yayi. Sama sama ta shirya ta dan shafa power kadan ta saka green abaya sai mayafin abayar da turaren da ta bata kamar zata tashi garin kano da kamshi, a dakin ta bar wayar ta fito ta nufi kitchen ta bude fridge ta dauko lemu da ruwa ta dora a tray da cups sannan ta rufe ta fito ta nufi kofar fita falon gabanta sai faduwa yake zuciyarta na raya mata Abiey ya zo mata da wani dadin bakin ne da zai yi amfani da shi ya roke ta ta sake cewa iyayenta ta fasa aurenshi, wata kila kuma Mai Martaba ya amince mashi da fasa auren ne ko kuma wata mafitar ya samu oho, ta tunani kala kala ta doshi inda motarshi take. Abiey da ya kwantar da kujerar motar ya kwanta ya juyo yana kallon Yasmin dake takuwa zuwa gurin motarshi kamin ta iso ya mike hannu ya bude mata front seat sai ta shiga ta zauna ta sauke idonta kasa ta kasa ce mishi komai, murmushi yayi ya tashi zaune da kyau yana kallonta.

“Na dade ban ga wata mace da ta yi kwalliya ta yi kyau kamar yadda kika yi ba Yasmin you look beautiful”

Ta dago ta kalleshi da tsananin mamaki.

“Yau da wacce ka zo?”

Yayi murmushin dake kara mashi kyau da kwarjini ya mika hannu ya dauki gorar ruwan dake saman tray dake rike a hannun Yasmin ya bude ya sha.

“Wani abun aka min da ya bata min rai, shiyasa na zabi zuwa gurinki na wanke zuciyata ko zan samu sa'ida”

“Idan akwai abun da kake so zaka iya fada ba sai ka yi gwaiďanci ba”

Wannan karon murmushin da yayi mai sauti ne, ya kara kurba ruwan.

“Ba ki yarda da ni ba kenan, Wallahi babu abun da ya kawo ni gurinki kawai rai na ne a bace kuma na ga babu gurin da zan je na wanke zuciyata sai gurinki”

“Abiey baka shan wani abu balle....”

Bata karasa ba saboda tana ganin kamar kalmar ta yi tsauri, sai ya karasa mata da murmushi a fuskarshi.

“Bana shan komai amman na sha giyar kaunarki ita ce ke juyana ni”

Ta dauke kai daga barin kallonshi ta sauke kafafuwanta kasa zata fice daga cikin mata domin gaba daya ita bata gane kan Abiey ba yau, sai ya riga bude side dinshi ya fita ya zagaya ya sha gabanta.

“Yasmin ba ina miki kalaman nan saboda na yaudare ki ko kuma ina neman wani abu daga gareki ba, no ina tunanin ya kamata mu watsar da komai a yanzu mu fuskanci rayuwa aure fa zamu yi idan ba mu fara fahimci juna a yanzu ba yaushe zamu fahimta? Ya kamata mu bar komai ya wuce ai”

“I know you are doing this just to make me happy, ba dan kana so na ba”

“Wa ya fada miki? A gurin wa kika ko yi wannan?”

“I know”

“No ina son ki Yasmin amman ba irin son da na ke yi ma Zahra ba domin ba zan miki karya ba, bana son wata rana ki tuna ni ni ce Abiey be taba so na ba amman ni na so shi sosai, dole ne na koyi kaunarki saboda kar na cutar da ke hakan ya saka ki tsani yayan da zamu haifa da ke nan gaba, kar wata ayi magana ta ko kuma ki tuna da ni ki yi nadama, a lokacin da bana raye”

Ta duka ta aje tray hannunta sannan ta dago ta dube shi.

“Wani ya fada maka zaka mutu ne?”

Sai yayi murmushi ya shafa kanshi.
Chapter 67 · 0% Book details