← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 127

Sashe 12

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ammy yau Mai Martaba yayi abun mamaki”

Tun kamin ta tambaya ya labarta mata, sai hawayen jindadi ya cika idonta.

“Mahaifinka yana alfahari da kai Aliyu, kawai ba zai iya fada maka ba ne, Mai Martaba mutum ne mai son ya ga dan'uwa yana son Yan'uwansa Allah ya maka albarka kuma na ji dadi na yi murna da na ji kana son Yasmin I'm very happy”

“No... kawai na yi kariya da ita na ni ban taba jin komai akan Yasmin ba”

“Then why do you mentioned her name?”

“Saboda na kare kaina ne mana, zan yi magana da Yasmin ai zan fada mata idan an tambaya tace bata so”

Ammy ya shafa kansa tana murmushi wani irin son ďanta take fiye da sauran, ta kai hannu ta dauki wani bangare na guava da take ci ta saka masa a baki, sai ya lumshe ido yana taunawa a hankali. Kamar an tsikare shi sai ya tashi zaune da sauri gabanshi na mugun faduwa irin faduwar nan ta faruwar wani abu da ba alheri ba.

“Lafiya?”

Ammy ta tambaya tana kallonsa.

“I don't know, gabana faduwa yake sosai look at this”

Ya nuna mata hannunsa tsikar jikinsa har tashi take.

“Something is wrong somewhere i hope Zahra is Safe”

Ammy ya girgiza kai.

“Zahra ko da yaushe Aliyu? What if a cikin yan'uwaka ne ma? Allah dai ya tsare ka yi ta ambaton Allah”

“Ammy i used to feel this duk lokacin da wani abu ya faru da ita”

Ammy bata ce masa komai ba, domin ya fara isarta da zancen Zahra yanzu kam.

ZAHRA POV.

Tun suna aikin ina kallonsu har bachi yayi gaba da ni, daman can ni da bachi ba ma rabo, bachin nawa be yi nisa ba na soma jiyo ihu da karar wani abu mai firgitarwa kamar cida, ina bude ban ga kowa ba a cikin matan da suke aikin kowace ta kama gabanta suna gudun ceton rai, ta inda nake jiyo karar na kalla wato samaniya, wani katon abu ne mai kama da karamin jirgi ya zo da gudu ya fado cikin gonar kamin na yi wani yunkuri har ya kai kasa, gudu nake son na yi amman tashin nawa ma sai ya zama aiki, irin jirgin nan ne mai kama da na yawo domin na sha ganin irinsa idan muka je dauko Abiey daga Airport, daga inda jirgin ya fadi zuwa inda nake kwance babu nisa sosai na samu kaina cikin wani irin tashin hankali marar misaltuwa, musamman hango mutumen da na yi yana kokarin ceton ransa wani bangaren na fiffiken jirgin ya danne, ga kuma wata na kokarin kamawa. Ba zan iya ganin rayuwa na bukatar taimako na kasa taimawa ba hakam yasa duk wani nauyin jiki da ciki da nake ji sai na neme shi na rasa da guduna irin na masu ciki na isa gurin ina jin abu na sauko a tsakanin cinyoyina zuwa kasan kafata kamar ruwa, dukawa na yi na saka iya karfin da nake tunanin ina da shi fifffiken sai dai abun ka da marar karfi ga kuma ciki ban iya dagawa yadda ya kamata ba sai dai na taimaka masa ya samu fitowa, yana fitowa ni kuma na fadi zaune a gurin ina wani irin uhu na fitar hankali domin cikina nake jin kamar zai bar jikina da karfin tsiya, mutumen da na taimaka ma ne ya saka hannunsa ya daga ni sama yana janye jikina kusa da jirgin saboda ya fara kamawa da wuta, be iya daukata gaba daya ba sai ya jani har kusa da wata rijiya ya aje kamar jiran ake ya yanje ni sai ya jirgin ya kama gaba daya da wuta mutanen karkarar da suka nufo inda jirgin yake suka koma da gudu ganin wuta, ni kuwa har lokacin ihu nake jinin kuma be daina min zuba ba....
[10/4, 9:55 PM] Oum_Nuwaira🥰: 1️⃣9️⃣

ABIEY POV.

Da tunanin hakin da Zahra take ciki ya wuni ya kwana kuma ya tashi, gaba daya zuciyarsa ta ki natsuwa, so yake ya san halin da sahibar tashi take ciki kuma babu hali, duk wani tunani da yayi da wata hanya da yake ganin zai bi ya san halin da take ciki ko zai iya taimaka mata ta tashe masa.
Suna fitowa sallah Isha'i wata dabarar ta fado masa, sai ya dauki keys din motarsa ya fice ba tare da ya fada ma Ammy gun da zai je ba, bata san fitarsa sai da ta ji tashin motarsa. Tafiyar minti ashirin ta kaishi gidan Dr Zainab, a bude ya tararda gate din gidan ita kuma tana tsaye tana jikin motarta tana magana da Babbar yarta Aslamiya.

“Is like fita zaki yi”

Ya fada bayan ya fito daga motarsa.

“Aikin dare nake”

“Uncle...”

Aslamiya ta fada tana mika masa hannu suka yi shaking.

“Go inside zan yi magana da Dr”

“Okay idan ka koma kace ina gaida Ammy”

Na daga mata kai yana murmushi, sai da ta shige falon sannan ya fuskanci Dr.

“Ina son ki min favor”

Ta kalleshi not saying anything.

“So nake kije ki duba Zahra”

“Seriously? Na ce mata me? Abiey yace na zo na dubaki? Da wani idon ma zata kalleni? Ka san yadda yarinyar ta tsane mu kuwa?”

Ya sauke ajiyar zuciya.

“Cikin hikima zaki yi, i just want to make sure she's fine jikina na raya min ba lafiya ba”

“Abiey listen to me...”

Kamin ta karasa ya tare numfashinta.

“No Dr this will be the last favor please”

Ta ja dogon numfashi ta sauke ba dan ranta ya so ba.

“Zan je da safe”

“No yanzu please kamin ki wuce gurin aikin, idan kin gani ko ji wani abu sai ki fada min a waya, but hankalina ba zai kwanta ba yanzu har sai na san halin da take ciki”

“Kai ba mala'ika ba kai ba aljani ba kai ba kowa ba sai ka rika cewa kaji kaza kaza Zahra bla bla haba”

“Ciwon so kenan mai hana mai yinsa zama lafiya”

Na fada yana murmushin dake nuna shi kadai ya san abun da yake ji.

“Amman zuwa gidan mutane da dare?”

“Ya fi sirri ai, kuma kin ga yanzu ba zan iya bachi ba sai na san halin da take ciki”

“Zan biya ta can kamin na je asibiti”

Ta fada tana bude motarta ta shiga, shi ma ya juya ya koma gurin motarsa ya shiga sai suka fita a tare sai dai direction din kowa dabam.

ZAHRA POV.

Ban sake sanin inda kaina yake ba, ban kuma san iya dakiko ko mintuna da na dauka a haka ba, wata kila ma nayi awanin da yawa. Sai farkawa na yi na ji akan wani gado mai yawo ina bude idon sai na ji bana gani da su da kyau, can sama sama nake jin yaniyar mutenen da wasu yareka da ba zan iya shaidar turanci ko hausa ko larabci ko kuwa wani taren ne na dabam duk ba zan iya ganewa ba a wannan lokacin, iyakar abun da na sani kamshin iskar da nake shaka ya sauya zuwa wani daban da bana so, ga wani irin zugi da murdawa da marata ke yi kamar abun cikina zai fito, na dan motsa saboda azabar ciwon da nake ji sai na ji wata muryar da ban sani ba sunan kiran.

“Malama Malama Malama”

Kalmar nake ji yana ta maimaitawa, kwakwalwata na ta hadawa amman na gagara fahimtar ma'anar kalmar da kuma yaren da yake magana da shi.

“Jini fa take bukata ta zubar da jini mai yawa...”

Na sake jin wata maganar da ban fahimci me take nufi ba, can kuma na ji wani ya ce

“Ku gwada jinina mana idan zai yi sai a saka mata”

Nan ma van fahimci abun da suke fada ba, ni dai taimako kawai nake nema idan suka ce zasu raba ni da abun da ke cikina ma zan yarda saboda azabar da nake ji, na maida idon na rufe ina numfashi kamar ba ni ba, bana jin kuzari ko kadan sai azabar murdawar mara, ina jin lokacin da aka daura min wani abu a hannuna aka buga hannu aka shafa min wasu ruwa sannan aka soka wani karfe a cikin jijiyata aka cirewa, komai kamar mafarki nake ganinsa.

“Hankali ba zai kwanta ba sai matar nan ta tashi she saved my life”

Wannan karon da yare biyu akayi magana sai dai hakan be saka na fahimci komai ba.

“Muje a gwada jinin”

Shi ne last sentence da kunnena ya jiyo min, sai kuma numfashin ya tafi dan sauran hankalin daya rage min ya cire gaba daya. Wannan karon na bude ido da dan kuzarina idon nawa kuma nawa kar ina ganin komai farin ceiling na fara arba sa shi fanka na juyawa a hankali, can kuma na juyo idona gorar jini ce abun da na fara yin karo da ita kamin na kalli hannuna da jinin ke shiga ciki, sai kuma na juya dama da ni na kalli Hafsat dake kwance tana bachi, da alama dare ne sosai domin alamu ya nuna haka yanayin yadda na ji tsit ta ko'ina ga kuma hudun da nake hangowa ta windows, na kai hannuna na taba cikina sai kuma na dan dago na kalli cikin, wata katuwar rigar ce a jikina sai kuma zanen da aka rufe min kafafuwana da shi.

“Alhamdulillah”

Na furta cike da nauyin baki, ina tabbatar da godiya ta ga wanda shi kadai ke kashewa ya raya, na yunkura ina rika karfen gadon na tashi zaune na mika hannu zan riko gorar ruwa sai gora ta fado kasa wanda hakan yayi sanadin tashin Hafsat.

“Uwani.... Sannu ya jikin”

Na daga mata kai ina nuna mata ruwa.

“Aa likitoci sun ce kar a baki komai sai an cire jinin”

“Ina jin kishin ruwa sosai”

“Ki yi hakuri kin ga dare ne, ba zai yiyu na kira likita ba tun da jinin ma be yi nisa ba gora ta biyu ce aka saka miki, kuma na karya alkawarin da na daukar miki na ji tsoro sosai saboda jinin da yayi zuba na dauka mutuwa zaki yi, na kira Anty na ce ta fadawa Mama kina nan gurina kuma muna asibiti dake”
Chapter 12 · 0% Book details