Sashe 26
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na amsa ina jindadin addu'ar da Mama ta yi masa, ni kam na san indai ba a yabawa masoyina ba to ba za a zage shi ba. Bayan sallah La'asar kiran Dr Hamid ya shigo wayar Mama da gangan na ki dagawa har sai da kiran ya yanke, fargaba nake kar a fada min cewar jajarin yayi ciwon ciki bayan ya sha nonona, yana sake kiran wayar gabana ya fadi sai da na yi Bismillah sannan na daga kiran na kai wayar a kunne ina kallon Mama.
“Hello”
“Zahra ya gida?”
“Lafiya Kalau”
Sai shiru ya biyo baya ni da shi babu mai cewa uffan har na kusan dakika ashiri.
“Hello”
“Yeah ina jinki daman na kira na fada miki za a sake gwada ba shi nononki a karo na biyu daga nan sai mu bincika mu gano daga ina matsalar take”
Lumshe ido na yi na kai hannuna kirjina ina jin wani irin sanyi a raina, domin ko be fada min ba na san nonona be saka ďana ciwon ciki ba.
“Ban fahimce ka ba”
“Zan kawo miki goro ne sai ki sake matsa nonon naki ki ba shi”
“Aa gaskiya”
Na amsa kai tsaye kamin na dora da cewa.
“Yawan matsar nonon zai iya sakawa mutane su gane, kuma ni ina jin zafi ba zan iya cigaba da yin hakan ba”
“Sai ya kenan?”
“Idan tana son na bashi nono sai dai ta kawo shi ya rika sha idan ya koshi sai a maida shi gurinta, shi ma kuma a bisa sharadi”
“Wane irin sharadi?”
“Zata biyani na shayar da yaronta, domin hakkin shayar da shi a yanzu ba a kaina yake ba”
“Zahra ya kike magana kamar ba ke ba? Ko kina ganin kamar kin samu wata damar da zaki wasa da hankalin mutane ne?”
“Ina zancen wasa da hankali a muhalin da zan taimaka muku? Ban ce dole ba fa idan kun ji kuna iyawa ne kawai”
Wani uban tsaki yaja ya kashe wayar. Sai na yi murmushi Mama ta kalle ni tana fadin.
“Miyasa kika yi haka?”
“Mama ai maganin biri karen maguzawa, idan ban musu haka ba ni za su fara disgawa a yanzu ma ai be nuna min nonon ya karbe shi ba sai cewa yayi wai za su kara gwadawa ba, kin ga ta nan zan gane idan ta gaske tana son yaron nan ko ba komai zan samu kusanci da shi, ina kallon wannan abun a matsayin wata mafita da Allah ya kawo min”
“Ina ji miki tsoron kar hakan ya janyo miki wata matsala a nan gaba”
“Babu wata matsala da zai janyo min da yardar Allah ke dai kawai ki taya ni da addu'a”
“Idan kuma ta yardar ki cigaba da zuwa kina shayar da shi, ba ki tunanin asirinta zai tonu? Kuma ke ma naki zai tonu? Domin mutane za su yi mamakin ace kina yawan fita zuwa wani gurin ga shi ko arba'in ba ki yi ba”
“Mama maganar mutane baya saka ni yin abu ko ya hana ni a yanzu, matukar kin amince bana shayin kowa lokacin da zan rasa mijina mutanen suna ina? Miyasa ba su kawo min dauki sun hada min ko da rabin kudin na yi magani ba? Sai yanzu za su fara magana? Maganar su ba zai dame ni ba”
“Tun yanzu dai sai ki tanadi abun da zaki fadawa Hajiya ba sai gaba ba, domin ina hango abun da tunaninki be baki ba a lamarin nan”
Na yi shiru ina sauke dogon numfashi.
[10/14, 8:36 PM] Oum_Nuwaira🥰: 2️⃣6️⃣
Ta mike tsaye da sauri ta sha gabansa.
“Haba Hubby miyasa kake da saurin fushi ne? Abu kadan sai ka hau ka fara fada ba zaka ma tsaya ka saurareni ba?”
“Me zan saurara? You're just try to kill my son, yaron nan baya samun lafiya idan ya sha nononki amman kin ki yarda kowa ya duba shi sai ďan'uwanki tun da kika samu cikin nan ba ki yarda da kowa ba sai ďan'uwanki har sharadi na gindaya miki cewar ba a nan zaki haihu amman kika bijire kika dauki kawarki kuka je asibiti sai kirana ka yi aka fada min kina gurin haihuwa, waya sani ko haihuwar da kika yi a nan ne ya janyo masa matsala?”
Ta yi murmushi duk wani abun da Mr Bashir zai fada ko ya nuna akan ďanta zata masa uzuri saboda ta san yadda yake son haihuwa tun kamin yau.
“Haihuwa a nan ba zai saka ya kamu da wani ciwon ba, ai da Hamid ya fada mana, kuma ba wani dalilin ya saka na ke son Hamid yana duba shi ba sai dan ganin na gida ne shi kuma kwararen likita ne, and duk wani bincike da ya kamata ayi akan nonon nan an yi ba a gano wata matsala ba, saboda har madara tana saka shi ciwon cikin nan ka ga ba daga nono ne kawai ba kuma jiya ma da ya sha be yi ciwon cikin ba na so mu dan jira mu ga idan abun ya bi haka ai mun fita ba sai mun fita waje ba”
“Duk kwarewar Dr Hamid akwai likitan da ya fishi kwarewa, kuma ba zai yiyu ace yaro idan ya sha nono ko aka ba shi madara yana ciwon ciki kuma ace babu matsalar komai ba, dole akwai matsala, so iya na yau ne idan yaron nan ya sake shan nono yayi ciwon ciki ni da kaina zan kai shi asibiti”
“Na yarda, amman idan ka akai shi na kowa ne likita zaka yarda da duba shi bana son likitan da be san kan aiki ba ya taba min yaro ka fi kowa sanin yadda na ke son ďan nan, kukan shi ma jinsa nake kamar na yi kuka”
Yayi wani kasaitaccen murmushi ya kai hannu ya taba fuskarka.
“Ke ma kenan da zan iya mutuwa ki auri wani ki samu haihuwa, balle ni da na san idan a yau na fadi a mutu ba ni da ďan da za a kasa dakiyar nan tawa a bashi kasonsa? Kin san iya kimarki da darajarki da kaunarki da ta karu a zuciyata saboda haihuwar nan da kika yi? Da ace wata uwar ce ta haifa min yaron nan ba ke da da kaunar da zan nuna mata zata saka na manta da ke na saboda soyayya da kaunar da na ke yi ma yaron nan, yanzu kuma da ya kasance ta dalilinki na samu yaron bana ganin kowa a gabana sai ke da ďanki, duk wata kauna da soyayya da na nuna miki a baya, sharar gafe ce kuma wasa ce”
Ya rumgume shi cike da jindadi ta lumshe ido, bayanta ya shafa yana jin wani irin kaunarta marar misaltuwa na kara tsarashi, shekara tara yana neman haihu Allah be bashi ba sai wannan karon.
“Lokacin da na fara jin kukan yaron nan sai da na fashe da kuka na farinciki, wai ďana ne na jinina nake jin sauti muryar kukansa, yaya rahama ne tabbas kuma ba zaka tana sani ba sai ranar da ka rasa ko ďaya, ko ba komai na san zan mutu na bar wanda za a kalla a tuna da ni”
Dagowa ta yi ta kalleshi sai ta yi arba da hawayen da suka cika idonsa har suka sauko masa, hannu ta kai ta share masa hawayen nata idon ma cika da hawayen tausayin mijinta, ba da yan furta cewa zai mutu sai dan tausayinsa na sanin cewar ďan da take ikirarin nasa ba jininsa ba ne, ita kanta da take ba ďanta ba ne. Wayarsa dake ringing ya ciro daga aljihunsa yana dubawa.
“Su gwaggo ne wata kila sun iso bari na tare su”
Ya fada fuskarsa da annashuwa domin ya san saboda a taya shi farinciki yan'uwa na nesa da kusa suke ta zuwa yi masa barka wasu ma suna tare a gidan, ta sake tana murmushin karfin hali sai da ya shafa bayanta sannan ya fice ita kuma ya juya ta nufi gurin gadon jaririn tana takawa a hankali har ta karasa kusa da shi ta tsaya tana kallonsa.
“Allah ya ba ni komai ban da haihuwa, na san mijina zai kaunarci yaron nan kamar ďansa alhalin ba ďansa ba ne, Allah ka yafe min wannan zunibin da na aikata da kuma wanda zan aikata nan gaba, ka rufa min asiri kar a gane komai har yaron nan ya girma”
Wannan karon hawayenta tare da murmushi suke, tabbas tana jin rashin kyautawa a abun da ta aikata sai dai bata da wata mafitar ne sai wannan, idan har ba ta yi haka ba ta san Mr Bashir zai iya auro wata kamar yadda ya sha yi a baya kuma su zo su haihu ya juya mata baya shi da yan'uwanshi, kuma a raba gado ba zata tashi da komai ba sai hakkin wanka kamar an fada mata shi zai rigata mutuwa, tana duba yadda yake da tarin dukiya ace idan ya fadi ya mutu bata da komai sai hakkin wanka, amman a yanzu fa? Yan'uwanshi za su kaunace ta daga ita sai ďanta, kuma mijinta ma dole ita kadai zai so haka kuma zata samu kaso mai yawa idan ya mutu domin namiji ne ďanta. Kusan a firgice ta juyo ta kalli kofar ďakin yaron da aka turo, domin tun kamin ya zo duniya mahaifinsa ya ware masa ďaki daya a cikin ďakunan dake kusa da nata kuma aka kawata shi da duk wani abun bukata irin na yayan turawa, a part dinsa ma sai da ya shirya masa wani dakin da yafi wannan da yake a ciki tsaruwa da kyau. Da karfi ta hade yawu ta kai hannu ta share hawayenta tana jin rigar tsadadden lace din dake jikinta yana sukarta.
“At least ya kamata ki yi knocked kamin ki shigo Ummiter”
“Shekaranjiya da na yi knocked na shigo kika ce zan tashi yaro yana bachi, yau kuma kin ce ya kamata na yi knocked, Anty Jamila ya kamata ki san ni fa ba yar aiki ba ce you can't just treat me anyhow just because kina matar yayana”
Hajiya Jamila ta yi wani gutun murmushin tana rausayar da kai.