Sashe 6
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Toh gashi an masa aikin be rayu ba, sai yaya? Dole ne a kama wannan likitan”
“Ki rufa min asiri dan Allah, karki bari kowa ya ji maganar nan idan yarjejeniyar ta fita sai na biya naira miliyan ashirin”
“Ba zaki biya ba, kuma dole za a barki da danki ko yarki, sai ma a kama su ita ce wannan matar data zo dazun ko?”
Na daga mata kai.
“Ni daman zuciyata ta daya ba zuwan banza take ba, Zahra na za mu cigaba da rufe maganar nan ba dole ne kowa ya san da wannan saboda a sama miki mafita”
Na rike hannunta da sauri ina girgiza mata kai.
“Aa Wallahi idan maganar nan ta fita wata matsalar zan sake shiga.”
“Miyasa kika aikata Zahra miyasa?”
“Ba ni da wata mafita, kuma ba zan iya kallon mijin ya mutu ba tare da na yi wani kokari na ceton ransa ba”
Na fashe da kuka mai karfi wanda ya saka muryata fita, har sai da ya rumgume ni, domin ita ma kanta tasan ina cikin mawuyacin hali a yanzu, rufe min baki ta yi tana kuka kamar yadda nake, Mama ta shigo da sauri tana kallona cike da tausayawa.
“Haba Zahra, wannan abun da kika ba zai dawo da Deen ba, kuma sai ki jawa kanki wani ciwon ai miye haka kamar na musulma ba? Haba Zahra? Dan Allah ki yi hakuri”
Ta karashe maganar cikin muryar kuka domin tuni hawaye suka wanke mata fuska. A ranar na ci kuka irin kukan na na rashin madafa irin kukan da babu mai cetonka kuma baka da wata mafita sai addu'a. Da yamma Mama ta dama min koko na sha domin shi na ji ina kwadayi sai ta aika makota aka siyo mata kamu ta dama min ta saka min suga da madara, na sha kumun sosai daman na dade ban sha kunu mai dadi irim yau ba, bayan na gama sha Yaya Maryam ta dauke kofin dana bata sannan ta aje min kwanon abinci.
“Ga wani nan ki kara”
“Ba zan iya ci ba”
Bata ce min komai ba ta bude abincin ta fara ci, sai da Mama ta tashi sannan ta matsa kusa da ni.
“Yanzu idan kika haihu sai ki yi yaya? Mama da Hajiya su ga ba ďa?”
“Likitam yace zai bani matacce wanda zan nuna a matsayin dan da na haifa babu rai, kuma yace daga yanzu kar na sake zuwa asibiti sai dai na kira shi idan ina jin wata matsala, kuma yace a gurinsa zan haihu”
Ta sauke ajiyar zuciya.
“Kin yi kuskure Zahra”
“Yaya Maryam dan Allah ki min alkawarin babu wanda zai ji maganar nan dan Allah, in ma zaki fada ki bari sai na mutu”
“Haba Zahra wannan karon wace irin magana ce, na miki alkawari babu wanda zai ji maganar nan har sai idan ke kika bukaci haka, amman dai ki yi tunani”
Na daga mata kai ina share hawayen ido, ni kaina ina jin kamar ba zan iya bada abun da zan haifa ba ga wata macen da ban sani ba, sai idan ban bada ba ina da wata mafitar ne? Ana daf da sallah magariba Yaya Maryam na zancen tafiya gida ni kuma ina kokarin tashi na yi alwala domin tuni Mama ta yi nata, Bahijja kuma tun da yamma tace zata je ta leka Family house dinsu gurin Hajiya ta duba jikinta. Sai muka ji sallama wata bakuwar murya ce kuma bakuwar fuska da ban wayance ta ba, ko ma na ce ban taba ganinta ba. Mama da Yaya Maryam suka amsa mata sai dai idonta a kaina yake kamar ta san ni sai murmushi take.
“Sannu ya hakuri”
Duk muka amsa mata har ni, sannan ta kalli Mama ta ce.
“Sunana Sadiya gidanmu na ta can baya, sai jiya Mama take fada min an yi rasuwa a nan har sun zo gaisuwa lokacin ina makaranta”
“Allah sarki, Allah ya saka da alheri”
Mama ta fada s zuciyata bata yarda da ita ba, na lura Yaya Maryam kallon rashin yarda take mata.
“Zo ki zauna”
Na fada domin na lura akwai magana a cikin cikinta, ashe kuwa abun da take nema kenan sai ta zauna, ni kuma na nufi butar da Mama ta aje na dauka na shiga bandakin tsakar gidan na yi fitsari ko da na fito na samu Mama ta shiga ciki Yaya Maryam kuma tana daga zaune bakin kofar dakin ta tsare budurwar da ido. Sanin Yaya Maryam ta san komai ya saka na kalleta na ce.
“Dan Allah Yaya Maryam dan ba mu waje”
Sai da ta sake kare mata kallon tun daga sama har kasa sannan tashi ta shiga cikin falon, na kalli yarinyar da sauri.
“Fada min waya turo ki?”
“Dr Hamid ne da Jamila suna son magana dake a waje”
“Su suka turo ki?”
Ta daga min kai.
“Ba zan iya fita na yi magana da su ba, saboda ina takama idan mutane suka gan ni a waje zai zama abun magana kuma ko ba takaba ina da tsohon ciki be kamata na fita waje na yi magana da wani a waje ba ina matar aure”
“Magana ce mai muhimmanci, da dai kin daure ba kowa zai san alakarki da su ba balle har a zargeki”
Ta fada min da sauri tana kallon kofar falon kamar mai tsoron kar wani ya fito.
“Tashi ki tafi zan fito”
Ta mike da sauri ta saka talkamin cikin sanda ta fice daga gidan, ni kuma na kira Yaya Maryam sai ta fito da sauri kamar daman jiran take na kirata.
“Wai Dr ne yana waje da matar za su yi magana da ni”
“Toh su shigo cikin gidan mana”
“Ba zai yiyu ba saboda Mama tana nan zata iya ji, kuma Bahijja zata iya dawowa ta tararda da mu”
“Gaskiya ba zan bari ki fita waje ba, na san me suka zo miki da shi”
“Ba zai wuce mu yi magana ba, kuma ba zan dade ba ni dai ki dauke min hankalin Mama please kar ta gane na fita”
Ba dan ranta ya so ta shiga falon ta dauko min hijab dinta.
“Zan kai buta bandaki idan kin dawo sai ki rataye Hijab din a waje ki shiga ki fito da butar”
“Toh Mama fa?”
“Zan tsayar da ita a falo ba zan bari ta fito ba sai kin dawo”
“Toh”
Na karbi Hijab din na saka da sauri sannan na saka talkamina na fice cikin sanda kamar yadda wacan bakuwar ta yi, kusa da kofar gidanmu na sami motar Dr Hamid. Yana ganina sai ya bude min gidan baya, ni kuma na girgiza mashi kai.
“Aa ba sai na shiga ba”
Sai ya bude motar ya fito, ita kuma ta sauke gilashin motar idonta sanye da katon tabarau irin wannan mai batar da kama.
“Ki shigo cikin mota zai fi sirri”
“Kuna son sirri kuka sako wannan matar a ciki”
“Bata san komai ba, kawai dai na fada mata yadda zata yi ne idan ta shiga gidan, kuma tana fitowa na sallame ta ta tafi”
Dr Hamid ya fada muryarsa kasa kasa.
“Me kuke kirana? Kuma ku daina yawan zuwa saboda mutane za su saka ido kuma mahaifiyata zata iya ganewa”
Na tambaya, sai ta bude motar ta fito, Dr Hamid ya kalleta sannan ya sake kallona ya ce.
“Dazun Jamila ta je min da wata magana cewar kin ce yarjejeniya ta fasu saboda mijinki ya mutu?”
Na kalleta sai dai ban ce komai ba.
“Ba a haka Zahra a ka'ida kudi ya riga ya fita daga hannun Jamila kuma an yi ma mijinki aiki kin ga da anyi nasara da yanzu yana nan raye rashin nasarar kuma ba zai canja komai ba saboda kudin an riga an yi amfani da su”
Nan ma shiru na yi hawaye suka fara cika min ido.
“Idan kuma kina son rike cikinki ne zaki ba mu naira miliyan ashirin, kuma ki sani ba ni kadai zan shiga a matsala ba idan ma kin fallasa har da ke sai kin shiga, saboda ke kika siyar a ra'ayin kanki ba cilasta ki aka yi ba, kin ga da ni da ke sai duk mu amsa tambayoyi yan jarida”
Jamila ta fada, a karo na uku da na kasa bude baki na furta komai sai ruwan hawaye nake.
“Ba haka ya kamata ki yi mata magana ba, ke da ita duka taimakon juna kuka yi, ita ta taimake ki ke kuma kin taimaketa, kuma magana ya kare na zo nan ne saboda na fahimtar da ita saboda na daga mata hankali ba”
Bayan Dr Hamid ya gama fadar hakan ya dauke idonsa daga barin kallon Jamila ya sake kallona.
“Sai abu na biyu kuma Mijin Jamila ya ce be yarda matarsa ta haihu a kasar nan ba sai a waje, saboda haka muka zo neman alfarma idan zaki iya bin mu waje ke ma ki haihu can”
Na girgiza kai da sauri.
“Ba mu wannan cikin yarjejeniya ba, ba zan bar garin nan zuwa ko'ina ba”
Sai ya daga min hannunsa.
“Shikenan babu dole daman roko kuka zo ba cilasta ki zamu yi ba”
“Amman Dr idan ba wannan ba bamu da wata mafita can ma din zai fi nan sirri kuma kasan yadda mijina yake ji da cikin nan ba zai taba yarda na haihu a nan ba”
Sai ya juya ya kalli Jamila wanda ta yi maganar.
“And we can't force her, idan bata ra'ayi babu dole, ke sai ki san yadda zaki yi janyo ra'ayin mijinki ya yarda ki haihu a nan”
“Ko kuma ka bata dama ta yi tunani ba, domin gaskiya na san Miji ba zai yarda ba”
“Kuma ba zamu cilasta ba, tun da har ta furta cewar ba zata je ba ki kyale ta kawai dan ba zan saka ta dole ba”
“Amman Dr... ”
Ta daga tana kokarin daga murya sai ya daga mata hannu.
“Ba sai kin daga mata muryar ba because she's pregnant women ba ayi ma mata masu ciki tsawa saboda ta yi yarjejeniya ba kanta ta siyar ba saboda haka tana da yancin ta yi abun da take so”
Wani kallo ta yi masa.