← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 127

Sashe 52

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ku kuma na tara ku a nan ne saboda na sanar muku cewa na saka auren Abiey nan da wata uku masu zuwa, idan iyayen yarinyar ba su shirya aurar da ita a yanzu ba, zamu nema mashi wata”

Kusan a rude Abiey yake Kallon Mai Martaba kamin ya juya ya kalli Anty baki a sake.

“Maa Shaa Allah ya kai mu ya sanya alheri”

Hajiya Kilishi ta fada cikin rashin jindadi rai domin ba wannan hukuncin suke son Mai Martaba ya yankewa Abiey ba, son so ya tsaurara fiye da haka, musamman nadin sarauta da Mai Martaba ya shirya yi masa. Kusan a tare Hajiya Kilishi da Mama Lami suka mike tsaye suna tafe suna yabawa da Allah kyauta gaba, Anty kuma na zaune kamar ďanta Abiey, sai da suka fice sannan Anty ta kalleshi ta ce

“Mai Martaba da dai ka duba dokokin nan ka saussauta wasu, Abiey yana son yarinyar nan sosai kuma abun da ya faru kuskure da dukanmu ba mu san waye ya aikata ba”

Mai Marataba ya daga mata hannu.

“Hukunci ne na riga da na zararta idan har akwai abun da yake son fada shi zai fada ba ke ba”

“Allah ya baka hakuri ya huci zuciyarka a gafarce ni”

Anty ta tashi jiki a sanyeye ta fice, tabbas ta jidadi da Mai Martaba be tsaurara ba kamar yadda suka so kuma nadin sarautar da zai masa yayi mata dadi, sai dai hukunci da ya yanke na shiga tsakanin Abiey da Zahra be mata dadi ba. After fitar Anty Abiey ya daga kanshi cikin nauyin kirji ya kalli Mai Martaba.

“Mai Martaba na gode da karamci da ka yi min, kuma da yardar Allah zan kiyaye wannan ma kuskure ne aka samu kuma ban aikata ba, sai dai na san ba lallai ne ka yarda da ni ba, amman ina rokon wata alfarma ka duba hukuncin da ka yanke na raba mi da Zahra, Wallahi Mai Martaba ina son Zahra irin son da uwa zata iya mutuwa idan aka raba ta da ďanta, saboda ita na dauki lokaci”

“Miye dalilinka na gabatar mana da wata ba ita ba?”

“Saboda a lokacin bata gama takaba ba, kuma bana son a bani wata amadadinta”

“So kake mu zama kananan mutane mu fasa wacan auren saboda kulla wani?”

“Mai Martaba ko kadan bana son Yasmin”

“To ka koyi sonta tun a yanzu, domin babu abun da za a canja ko da bana raye”

“Ka gafarce ni Mai Martaba Wallahi ban ba zan iya son wata ba bayan Zahra, ka taimaka min wajen bin umarni Mai Martaba na san ba zaka so ni fiye da sauran yayanka ba, a haka na ke rokon alfarmar ka tausaya min akan abun da nake so dan Allah kar na kasa bin umarninka”

“Bana saka doka a karya, bana bada umarni a musa ko a gurin jama'ar gari balle a cikin gidana, amman kai ka yi ka tabbatar ďan Uba biyu Umaima ta gurbata min zuri'a, har yanzu ina kyamar abun da Mahaifiyarka ta aikata da ya saka wani kaikayi a zuciyata, idan har ba zaka iya bin umarni na to sai ka bi zabi zuciyarka, amman fa ka sani zan cire hannayena a duk wani lamari da ya shafe ka”

Abiey ya runtse ido yana jin jiri na dibanshi daga zaunen da yake, gaba daya duniyar ta juye masa kasan ya dawo sama saman kuma ya koma kasa, dan haske da farincikin da yake hangowa a gurin Zahra ya fara sauya masa zuwa duhu, kofar ta kulle gaba daya wani kalar nauyi kanshi yayi zuciyarshi kuma na aiki raba jiki kamar jikin zai fasa fasa jijiyarshi ya fito.
[11/3, 11:29 PM] Oum_Nuwaira🥰: 3️⃣7️⃣

Meaning of POV 👉 point of view

HAJIYA JAMILA POV

Cikin kuka ta shigo dakin ta fada kan gadonta tana jin wani sabon kukan marar misaltuwa na tunkaro ta, ta san idan har wannan likitar tace zata zafafa bincike akan ciwon Amir asirinta zai iya tunowa, idan kuwa har asirinta ya tono, ta rasa Mr Bashir kenan kuma ta rasa duk wani abu da take mafarkin mallaka ta dalilin shi da ďan da take ikirarin na shi ne, kuma ta jefa ďan'uwanta cikin matsala. Har ta unkura ta tashi zaune sai ta ji ana murda kofar dakinta hakan yasa ta kara lafewa ta cigaba da rairai kukan. Mr Bashir ne ya shigo dakin ya karaso har kusa da gadon ya zauna ya kai hannunshi ya shafa bayanta a kokarin shi na dagota ya ce.

“Madam ki kwantar da hankalinki ba wani abu za'ayi ma Amir ba, ke ma kin san idan zai cutu ba zan ba kira wata likita ba, duk wani tunani da kike ko ganin kamar za su janyo mashi wata matsala ba haka ba ne, ita ma wannan kwarariyar likita ce ta san aikinta kawai ki yi fatan ya samu lafiya”

Ta kwantar da kanta jikinshi.

“Tsoro nake Hubby kar na rasa ďana ko kuma su ce min wata matsala ce da maganinta ba nan kusa ba”

“Babu abun da zai faru Ki kwantar da hankalinki duk yadda kike son yaron nan na fiki son shi”

“Shikenan Allah yasa sikar samun lafiyarshi kenan”

“Ameen haka nake son ji”

Ya sake shafa bayanta yana murmushi zuciyarshi cike da kaunarta da kuma tausayin yadda take son ďanshi.

“Bari na je na yi magana da ita”

Ta daga mishi kai kana ta bishi da kallo har ya fice, da sauri ta tashi ta nufi inda wayarta take aje ta dauka ta shige bandaki ta saka key duk kuwa da ta san da cewar abu ne mai wahala Mr Bashir ba zai dawo ďakin domin ya fi son zama a bangarenshi balle kuma yanzu da take kyautata zaton yana can tare da Dr Zainab.

ZAHRA POV.

A gidan makota da muka shiga wasu suka shigo suna mana jaje wasu kuma na shigo gulma domin na san abun da yake kawo su kenan. Sai da aka kira sallah azahar sannan muka koma gidan tare da taimakon jama'a muka kwashe kayan da za su kwasu Mama ta saka maza suka dauke mata gadonta da katifa suka kai mata makota. Na san abun da Baba yayi mashi be kyauta ba, kuma na jidadin da ya saka aka kama Baba duk kuwa da ban san kalar hukuncin da zai mashi ba, amman hakan zai koyar da shi darasi, domin ni ma ban jidadi ba, kuma iya hakuri Abiey yayi domin yana da karfin iko da dukiyar da zai iya daure Deen a wacan lokacin be yi ba, a yanzu kuma ace mahaifinshi yana kokarin cin mutuncin shi? Ina laifi yayi masa gargadin cikin mutunci ba ta hanyar tara jama'a ba, wata kila kuma Abiey ya zafafa domin ban san zafin zuciyar Abiey ya kai har ya saka a rushe gidan da shi ne rufin asirin mu ba, gashi a yanzu muna tsakiyar fili muna kwasar kaya mutane sai kallonmu suke makiya na mana dariya, na san ko ba a fada a gabana ba za a fada bayana cewar saboda ni aka yi kuma ni ce silar komai, hakan kuma ba zai min dadi ba kamar yadda rushen gidan be mana dadi ba dukanmu.

“Abiey mu ya wulakanta ba Malam ba, domin mu muke rabe a nan”

Mama ta fada tana kwashe spoons din ta dake cikin ginin bulo.

“Mama ina jin kamar ba Abiey ne ya aikata mana haka ba”

“To waya aika? Me muka tarewa wani balle a rushe mana muhallin ai shi ya kama Malam wannan aikin ma na shi ne”

Na yi shiru domin bana son musa mata kuma bani da hujja, sai dai na kasa yardar Abiey zai aikata haka, ko da yake hausawa na cewa wanda be fushi ba idan ya fusata be iya ba, idan har ta tabbata shi ya aikata be kyauta ba, domin laifin Baba be kai ya rusa mana gida ba. Abun da ba mu sani ba ashe labarin abun da ya faru ya kadare social media, a gidan da Mama take kai ajiyar kaya muka samu labari amayar gidan ta nuna min yadda aka watsa labarin a facebook mutane na ta yi mana fassara kala kala su kansu wadansu gidajen jaridun yanayin yadda suke buga labarin kamar suna cewar ni din karuwar Abiey ce, wasu kuma kamar suna kokarin taba martabar gidansu ne da na Mahaifinsa, a lokacin ne na tabbatar lallai abun da Abiey ya aikata babba ne domin kokarin bata mana suna yake daga ni har shi. Sosai da sosai na ji ina son magana da Abiey sai dai babu dama domin wayar Mama ta lalace daker ma muka ganta a cikin gini, gashi be zo ba kuma ba zai yiyu na je gidanba domin ban san halin da yake ciki ba, kuma ban san irin kallon da za'ayi min ba, kuma be zama lallai Mama ta bar ni na tafi ba.

A gidan muka yi sallah azahar sannan muka hau Napep zuwa gidan Kawun mahaifiyata wanda kaka ne a gurina, sai muka sha banban muna isa aka ce yanzu ya fita bayan ya fada musu cewar gurin mu zai je saboda ďanshi ya fada mishi abun da ya gani a media yana yawo, kuma ya kira wayar Mama be samu ba, shimfida matarshi ta yi mana muka zauna ita da surukarta suka kawo mana abinci kasancewar tana gida daya da suke da ita. A nan Mama ta labarta musu abun da ya faru ni dai ina zaune waje daya jiki ba kwari na kasa ganin laifi Abiey kuma ba ni da hujjar wanke shi, Matar Kawu ce ta kira Kawu ta fada masa cewar ni da Mama muna gida, sannan na saka number Yaya Maryam na yi mata flashing, after few seconds ta kira na labarta mata abun da ya faru bayan na fada mata cewar muna gidan Kawu.

Ana daf da sallar La'asar Yaya Maryam ta shigo gidan tare da fuskarta babu walwala kamar yadda ta mu take, ita kan bata bawa ko wane bangare gaskiya ba, ta nuna abun da Baba yayi be kyauta ba, haka ma abun da Abiey yayi be kyauta ba, musamman Abiey da take ganin kamar ya zafafa da yawa.

“Ni sai nake ganin kamar ba shi ya aikata ba”
Chapter 52 · 0% Book details