← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 127

Sashe 77

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya furta yana murmushi tare da wasu hawaye masu matukar zafi, ya saka hannunshi ya rufe idonshi ya cize bakinshi yaja wani kalar numfashi mai wahalar saukewa, daga Dr Zainab har mijinta sai da tausayin Mr Bashir ya kama su.

“Alhamdulillah da Allah ya nuna min haka da wuri, daman zuciyata bata natsu da Jamila ba, tun daga lokacin samun cikinta har zuwa haihuwar da ban so ta yi ta a nan ba bata yarda da kowa ba sai ďan'uwanta, Ummiter ma tana min complain amman na taka mata burki saboda na yardar da matata 100%, sai dai daga baya bayan nan na ga wasu abubuwa a camera tsaro na gidana, ta fada min cewar wata ce ta kawo Zahra sai ga shi na ga farkon shigowarta tare da Dr Hamid, sai dai ban yi tunanin matata zata iya cutar da ni ba duk wani abu na jindadin duniyar nan na mallaka mata shi na yarda na zauna da ita saboda ina tunanin ni da ita zamantakewarmu a tare jarabawa ce...”

Yana magana hawaye na sauko mashi.

“Wata kila ta yi haka ne saboda ta faranta maka rai, domin ita ma wanda ta siyar da ďan ta ta siyar ba dan bata son shi ba sai dai ta ceto rayuwar mijinta”

“Zahra...”

Ya tambaya hawayen dake sauka a idonshi sun ki tsayawa shi kuma be fasa sharewa ba, bakin cikin dake zuciyarshi ya kusa saka shu hadeye zuciya.

“Ita Dr Hamid ya nuna min komai na yarjejeniyar da suka yi....”

A tsanake Dr Zainab ta labarta mashi komai ciki har da bangaren da mijinta ya shigo ciki, sai yayi murmushi ya girgiza kai still hawaye na sauko mashu har lokaci be taba jin bakinciki rashin haihuwa irin yanzu ba, farinciki da ya ginu saboda ďan da yake tunanin na shi ne ya rushe a yanzu.

“Na gode Likita a yanzu ma ina son ki sake taimaka ki min wani jihadi”

“Kamar me ranka ya dade”

Wayarshi ya dauka ya hoton results din sannan ya mikawa Dr Zainab original din.

“Ki koma da results din nan, ki bawa Dr Hamid yayi abun da yake so ya baki wanda yake so sai ki kawo min, kuma ki dauki kudin da suka baki ni ma kuma zan miki wani tukicin mai tsoka”

“Amman hakan ba zai haifar da matsala ba?”

“Babu matsalar da zai haifa, sai dai ya taimaka min ke ma kuma ya taimake ki saboda rayuwarki zata zama kamar a cikin hadari idan baki aikata abun da suke bukata ba”

Ya amsa mishi da kai, hannunshi ya kai ya dauki wani tissue ya goge hancinshi.

“You can go ki kammala komai cikin lokaci, kuma ina son maganar nan ta tsaya iya tsakanina da ke”

Nan ma kan ta daga mashi, sannan suka tashi suka mishi sallama ita da mijinta suka fice, after fitarsu ya mike tsaye yana jin kamar zaman kujerar ba ya mashi dadi, zagayawa ya fara yi a cikin falon yana sauke ajiyar zuciya daker wani irin daci yake ji a cikin ranshi dacin da ya bayyana dannano har a halshen bakinshi, a takw ya ji kamar fever na neman kai shi kasa gurin windows din falon ya nufa ya zanye curtains din yana kallon waje. Tunanin matan da ya rabu da su yake saboda farinciki Matarshi, yar'uwarshi ma Imaan wanda yaya ce a gurin Ummiter ya bar gidanshi saboda Jamila, runtse ido yayi yana jin yadda duniya da abunda ke cikinta yake juya mashi a kai. A iya kar tunaninshi da hangenshi be hango wani good reason da zai saka Jamila ta yi mashi haka ba, duk da juriya irin nashi sai da ya zauna saman kujerar yayi ta kuka kamar wanda aka yi ma mutuwa.

“Allah ka ba ni komai kuma na gode maka da haka, Allah ka ba ni jarabawa guda biyu ta arziki wanda zaka tambaye ni a ina na samo kuma ta ya na kashe ta, sannan Allah ka yi jarabawa mafi girma ta rashin ďa ko ya, ya Allah ya dube ni da Rahma lallai kai mai yawan rahama ne mai jinkai, ya Allah ka saukar min da ijaba ya Allah, Ya Ubangijina karka karbi rayuwata har sai na ga sanyi idanuwana, ya Allah ka ba ďa ko ya ta ta tsabbaciyar hanya, idan kuma ba ni da wannan robon na samu haihuwa a duniya ya Allah ka saka min juriya da hakuri da dangana a zuciyata domin ka fini sanin abun da zai zama alheri a gareni kuma ka fini tausayin kaina tabbas kai gwani ne kuma kai fi kowa sanin abun da ya dace da ba yinshi”

Ya shafa addu'a tare da ruwan hawayen dake saukar mashi, can kuma ya girgiza kai.

“Rashin ďa bala'i ne tsarki ya tabbatar maka ya Allah”

Ya saka tafukan hannayenshi biyu ya rufe fuskarshi yana kuka irin kukan da bakinciki baya bari sautinshi ya fita.

*** *** ***

A mota suka yi ta tattauna maganar ita da mijinta kamin su isa gidan Ammy domin daukar yaransu, duk tsawon lokaci da suka dauka a gidan Mr Bashir Ammy na bandakin tana rutsar kuka abun da ta aikata ya dawo mata sabo fil tana ganin kamar ta aikata shi ne a gaban yayanta. Jin shiru yayi yawa ya saka Abiey ya hauro sama ya shigo dakin sai ya samu bata ciki sai dai ya ji motsin ruwa a bandaki, zuwa yayi ya tsaya bakin kofar bathroom yana ta jiran firowarta, shiru bata fito ba ga motsin ruwa yana ji hakan ya saka shi kiran sunanta.

“Ammy....”

Sai ta kasa amsa mashi tana kokarin tsayar da kukanta hawayen kuma suka ki bata hadin kai, tura kofar yayi ya shiga ciki a hankali tana jin motsin shigowarshi sai ta tara hannunta tana ta watsawa fuskarta ruwa babu kakkautawa, karasawa Abiey yayi kusa da ita ya rumgume mahaifiyarshi ta baya kukanta na taba zuciyarshi.

“Ammy are you still crying? Haba Ammy ke fa mahaifiyata ina kaunarki no matter what you did, no matter how bad you're daukar cikina kawai da kika yi zuwa haihuwata hakki ne balle kuma na girma a tare da ke na rayu da ke har yanzu i love you so much Ammy”

Hawaye ne suka zubo mashi har cikin kahon zuciyarshi yake jin kaunar mahaifiyarshi irin kaunar da yake da tabbacin Ammy bata da ta biyu a gurinshi ko da kuwa ace ta kashe kowa dake duniyar nan ta aikata duk wani abu da zai saka ta zama bad mother, da ace Ammy ta haife shi ta hanyar da bata aure ba hakan zai yi effecting dinshi ya saka shi damuwa amnan ba zai saka ya tsana ta ba ko ya juya mata baya because he know what MOTHER means. Ammy ta juyo ta rika fuskarshi tana kallonshi

“Allah ya maka albarka Aliyu ya baka yayan da za su maka biyayya kamar yadda kake yi min”

“Ameen Ammy”

Ya amsa da murmushi a fuskarsa, sannan ya saketa yana kokarin Juyowa suka juyo muryar Dr Zainab ta shigo dakin Ammy, kamin Abiey ya isa bakin kofar fita bathroom din Dr ta iso ganin kofar a bude ta tsaya tana kallonsu.

“Lafiya?”

Abiey ya juya ya kalli Ammy sannan ya sake juyawa ya kalli yar'uwarshi.

“Lafiya Kalau”

Shigowa ta yi katon bathroom din mai kama da wani karamin ďaki ta nufi Ammy da sauri hankalinta a matukar tashe.

“Wane irin lafiya kalau Ammy miya faru”

Abiey ya juyo yana kallonta.

“Dole ne sai kin san abun da ya faru tsakanin ďa da uwa?”

“Is not about ďa da uwa kuka fa Ammy ta yi kalli idonta”

“Akan maganar da na yi ne”

“Ba laifinka ba ne laifi na ne da na fada mata, miya saka ka wannan tunanin ma tun farko?”

Abiey ya dan tabe baki yana kokarin boye abun da yake nan.

“Saboda na ga Mai Martaba ya tsane ni da yawa ne, i thought ko haka ne ashe na yi kuskure”

“Amman Abiey zai ka zargi Ammy akan haka? Be kamata ka yi haka ba tun farko...”

“Komai ya wuce Allah ya muku albarka dukanku”

Ammy ta fada, sai Dr Zainab ta rumgume ta.

“Ameen ya bar mana ke Ammy”

Abiey yayi murmushi, sai da Ammy ta gyara sannan ta fito suka gaisa da mijin Dr Zainab, da za su tafi gida Dr da Abiey suka taka zuwa gurin gate suna tafiya tare tana labarta mashi abun da ya faru tsakaninta da Mr Bashir Mijinta kuma ya ja motar ya fita da ita waje ya jira tare da yara har sai da suka gama tattauna da dan'uwanta sannan ta shiga front seat yaja motar suka wuce.

ZAHRA POV.

“Zahra...”

Ina jin Sauban dake duke gabana yana leken fuskata yake kirana amman na kasa amsawa balle ma na dago.

“Subhanallahi Zahra kina cikin wata matsala ne ko kuma kiran da na yi miki ne ya kara saka ki cikin damuwa?”

Nan ma ban amsa mishi ba ban kuma san ranar amsa mishi ba. Jinginawa yayi da motar ya zauna kusa da ni sai na dago kadan na kalleshi tausayina na gani a cikin idanuwanshi.

“Zahra miya faru?”

Ina shisshikar kuka na bude baki sai na kasa cewa komai.

“You don't have to tell me idan kina ganin kamar be kamata na ji ba, amman bari na tambaye ki akwai wani abun da zan iya yi na taimaka miki?”

Na girgiza mashi kai alamar aa.

“Okay amman akwai abun da zan iya yi na tsayar da zubar hawayen nan na ki?”

Nan ma na girgiza mashi kai, sai ya mikar da kafafuwanshi ya zauna da kyau ya daga kanshi sama yana kallon taurari.

“Zahra wani lokaci kaddara tana zuwa ma bawa ba a yadda ya so ba, sai dai ta yadda Allah ya so, ban san miye damuwarki ba, ban san ta ina zan iya shiga rayuwarki na miki maganin matsalarki ba, amman zan roka miki Allah ya yaye miki damuwarki kuma yayi miki mafita ya tsaya miki a ko miye ke damunki and i promise you zan raya dare ina roka miki Allah ya yaye miki danuwarki”

Ni ma kaina na daga ina kallon samaniya.
Chapter 77 · 0% Book details