Sashe 92
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani irin numfashi yaja ya sauke yana jin zuciyarsa kamar zata rabu biyu, akan Zahra baya ji baya ganin duk wani abu dake gabansa, wani azababben kaunar Zahra ce ta motso masa har take kokarin neman ciwon da yake jin kamar ya matsa matsa kawana biyu wato ciwon zuciya... Da sauri ya bar gurin ya shiga falon Ammy cikin azabar ciwo ya haura sama ya shiga dakinshi ya nufi bandaki kai tsaye. Tarin jini yayi ya zubar tara hannunshi ya wanke bakinshi da fuskarsa, a hankali ya sulale ya zauna kasa yana maida numfashi, ko kadan baya son zama da Yasmin a matsayin mata sai dai baya iya karya alkawarin Zahra na cewar da tayi ya nuna mata son da yake mata na gaskiya ne ta hanyar auren Yasmin shi kuma yayi mata alkawarin tabbatar mata da hakan, ga wasan kwallon da Mai Martaba yake son raba shi da ita is one of his favorite, thirdly baya son sarauta ko kadan, but ya bar komai a zuciyarsa ya daurewa kansa ya yarda ya rasa na shi farinciki su samu na su cikar burin...
[11/22, 9:05 PM] Oum_Nuwaira🥰: 5️⃣8️⃣
Abiey ya dade zaune a bandakin sannan ya fito ya tsaya gaban madubi yana duban kanshi, idan ka kalleshi zaka yi zaton mutum ne mai kwanciyar hankali, musamman yadda natsuwa irin ta masu maida komai ba komai ba ta sauka a fuskarsa.
“Alhamdulillah”
Ya furta yana kara jaddada godiyarsa ga Allah, abun da ya dace ga musulmin kwarai mai hankali da aikata a lokacin da yake cikin kunci da kuma farinciki. Hannunshi ya saka aljihu ya ciro wayarsa ya dannawa Sauban kira, bayan Sauban ya karba kiran ya gyara tsayuwarsa gaban madubi yana kallon kansa cike da tarin tunani kala kala.
“Na kira ne kawai saboda na baka hakurin abun da ya faru I'm sorry”
“Ni ma na yi unkurin kira sai ka rigani, I'm sorry”
Sai duk suka fashe da dariya.
“Kana ina yanzu ina son magana da kai”
Abiey ya daga kanshi yana karewa dakin da ba bakonshi ba kallo.
“Ina gida ina dakina”
“Okay gani nan zuwa”
Aje wayar yayi ba tare da ya sake furta komai ba, ya zauna kan gadonsa idonsa na duba agogon dake hannunshi, kafin zuciyarsa ta ayyana masa karanta rubutun da yaki yardar ya bude tun bayan da ya karbi files din ya dauko pen ya saka hannu a duk inda ya kamata sannan ya maida takardun ya aje ya yana busar da iskar bakins. Ammy ce ta leko dakin ta tsaya daga bakin kofa tana kallon yanayin ďanta
“Aliyu”
Ya dago idonsa da kwalla ya tara har ya kwanta ya kalleta, cike da karfin hali irin na masu juriya ya sakar mata murmushi ya sauke kansa kasa, ba karamin tashi hankalinta yayi ba ganin danta a cikin damuwa ma wani babban abun tashin hankaline a gurinta balle kuma ace ta yi arba da kwalla a idonsa. Karaso ta yi kusa da shi ta zauna cikin murya irin ta masu rarrashi ta ce.
“Ina tunanin baka da wata abokiyar shawara ko wanda zaka fadawa damuwarka idan wata matsalar ta same ka a duniyar nan sama ni, fada min Aliyu me yake damunka?”
Babban dan yatsansa ya saka ya tare hawayen idonsa ya juyo yana murza idon.
“Abu ya fada min a ido yanzu”
“Idan akwai abun da na tsana a duniyar nan to ganin hawayenka ne Aliyu, ace yau na ga hawaye a idon ďana kuma na gagara sharesu, ka fada min danuwarka dan Allah”
Cikin wani irin rudu da rigici na uwar da ta damu da danuwar danta Ammy take tambayarsa muryarta na rawa kamar zata saka kuka. Yayi saurin juyowa ya kalleta tana murmushi
“Ammy ba komai i promise”
“Saboda Mai Martaba ko? Na san ya tsaurara zan kuma sake yi masa magana idan ma rabuwa zai yi da kai fine”
“Subhanallahi, shekara talatin kika yi Ammy kina jiran ranar da Mai Martaba zai kula da ni ya nuna damuwarsa a kaina, a yanzu Lokacin ya zo sai kuma ki nemi bata lamarin? Ke kika yawan fada min cewar na bi Mai Martaba ko dan saboda na samu aljanna, taya yanzu kike nuna min hanyar bijeri masa? Yardar Allah tana tare da yardar iyaye haka yardar iyaye tana tare da yardar Allah, ana bin umarnin Allah sama da na kowa kuma Allah shi yace abi iyaye, sannan ana bin umarnin Iyaye matukar be tsaba umarnin Allah ba, umarnin da Mai Martaba ya ba ni be tsabawa unarnin Allah ba, kuma ina tunanin haka ne saboda kara martabar gidansa da kuma tawa, abun da nake ganin ya fi kawai ki taya ni da addu'a Allah ya ba ni ikon jurewa da karfin halin bin umarninsa”
Hawaye ya cika idon Ammy har ya sauko masauki a kumatunta, babu komai a zuciyarta sai tausayin ďanta, tun tasowar Abiey be san wani abu farinciki mai daurewa ba, ya taso cikin bakinciki da wulakancin da Uba yake masa, after that ya samu Zahra daga bisani ya rasata ya shiga wata sabuwar damuwar, yanzu kuma ya sake samunta wani abun ya shiga tsakani ga Mai Martaba zai nada shi Sarauta abun da baya so, kuma ya hana shi wasan da yake, daman can Mai Martaba baya son ace jinin sarauta na abun da ya sabawa addini da al'ada.
“Da gaske zaka duk wannan Aliyu? Ni ma ba wai bana son aurenku da Zahra ba ne, matsalar da kuke yawan samu da kuma abubuwan da suke faruwa ne bana so, sannan sanadin ta ka san abun da na shekara da shekaru ina boyewa”
Hannayenta ya kama ya rike irin yadda yara suke idan suna bukatar abu cikin lafazi mai dadi da kokarin fahimtar da mahaifiyarsa ya soma wanke masoyiyarsa.
“Wallahi Ammy Zahra bata san da wannan maganar ba, duk abun da na fada miki na fada ne kawai saboda na samu labarin komai, amman Zahra bata fada min komai ba, dan Allah karki dora mata laifi kuma karki tsane ta akan haka”
“Ina fatar hakan”
Ta kai hannu ta share hawayen da suka zubar mata.
“Yanzu Zuwaira ta kira ni tana min maganar ya kamata a fara hada maka lefe na zancen aurenka da Yasmin”
Ji yayi wani abu ya daki kahon zuciyarsa kamar mashi, saurin dauke kai yayi ya sauke numfashi ba tare da ya bari Ammy ta fahimta ba.
“Okay ku hada duk abun da ya kamata Ammy, zan baki ATM dina”
Ya mike tsaye a kokarinsa na avoiding maganar.
“Tace Mai Martaba zai bada kudi, yace komai ake bukata ayi masa magana”
Murmushi ne ya subuce masa.
“Yasmin ta yi sa'a ta zo a daidai lokacin da zata ji dadi rayuwa, na rayu da Zahra ta so ni ba dan wani abu nawa ba, daga baya kuma ta rasa ni bata taba so na saboda wani abu da nake da shi ba”
“Yasmin ma bana tunanin tana sonka saboda wani abu naka Aliyu, yarinyar tana da tarbiya idonta be yi budewar da abubuwan duniya za su fara kawatuwa a zuciyarta ba balle har su yi tasiri”
“Amman Zahra tana son abun da zai kawo min kwanciyar hankali, ko kuwa tashin hankali ne ita a gurinta, any way Allah ya zaba mana abun da ya fi zama alheri ina tunanin Sauban yana waje yana jirana bari na same shi”
Kamin Ammy tace komai ya nufi kofar fita dakin ta bude ya fice. Sun samu awa daya a tsaye shi da Sauban yana labarta masa abubuwan da suka wakana tsakaninsa da Dr Zainab, halin da Zahra take ciki da kuma abun da yake tunanin shi ne mafita a garesu a yanzu. Sauban ya gyara jinginar da yayi mota yana kallon Abiey ya ce.
“Amman kana ganin wannan abun ya isa ya saka Zahra ta amince da aurena kai tsaye?”
“Tun farko zuwa ba zaka je mata ta siffar rarrashi ba ne, kai tsaye zaka tafi mata da barazanar hakan zai tsoratar da ita ta amince, sai dai bayan ka yi magana da ita ni da kai da Dr Zainab ina son zamu je mu samu mahaifiyarta mu yi magana da ita”
“Ina fatar hakan ya zama mafita, amman zata yi mamakin yadda aka yi na ji”
“Zata yi mamaki, sai dai zamu batar da mamakin nata, kuma mahaifiyarta zata taimaka mana ina tunanin, domin idan muka fito mata kai tsaye ba zata yardar ba, zata fara baka wasu sharudai akaina da kuma mutane kamar yadda ta baka da farko”
Sauban kallon shi kawai yake yana maganar har ya kai aya, sannan ya jingine maganar ya dauko wata.
“Abiey ina fatan hukuncin nan da Mai Martaba ya yanke maka be yi sauri ba”
Abiey dake faman maida numfashi ya ce
“Yayi Sauban, amman ina fatar samun sauki a gaba kuma ina fatar hakan ya zama silar warware abubuwa da dama, ina son na yi masa biyayya ne saboda Ammy da Zahra kuma ina son ni ma idan na sake bijiro masa da tawa bukatar ba zai ce min aa ba”
“Muna wannan addu'a, Allah ya yaye maka damuwa Abiey”
“Amin thank you”
Ya amsa da murmushi yana jin dadin yadda abokinsa ya zame masa kamar dan'uwa.
ZAHRA POV.
Bayan gama sallah azahar ina zaune ina nazarin gargadin da Mama ta yi min na cewar na kauce kuma na dauke ido akan mijin Hajiya Jamila tun da har ta fara nuna min bata tun kamin lamarin yayi nisa, sai dai na rasa yadda zan yi na kaucewa hakan domin duk wata hanyar da zan hango ina ganin kamar mafita sai na ga ba mafitar bace, domin Mr Bashir ba zai aiko yana kirana na ki zuwa ba, na zai tambaye wani abu na ki fada masa ba.
“Amman Mama kin san ba zan masa ba zan je ba idan ya kira ni, ni ban san ya zan yi ba”
Mama ta matsar da plate din abincin dake gabanta ta ce.
“Anya Mutumen nan be gane gaskiyar abun da ke tsakaninki da Jamila ba? Ina ganin kamar yana gwara kanku ne ke da ita”
Na bude baki irin na mamaki.