← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 127

Sashe 3

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya amsa sannan ya yanke wayar yana jin kamar ya fasa tafiyar, yana faka motarsa harabar masarautar Zahra ta fado masa a rai, ya kan irin wannan yanayin da kuma tunaninta a duk lokacin da take cikin wata matsala ko damuwa, wayarsa ya dauko kamar ya kira Sauban sai kuma wata zuciyar ta hana shi, a ganinsa hakan be dace ba why zai yi ta neman shiga rayuwarta? Bayan tana matar wani? Ya bude motar ya fito da kafa ya taka har bangaren Anty, yana kokarin ya kai hannunsa ya bude kofar falon Aisha ta bude ta fito tare da kawarta, cike da murna ta tarbe shi.

“Oyoyo Big bro daman ina ta nemanka, yau ma zan buga maka waya”

“Akwai wata matsala ne?”

“Eh Babba”

Ya kalli kawarta dake gaishe shi ya amsa sannan ya sake kallonta.

“Je ki dawo sai mu yi magana”

“Okay Ya shiyasa na ke sonka”

Ta fada cikin murna da jindadi, ya sakar mata murmushi kadan ya shiga cikin falon, kai tsaye ya nufi upstairs kasancewar babu kowa a falon sai Ac da plasma, Bedroom din Anty ya fara knocked sai da ta yi masa izinin shiga sannan ya tura ya shiga, idonta na yin arba da shi sai fuskarta ta cika da kyakkyawan murmushi.

“Maa Shaa Allah kamar ka san ina nemanka”

Ya zauna saman kujera yana kallon yadda ta canja tsarin furniture din.

“Aisha tace min akwai matsala? Miya faru?”

“Matsala ba yar karama ba, amman dai yanzu ka fara zuwa ka gaisa da Mai Martaba sai ka dawo mu yi magana”

“Daman bankwana na zo masa, gobe zan wuce Abuja daga can zan hau jirgin England”

“Hutu zaka je?”

“No akwai wasan da zamu buga ne, kuma daman ina bukatar barin kasar nan”

“Amman dai ba zaka dade ba ko?”

“Ban sani ba for now, wasan dai zai dauke mu for 3 days ban san adadin kwanakin da zan kara ba”

“Allah ya ba ku nasara ya sa ayi a sa'ah”

“Ameen”

Ya mike tsaye ya fice daga dakin, sai da ya leka dakin Narji duk da ya san ba lallai ne ace tana ciki ba a irin wannan lokacin saboda tana zuwa makaranta, ko bayan haka Narjin ba irin yan matan nan ne masu son zaman daki ba. Ta cikin kofar falon ya kunna kai zuwa bangaren Mai Martaba, samun kofar yayi a rufe, hakan na nufin Mai Martaba ya fita daga turakarsa kenan yana fada ko kuma falonsa da yake ganawa da baki, a dole ya juya ya dawo ta cikin falon Anty, ya fita ta kofar falon ya fita daga bangaren gaba daya ya shiga bangaren Mai Martaba, jerin motocin Mai Martaba ya tarar a harabar fadar ko ba a fada masa ba ya san Mai Martaba fita zai yi ko kuma ya dawo daga wani gurin. Yadda fadawa da dogarai suke mika masa gaisuwar suna zubewa kasa sai ka rantse da Allah shi ne dan sarki na fari ko kuma wanda ya fi kauna. Be shiga fadar ba saboda hangota ta yayi a rufe sai ya nufi masaukin bakin Mai Martaba.

“Idan kuma ya disgani a gaban mutane fa?”

Ya ayyana a ransa a tunaninsa zai tararda baki ne a falon, sai dai yana tura kofar falon ya shiga sai ya hango Mama Lami zaune a kujerar dake kusa da ta Mai Martaba sai wata matashiyar yarinya da zata tofi Aisha kadan tana zaune daga kasa sanye da abaya ash colar sai madaidacitar jakata a gabanta dayan hannunta rike da tabarau. Ba al'adarwa ba ce yin sallama idan ya shiga bangaren Mai Martaba saboda ya san Mai Martaba ba zai amsa masa ba, domin baya amsa sallamar kowa idan yana cikin mutane sai dai fadawansa su amsa, idan kuma daga shi sai iyalinsa ne ya kan amsa wani lokacin musamman idan zaman be wuce na mutun biyu zuwa uku ba, ko kuma matansa, sai da ko daga shi sai Mai Martaba ne a gurin Abiey yayi sallama Mai Martaba ba zai taba amsa masa ba saboda tsana.

“Wa'alaikassalam”

Mama Lami amsa masa sallamar da be yi kamar da gayya, kallonta kawai yayi ya risina har kasa da gaishe da mahaifinsa, be amsa masa ba sai ma dauke kai da yayi ya maida wani gefen kamar wanda yayi arba da makiyinsa, Abiey be damu ba daman inda sabo ya kamata ace ya saba da wannan yanayin.

“Daman na zo ne na yi maka bankwana za mu tafi England gobe da yardar Allah”

Nan ma Mai Martabarta be ce masa komai ba, sai Mama Lami ce ta amsa masa.

“Maa Shaa Allah, Allah ya tsare ya kaiku lafiya kuma ya bada nasara”

“Ameen”

Ya amsa da kamar dole.

“A tashi lafiya”

Na fada yana kokarin tashi sai Mama Lami ta ce

“Abiey baka gane wannan ba?”

Ya kalli matashiyar budurwar da Mama Lami ta nuna masa sai ta dago ta kalleshi da manyan idonta, baka ce wulik sai dai irin bakin nan mai kyau mai shining irin na yayan manyan masu kudi.

“Ban santa ba”

Ya amsa a takaice.

“Ummiter ce kanwar Engr ce”

Cewar Mama Lami.

“I thought ba Engr data muke da shi a Kano ba”

“Engr Bashir Alkali Auta daya ne dai a Kano”

Mama Lami na fadar haka sai matashiryar da aka kira da Ummiter ta gaishe shi.

“Good afternoon”

“How are you”

Ya amsa mata ba tare da ya jira ita ko Mama Lami sun sake magana ba, ya kalli Mai Martaba yana dan rankwafawa cikin girmamawa ya ce.

“Ammy ta ce a gaishe ka”

Sai a lokacin Mai Martaba ya daga masa hannu ya daga masa kai a lokaci daya alamar yana amsawa, Mama Lami ta dan sauke kai kasa Abiey kuma yayi murmushi kadan sannan ya ya juya ya fice. Mama Lami ta bishi da kallo kamin ta kalli Ummiter.

“Tashi ki tafi tun da kun gaisa, daman dai tace duk zuwan da take bata taba ganin Mai Martaba ba shiyasa yau ta zo ta kana nan na ce ta zo ta gaisheka”

Ya mike tsaye tare da jakarta ta yi ma Mai Martaba a tashi lafiya sannan ta fice. Wannan karon a karamin falo ya samu Anty zaune tana jiransa ita da Aisha, sai da ya karewa fuskokinsu kallo sannan ya zauna.

“Ka yi breakfast ma kuwa?”

Anty ta tambaya sai ya girgiza mata kai alamar aa, tun kamin tace komai Aisha ta tashi ta fito daga falon fa nufi dinning.

“Kun gaisa da shi?”

Ya daga mata kai, shi kansa haka yake wani lokacin idan jinin sarautar ya motsa sai dai yayi ta maka magana da kai sai ta kama dole zai bude baki yayi magana. Bayan ya sha farfesun kayan ciki ya ci soyayar plantain Aisha ta fara koro masa matsalarta.

“Kiri kiri matar nan ta hana Mai Martaba ya fitar da mu waje karatu Fisabilillahi adalci ne? Yanzu kuma na je na yi ma masa magana akan motar da yace zai siya mana yace na bashi lokaci zai nemi ni amman yanzu sai ta zo da wata magana a jiya wai kara dai ya bari sai idan zai aurar da mu ni da wadanda be bawa ba, kuma yayanta manya duk an ba su wadanda take cewa a bar mu sai zai aurar kanana ne fa, kuma idan aka yi haka ai ita riba biyu zata ci, saboda zata iya cewa a siyawa su Murshida idan za a musu aure bayan kuma yanzu ya siya musu”

“Shi ne kawai matsalarki?”

Ta daga mashi kai.

“Kuma ina son na yi Masters dina a waje”

“Sai kuma me?”

“Shikenan zan yi magana da PA sai kuje da shi ki zabi motar da kike so, kuma ki fada masa inda kike son yi da Masters din sai ya nema miki”

Amaimakon ta yi murna sai ta bata rai domin ba haka take so ba.

“Ai ko yanzu ta samu yadda take so, saboda kao ka biya min ba Mai Martaba ba, kuma motar ma kai ka siya min”

“Toh ya kike so yayi? So kike ke da shi Mai Martaba ya tsine muku? Kin san dai ba sauraren Abiey yake to miye na kawo karar Mai Martaba a gurinsa”

Anty Amarya ta fada tana kallon babbar yar tata.

“Haba Anty haka zamu yi ta zama ana nuna mana banbanci a gidan nan? Komai sai a ware mu dabam kamar ba haihuwarmu Mai Martaba yayi ba, tsakani da Allah na gaji ni wannan tsoron da kike nuna musu yana cutar da mu”

“Ammy ma da take magana idan Mai Martaba yayi abu ya sa ya canja ne daga abun da yayi niya?”

Abiey ya fada sai ta mike tsaye a fusace tana fadin.

“Ni dai ba kai nake son ka yi min ba, ina da gata kuma ni ma yarsa ban san banbancina da sauran yayansa ba da zai rika ware mu dabam”

Daga Anty har Abiey binta suka yi da kallo, Abiey ya dauke kai yana fadin.

“Allah sarki Aliyu bawan Allah”

Domin shi abun da Mai Martaba yake masa ya fi na kowa. Anty ta yi murmushi tana maida dubansa gurinsa.

“Sai kuma matsalar Narjis, Mama Lami ta yi mata miji ita kuma tace bata sonshi”

Abiey ya wara ido yana kallon Anty da mamaki.

“Ta mata miji kamar ya?”

“Dan gidan Justice Umar ne, shekaranjiya ta same ni da maganar amman tace bata fada ma Mai Martaba ba”

“Miyasa ba zata bawa yarta ko yar Hajiya Kilishi ba sai Narji?”

“Cewa ta yi wai shi ya ganta yace yana so”

“And sai ki fada musu bata son shi”

“Shi ne ba zan iya ba Abiey, kuma ka san idan Maganar ta kai gurin Mai Martaba zai iya cewa ya amince tun da komai suka ce shi ake yi, ita kuma ta zo ta nuna masa bata so wata matsala ta taso”

“No kin ga banbancin Ammy da ke, ke tsoronsu kike so ta halin yaya Ammy kuma bata sharkar kowa a cikinsu har Mai Martaba, akan me zaki amince ma from place yaron nan fa mashayi ne, kuma kamin Narji ai
Aisha ce babba why not ita ba a kawo mata shi ba sai Narji da suka raina?”
Chapter 3 · 0% Book details