Sashe 41
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri na dago daga jikin Yaya Maryam da nake kwance ina kallon kofar waje kasancewar labulen kofar ďakin a dage yake, zuciyata bata raya min kowa ba sai Abiey.
“Je ka ce waye”
Na fito na kalli Mama da sauri.
“Wata kila Abiey ne”
“Bari dai ya dawo mu ji”
Na share hawayena da sauri ina jin kamar kukana ya kare.
“Wai yace wani ne”
Yaron ya fada bayan ya dawo, sai na kalli Yaya Maryam wanda ta fito wajen na kuma sake kallon Mama na ce.
“Wata kila yana tsoron yace shi din ne na ki Fitowa, bari na je na duba Mama”
Ina cira kafa sai Yaya Maryam ta rike ni.
“Zahra be kamata kina fita any how ba, haihuwa fa kika yi, mutane ma ai sai su yi ta magana”
“Magana kawai zan yi da shi dan Allah ku bari na fita”
“Sake ta, ai yamma bata yi ba babu mutane safiya ce”
Tana saka ki na juya da sauri kamar baiwar da ta samu yancin, ina zura talkami na fice da saurina zuciyata na wani irin bugawa da karfi. Tsaye na yi cirus ina kallon Dr Hamid dake sanye da farar shadda tsaye daf da kofar gidanmu, a take na kunshe zumudi da nake na sauke kaina kasa daga barin kallonsa da nake na kusan dakiku goma na lumshe ido.
“Ba gaisuwa ba sallama kar dai fushin Jamila ya shafe ni”
Ya fada yana dan murmushi sai a lokaci na tuna da yadda muka rabu gaba daya na manta da lamarinta sai a yanzu, a sanyaye na gaishe shi ina bude idon.
“Barka da safiya”
“An tashi lafiya?”
“Alhamdulillah”
Ya leki fuskata
“Miya samu idon nan na ki?”
“Ciwo suke min”
“Kuka kika yi? You don't need to hide na san abun da Jamila ta yi bata kyauta ba, kuma na yi magana da ita on behalf of her ina mai baki hakuri ina neman yafiyarki”
“Babu komai dama ta samu ita ma ban ga laifinta ba, kasan hausawa sun ce idan ka samu rana ka shanya garinka”
“No bata kyauta ba tsakani da Allah, kuma ba a haka shiyasa ban kira ki na zo kai tsaye na san idan na kira ba lallai ki dauka ba, idan ma kin dauka be zama lallai ki fito ba”
“Komai ya wuce Dr Hamid ba zata sake ganina ba, ni ma kuma bana fatar na sake sakata a idona, it over”
Na furta cikin wani yanayi da nake jin kamar zuciyata ba zata iya yafe ďana ba.
“Ba fahimta ba...”
“Ba zan sake shayar da shi ba, ku nemi wani nonon ku bashi”
“Fushin ne haka?”
“Zahraty ban san mai halinki da daukar zafi ba”
“Da gaske na ke yi, i need to move on, akwai abubuwa sa yawa da ya kamata na canja a rayuwata, na yi sadaukarwa a muhallin da be dace na yi ba, ďana be yi min komai ba, amman uba ďana....”
Jikina ya fara rawa kamar ba zan iya tsayuwa ba ina kokarin dukawa a kasa sai Dr Hamid ya dafa kafaduna ya rike ni.
“Are you okay.?”
Na daga mashi kai ina kokarin daidaita natsuwata na hana kaina kukan da yake son kubuce min. Kamar ance dago kai ki gani ina kallon gurin motar da ban lura da ita ba sai yanzu kuma a zatona Dr Hamid ne ya zo da ita, kwasam na yi arba da Abiey a tsaye jikin motar yana kallonmu fuska ba yabo ba fallasa. Wani irin numfashi na ja na aje da karfi har sai da Dr Hamid ya juya ya kalli inda nake kallo, sannan ya juyo ya kalleni sai ya saki kafadata.
“Mutumen da ya hana ki shiga motana ne ko?”
Sarai na ji tambayar da yayi min sai dai hankalina baya gurinsa gaba daya imanina ya tafi gurin Abiey da shi ma kallona yake yi. Ya sake juyawa ya kalleshi sannan ya kalleni.
“Miye alakarki da mutunnan ne ni kam?”
Sai a lokacin na kalleshi.
“Labari ne mai tsawo da ba zai fadu a lokaci daya ba”
“Allah yasa be san abun da yake tsakaninmu ba, domin na yi mamakin ganinsa a gidan
“Be sanin abun da ke tsakaninmu ba yayi abun da yayi jiya ne saboda yana tunanin akwai soyayyar a tsakaninmu”
“I'm glad, bana son kowa ya san da maganar nan Zahra dan Allah ki rike mana amana, ki bari yayi ta tunanin soyayyar ce kawai kamin Allah ya yayi mana mafita”
Ya fada sannan ya kama hannuna na dama ya kai bakinsa ya sumbanta.
“Bari na barku wata kila akwai abun da zaku tattauna, zan kira ki”
Kasa ce masa komai na yi na bishi da wani irin kallo na mamaki da ya kamani. Be juyo ya kalleni ba sai da ya isa gurin motarshi da sai a lokacin na lura da ita, murmushi kawai yayi sakar min ya bude motar ya shiga sai ya bar gurin sannan na juyo da kallo gurin Abiey. Ga mamakina sai ya tako ya karaso inda nake tsaye bakin kofar gidanmu yana wani irin kamshi mai tayar da hankali da saka faduwar gaba.
“Hi”
Wani irin kallo nake masa kamar a yau na fara ganinsa, wani irin kallo ne da yake kara fito min da tsantsan kyansa da martabarsa a yau. Sai yayi murmushi ya saka hannayensa aljihu.
“Yaushe kika lalace har kika bar maza na taba ki any how?”
Na yi murmushi ina tuna lokacin da yake kai hannu zai taba ni sai na ce masa ni ba yar iska ba ce.
“Zahra you don't need to hurt yourself just to make me feel like an idiot, baki bukatar ki ari dabi'un da ba naki ba saboda kawai ki ba ni haushi”
Ya sauke numfashi sai na sake kallonshi hawaye na sauko min.
“Abiey...”
Be bari na fadi abun da zan fada ba ya tari numfashina.
“I know ina takura miki, i just come to talk you, Ammy ta fada min kin je har gida kin fada nata cewar akwai wanda kike so shi ne wannan?”
Sai na samu kaina da kasa furta komai, na karyata mahaifiyarsa ne? Na fada masa gaskiya cewar ita ta kira ni da kanta? Ko kuma na yi shiru.
“Wannan din ma ba son shi kike ba, kamar yadda kika kara tabbatar min da cewar ba son Deen kike ba, da kina son shi tsakani da Allah da baki isa kula wani ba bayan mutuwarsa da dan lokaci kadan, wannan din ma na san kina kula shi ne saboda na yarda da cewar kina son shi na kyale ki”
Ya jingina da ginin gidanmu sannan ya cigaba.
“Zahra Wallahi zan jurewa zuciyata matukar daina zuwa gurinki zai kawo miki farinciki, kuma idan har ta tabbata wannan mutumen kike so zan kyale shi da shi muddin zaki samu farinciki a zamanki da shi, amman hakan ba yana nufin na daina son ki ba har abada ba zan taba iya daina son ki ba, ko da ba zaki aure ni ba, ina fatar ki fahimci cewar ni Aliyu ban ci amanarki ba, ban san yadda zan miki ki fahimta ba amman tabbas ban ci amanarki ba Zahra kuma ban yaudare ki ba”
Na sauke kaina kasa ina murmushi hawaye na ta tsiyaya.
“Secondly kar haushi da kike je ya saka ki rika neman cin mutuncin iyayena ko cin fuskarsu, ba sai kin je kin samu Ammy da magana marar dadi ba akaina, kina shuka kiyayya ne a zuciyarsu, duk abun da zaki yi ki yi min ni kadai”
Zubewa na yi kasan guiwoyina na saka hannu biyu na dafa kafarsa na runtse ido.
“Abiey......”
Sai kuma na kasa furta komai sai kuka nake, matsawa yayi baya baya yana kallona, na mike tsaye na matsa kusa da shi na kama hannunsa na mari fuskata da shi zan sake marin a karo na biyu sai ya fisge hannun.
“Subhanallahi”
Ban tsaya komai ba na saka nawa hannun na mari kaina kamin na yi na biyu ya rike hannuna.
“Miye haka Zahra”
“Wallahi da zan iya Abiey da na cire hannunan na jefar domin da shi na aikata abun da a yanzu yake damuna, baka cancanci komai gurina ba sai girmamawa da mutuntawa”
Ya sake hannuna yana kallona, sai na sake durkusawa kasa na hade hannayena.
“I'm sorry”
Ya girgiza min kai ya matsa baya.
“Abiey i love you more than i did before, no one can take your place Abiey no one, babu abun da ya canja daga kaunar da nake maka babu daren da zuciyata baka begenka amman gadar da Deen ya gina mana ya saka na ke maka kallon mayaudari, you're here in my heart...”
Na taba saitin zuciyata, sai ya daga kansa sama da sauri ya dantse baki ya rufe ido kana ya jumke hannunsa, sai kuma ya bude idon ya kalleni hawaye dake makkale suka zubo masa ya juya ba tare da yace min komai ba ya nufi motarsa ya bude ya shiga ya bar ni gurin ina kuka.
[10/29, 10:48 AM] Oum_Nuwaira🥰: 3️⃣2️⃣
Ammy ta sauko a hankali tana kallon Abiey da ya hade kai da guiwa, da fargaba ta karaso inda yake zaune ta dafa shi.
“Aliyu...”
Dagowa yayi ya kalleta sai kuma ya mike tsaye da sauri ya rumgumeta, daman yana bukatar ya rumgume wani saboda farincikin da yake a ciki.
“Alhamdulillah Ammy tafiya mai nisa ta yanka min a yau”
Ammy ta dan yi dariya sannan ta kai hannunta ta shafa bayanshi.
“Alhamdulillah”
Ta furta duk da kasancewar bata san dalilin farinciki nasa ba, kuma ta yi ta ayyanawa a zuciyarta bata canka ba. Sakinta yayi ya kama hannayenta ya rike.
“Rabon da na ga ďana a cikin irin wannan farinciki har na manta”
Ya daga kansa sama wani wata kalar dariya kamar ba shi ba.
“Guess what Ammy”
Ammy ta yi shiru alamar tunani sannan ta girgiza masa kai.
“Ba ni da wannan basirar fada min kawai”
Zaunar da ita yayi sannan ya zauna gefenta.
“Ammy yau Zahra ta durkusa gabana tana neman yafiyata, ita da kanta take fada min cewar tana kauna a yanzu fiye da yadda take kauna ta a ada?”
“What do you mean?”
“Ammy ta gane gaskiya”
“Just like that”