← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 127

Sashe 66

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamin mu ce komai Hajiya Jamila ta fita daga gurin, jiki na rawa suka iso suka fara kama kayan suna sakawa ciki ni kuma Dr ya cilasta min shiga cikin gidan wai har sai sun gama, a tare muka jera da shi muna takawa har muka isa gurin na mika hannu na taba kofar shiga falon sai ya riga ni ya rike hannun kofar.

“Kamin ki shiga Zahra ina son ki yi hakuri da duk yadda zaki samu rayuwa a nan gaba ko kuma a yadda kika same ta a yanzu, lokuta da dama abun da muke so ba sai da mike samu ba, kuma kin ga yanayin jikinki dole be ki kawar da damuwa a ranki da duk wani abu da zai kawo miki bacin rai, karki yarda ki rika zama ke kadai ki rika samun wani abu da zai dauki miki hankali kuma ki daina bari idonki na ganin abin da zuciyarki bata so, hakan zai taimaki lafiyarki kuma zai taimaka miki sosai ta bangaren rayuwa da kuma mu'amala da mutane, and you have to be very careful da duk wani abu da zaki yi ba sai abun da ya shafi tsakaninki da Jamila ba, ko da tsakaninki da yan'uwanki ne saboda akwai security camera ko'ina a gidan nan, ki kula da shan maganinki akai akai”

“Inshallah na gode sosai Allah ya saka da alheri dawainiyar da kai da ni Allah ya biyaka”

“Wannan kuma Mijin Jamila zaki yi ma godiya shi ya dauki nauyin komai”

Na daga mishi kai sai ya bude min kofar.

“Ki fada mata na wuce”

“Ba zaka shiga ciki ba?”

“Mijinta yana ciki”

Kamar ya san zan tambaye shi ba ka ce yayi tafiya sai yace min

“Yayi tafiya amman ya dawo dazun da zamu shigo na kirata take sanar da ni”

Na daga mishi kai sannan na shiga cikin falon na alfarma yaja kofar ya rufe daga can waje, a karo na biyu bayan shigowar da na taba yi a gidan yau na sake daga kai ina kallon kyakkyawa falon da masu shi ba su san darajar naira ba.

“Sannu da jiki Zahra”

Kamar daga sama na ji muryar Mr Bashir da sauri na dawo da dubana gurin kujerun dake dama da ni sai ganinshi na yi zaune sanye da Jallabiya Ash color wani dan karamin teburi a gabanshi ya dora system dinshi a gaba. Da sauri na durkusa ina gaisheshi daga inda nake tsaye be amsa min ba sai yayi min alama da na zo da hannu, abun ka da talaka sai na tashi jiki na rawa na karasa inda yake zauna na duka kasa.

“Barka da yamma yallabai”

Ya dade yana kallona kamin ya amsa min da wata siga ba zan iya karantar halin da yake ciki ba, damuwa ko. akasin haka? Ba zan ce farinciki ba dai domin ban ga annashuwa ko nishadi a tare da shi ba.

“Yauwa ya jikinki?”

“Alhamdulillah, na gode sosai da dawainiyar da kai da ni Allah ya saka da alheri”

“Ameen, Dr yace zuciyarki ce ta buga haka ne?”

“Eh haka ne”

“Kina da wata damuwa ne?”

“A yanzu dai babu”

“Kamim yanzu fa?”

Na yi shiru kaina a kasa.

“I know be kamata na shiga cikin rayuwarki ba, but ya zama dole ko dan na san wacece uwar ďana....”

A firgice na dago na kalleshi gaba na mugun faduwa irin faduwar da na tabbatar idan aka auna jinina a lokacin za a ce ya kai 1000 dubu ba ma dari wani abu ba, yawun bakina suka tsarke ni a take na fara tari, wani kallo yake min kamar mai karantar abu a fuskata.

“Uwar ďan...ďan...ďan... ka kuma?”

Yayi murmushi ya dauki kofin dake kusa da shi ya kai bakinshi.

“Mai kula mai ďanka ai kamar mahaifiyarshi ce, be kamata ace na yanke miki hukunci kai tsaya ba ba tare da sanin wacece ke ba, gudun kar wani abu ya faru nan gaba mu koma da na sani, ya kamata mu san da wa muke zaune”

Ya karasa yana daga kai ya kalli Hajiya Jamila dake saukowa downstairs din da mamakinta.

“Hubby yaushe ka shigo falon?”

“Yanzu nan, ina yi ma Nanny ya jiki ne”

Na kalli Hajiya Jamila idona kamar za su yi magana ita ma kallona take cike da fargaba.

“Zahra yanzu kika shigo?”

Kai kawai na iya daga mata na mike tsaye sai na ji kafafuwa kamar ba za su dauke ni ba.

“Bari na je na duba su Mama ko sun gama”

“Ai da kin ce kin duba Amir yana ďakina”

Ko bata fada min ba na san ba zai wuce idan na shiga dakin tace min na bashi nono ba, fasa fitar na yi sai na nufi inda ta sauko zuciyata na raya min abubuwa da dama jikina na rawa kamar mai jin sanyi, any Mijin Jamila be gane gaskiya ba kuwa? Amman kuma idan ya gane ba zai saka mana ido mu yi ta wasa da hankalinshi ba. Daf da zan shige na juyo sai muka hada ido domin ni yake kallon irin duban da ba zan iya fassarawa ba, ita ma Hajiya Jamila kallona take tana rike da hannun mijinta.

ABIEY POV.

Ya aje spoon din hannunshi ya dauki ruwa ya sha sannan yaja kujerar baya ya mike tsaye.

“Aliyu”

Ya kalli Ammy

“Zauna”

Ya koma ya zauna, Dr kalli Ammy ta kalli kanenta.

“Dazun na duba jikin Zahra ta ji sauki sosai”

Ya daga mata hannu.

“Yasmin kuke son na aura kuma zan aureta, dan Allah ku daina min zancen Zahra ko wani abun da ya shafe ta”

Dr Zainab da Ammy suka hada.

“Aliyu ba mun hana ka auren Zahra ba ne saboda wani ra'ayi na karan kaina, sai dai tunanin haka shi ne mafita a gareku, bana son abun da zai bata tsakani ka da Mai Martaba, kai ka sani na fi kowa son farincikika kuma ina son abun da kake so wannan ya saka tun kamin ya furta cewar kana son Zahra na ke girmama ta ina kaunarta, ko a yanzu idan Mai Martaba ya yarda ka aureta ni ba ni da matsala”

“Mai Martaba ba zai yarda na aureta ba, saboda ina son ta kuma na san matanshi za su iya zuga shi su nuna mashi illarta, saboda haka ba ni da wani zabi da ya wuce auren wanda kuke so, da farko ni na cutu, yanzu kuma yar mutane za a cutar”

Ya mike tsaye ya fita daga dinning area din Ammy da Dr suka bishi da kallo.

“Ammy ni kan da zaki iya lallaba Mai Martaba da an bar Abiey ya auri Zahra saboda yana sonta sosai kuma ita ma tana sonshi”

“Na yi magana da shi amman be saurare ni ba, kuma ya tabbatar min idan har Aliyu zai bi zabin ranshi to shi kuma zai yafe shi, na san ďana mai biyayya ne ba zai iya musu mana ba shiyasa ya amince amman ni ma bana son aurenshi da Zahra yanzu”

“Saboda me?”

“Zai zama abun magana a cikin dangi kuma a duniya kasancewarshi sanannen mutum za ace ya auri bazawara a cikin dangin ubanshi ma zai zama abun magana shi kanshi Mai Martaba bana jin zai yarda ya barshi ya aureta”

“Da wannan dan wannan amman da zai yarda sai yayi ta biyu da ita”

Ammy ta yi shiru bata sake cewa komai ba, ta san ďanta yana son Zahra sai dai ita kuma a yanzu bata son aurenshi da ita ko dan sirrin da take kallon Zahra ta fallasa a gurin Abiey wanda tana da tabbacin da shi Abiey yake kallonta, kuma ba zai daina kallonta abun da ko da ta mutu, kawai dai ya kasa nuna mata komai ne saboda kunyarta da kuma irin tarbiyar da ta yi mashi ba zai iya nuna mata komai ba.

Harabar gidan ya fito ya saka hannayenshi aljihu yana kallon ma'aikatan gidan dake aikin yanke gyara fulawa zuciyarshi na raya mishi wani abu da yake fatan ba gaskiya ba ne, ringing din wayarshi ya katse mashi tunanin da yake sai ya ciro wayar ya kalli screen din.

“Sauban”

Ya furta sannan ya amsa kiran.

“Ina jinka”

“Na je na duba Zahra dazun”

Abiey yayi murmushi.

“Ka yardar kenan?”

“I can't say no to you as long as haka kake so zan yi”

“How is she?”

“Jikinta da sauki sosai amman dai tana cikin damuwa Abiey kuma yarinyar nan tana kaunarki you make the right decision, na same ta tare da likitan nan da ya hana ka shiga ranar yana gabanta a kasa ita kuma tana zaune saman gado tana kuka ban san abun da suke tattaunawa ba amman dai kuka take”

“Next time idan zaka je ka yi min recording so that i can trust you more, and ka bincika gida mai kyau ka siya mata idan kuma wannan take so sai a gyara mata, if kuma tana son wannan gidan da aka gina sai a bar mata shi”

“I will ask her”

“Thank You”

Ya mashi godiya sannan ya juyo ya maida wayar aljihunshi ya juyo gurin kofar falon ya murda ya bude ya shiga cikin falon, Dr Zainab na rike da jakarta tsaye tare da Ammy tsakar falon suna magana sai dai ganshi ya saka sun katse maganar suka juyo suna kallonshi, be ce musu komai ba y nufi wata doguwar cushion ya zauna ya maida hankalinshi gurin tv ke aiki, Dr Zainab ta nufi kofar fita falon Ammy ta yi mata rakiya. Ammy ta rufe kofar falon ta dawo cikin falon ta zauna kusa da Abiey tana kallonshi

“Aliyu”

Be amsa mata ba kuma be bari ta fada mishi abun da ke bakinta ba ya ce.

“Ammy zan tambaye ki tsakani da Allah this time daga bakinki nake son jin amsar nan”

Runtse ido ta yi ta bude ta sadda kanta kasa kamar mai kunyar hada ido da shi.
Chapter 66 · 0% Book details