Sashe 49
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
“Safiyar yau aka wayi gari da sabon labari cewar ka saka an rusa gidan wani magidanci sakamakon gargadin da yayi maka cewar baya son ganin ka kofar gidan, har wasu na cewa ka saka an sace mutumen ba a san inda yake ba a halin yanzu”
Abiey ya kalli mai mashi tambayar yana mamakin yadda yake kirkira marar karya kuma ya jefe shi da tambayarta.
“Da gaske ne kana neman yar gidan ko kuma rade rade ne?”
Mace ta tambaya a nan ma juyowa yayi ya kalleta.
“Gaba dayanku ba ku iya aikinku ba, ba kananan yan jarida ke hira da ni ba manya”
Yana gama fadar hakan ya juya ya bude kofar falon ya koma ciki, gurin da Telephone din falon take ya nufa na kira masu kula da gate din.
“Karka sake bari wani ya shigo cikin gidan nan da sunan aikin Jarida, idan na sake ganin yan jarida a gidan nan to a bakin aikinku”
Ya maida wayar a muhallinta sannan na nufi stairs da tunani kala kala da mamaki, mi zan saka yan jarida su yi mashi irin wannan tambayar idan babu rame mi ya kawo maganar rame? And waya gayyoto yan jarida a gurin ma abun da ya faru da dare? Yana tsaka da jerawa kanshi tambayoyi Ammy ta jefo mashi wata.
“Me ka aikata Aliyu?”
Ya tsaya daidai inda take tsaye a lokacin da ya jingina.
“Ammy ban yi wani abu ba, abun da na sani kawai mun samu matsala da mahaifin Deen a jiya”
“Mahaifin Deen? Miye hada ka da mahaifinshi?”
“Na je ina son zan yi magana da Zahra ne sai ya fito ya fara fada min magana yana cewa kar na sake zuwa gurin a gabana ma ya mari Zahra”
“Ni ban gane wannan maganar ba”
“Ammy kin san Mahaifin Deen shi ke auren mahaifiyarta maybe yana jin haushi ne, ni kuma da ya min haka sai na kira Ya Auwal na fada mishi abun da ya faru kuma na bukaci ya saka a kama mahaifin ayi masa duka, na tura mashi address din kuma ina tunanin ya aikata, but kamin na akwanta jiya na fada shi ya sa a sake shi”
“Yankin Kano ba hurumin shi ba ne, miyasa zaka saka shi ya aikata ta haka? Aliyu ina ta hango maka matsalolin da suke tattare da yarinya gashi tun yanzu abubuwa marasa dadi sun fara faruwa, ka san kuma mutane abu kadan suke jira su fara yadawa gashi muna zagaye da makiya ta ko'ina, abu kadan na samun ka dadi za a ji, jiya jiya da faruwar abu ace yau har yan jarida sun shigo gidan nan neman karin bayani? Idan wannan labarin ya samu Mai Martaba ya kake tunanin zai ji?”
“Ammy ki daina zafafa abu dan Allah, wannan abun har wata magana ce da zata je kunnen Mai Martaba? Idan ma ta je i can explain...”
Ammy ya sakar mashi ido irin kallon nan na mamakin yadda yake maida komai ba komai ba.
“Me ka fadawa yan jaridar?”
“Ban yi magana da su ba”
Ya amsa mata ya sannan ya fara takawa ya karashe hayewa Ammy kuma ta bishi da kallo har ya shige ďakinshi sannan ya sauko falo ta zauna ta dialing number babban ďanta,tana kwalawa Jummai dake kitchen tana wanke wanke kira
“Jummai”
“Na'am Hajiya”
Jummai ta fito da sauri tun kamin ta karaso Ammy ta ce.
“Fruits zaki yankawa Aliyu, maybe ba zai karya da ruwan zafi ba yau ki kai mashi ďakinshi kamin ya fito”
“Toh Hajiya”
Jummai ta amsa sannan ta juya da sauri ta koma kitchen din, Ammy kuma ta dauki remote ta rage volume din plasma tana amsa sallamar da Ya Auwal.
“Wa'alaikassalam”
“Ammy an tashi lafiya”
“Lafiya kalau ya iyali?”
“Alhamdulillah, har na ji kunya sosai Wallahi.ya kamata na kira aiki ne yake saka mu gaba”
“Wane irin aiki ne da zai saka ka manta da iyayenka, kai da ďan'uwanka halinku daya, shi da yake ba ya kasar sai dai mu gaisa da chat”
“Ammy Wallahi abubuwan ne ba daya ba, kuma kin san daman kusan karshe karshen shekarar nan aiki ya kan yi yawa, amman da zan mun samu natsuwa ina son zan dauki hutu na dawo gida na yi wata daya”
“Hmmn yanzu dai ba wannan ba, na kira ne akan maganar Aliyu yace ya saka ka kama wani”
“Eh yau da safe ma na ga sakon shi cewar a saki mutunen kuma na fada musu za su kai shi har gida”
“Me yace ayi mashi?”
“Kawai dai ya nuna min yana son ayi mashi horo ne kawai”
“Okay da mijina”
“Zai ji, akwai wata matsala ne Ammy”
“Aa Allah ya muku albarka ya shirya zuri'a”
“Ameen na gode Ammy Allah kara miki lafiya”
“Ameen”
Ta amsa sannan ta yi mashi sallma ta sauke wayar, ta dago tana kallon Abiey da ya sauko cikin shiga ta shadda kanshi da sauran ruwa, da alama wankan kawai yayi be tsaya shafa komai ba ya saka tufafinshi ya fito uzurce keys din mota a hannunsa dayan hannunshi kuma rike da waya.
“Ina zuwa?”
“Gidansu Zahra i need to see her”
“Breakfast fa?”
“Maybe sai na dawo”
“Na saka Jummai ta yanka maka Fruits”
“Ba zan iya cin komai a yanzu ba Ammy sai na dawo”
Ya amsa ta yana duba wayarshi dake ringing, be bata lokaci ba ya amsa kiran.
“Sauban”
“Abiey me yake faru?”
“Ban gane ba”
“How online zan turo maka wani labari da wasu gidan jaridu online suka buga”
Abiey ya kai zaune tare da sauke wayar gabanshi na mugun faduwa, data ya kunna tunani kala kala suna bijiro mashi, sai da sakwanin da aka turo mashi suka fara shigowa sannan na Sauban yayi appearing sama. Da kamar tsoro ya taba chat din ya bude sai idanuwanshi suka fara arba da wasu hotuna da jaridun online suka wallafa.
*Fitaccen Jarumin kwallon kwando Aliyu Abubakar Aliyu da aka fi sani da Abiey ya rusa gidan wani magidanci saboda ya hana shi magana da agolarshi*
“Abiey ya saka an rankadawa wani magidanci doka, kuma ya rusa gidanshi a dalilin wata yarinya dake zaune a gidan*
*Da gaske dan Sarkin Kano kuma fitaccen jarumin wasan kwallo kwando Abiey ya doki wani tsoho saboda budurwar da ake riko a gidan?*
*An rusa gidan wani magidanci saboda mace...*
*Fada tsakanin talaka da mai kudi, Abiey ya rusa gidan su talaka saboda ya hana shi mu'amala da yar da yake riko*
*Me yake faruwa da ďan Sarkin kano?*
Ko wane gidan jarida da kalar kanun labaranshi da suka buga labarin da shi, sun yi ado da katon hoton Abiey, wasu sun saka a inda yake sanye da kayan aikinsa wato na buga wasan kallonn kwando, wasu kuma manyan hotunanshi masu zafi dake trending a instagram suka dauka suka saka. Gidan jarida biyu ne suka saka hoton gidan da aka rusa, suka saka hotonshi a gefe. Abiey ya mike tsaye da sauri ya shiga kiran number Mama sai ta ji ta a kashe kamar dazun.
“What is happening here? Waya yayi wannan aikin? Why? Who do this?”
Ya fara safa da marwa a falon yana sake gwada number Mama, but still switch off. Jumma ta karaso inda yake tsaye ta janyo karamin tebur ta dora mishi plate din fruits.
“Gashi ranka ya dade”
Be kula ta ba balle ma plate din, sai kallon wayarshi yake da kiran Anty Amarya ke shigowa, kiranta na yankewa na Dr Zainab ya shigo nata ma na yankewa na Sauban ya sake shigowa, haka aka rika jero mashi kira har da old friends ďanshi da suka jima ba su kira shi ba, kuma ya kasa picking call ko daya, da sauri ya saka wayar aljihu ya nufi stairs din da kamar gudu ya shiga dakinshi ya bude gurin da yake ajiyar mask ya dauko baki ya saka ya bude gurin ajiyar glasses dinshi ya dauko kato wanda ke batar da fuskar mutum ya saka ya fito, kamin ya sauko downstairs Ammy ta kai tsaye waya a kunnenta dayan hannunta kuma dafe a kirji.
“Ina zaka je?”
“Someone is behide this Ammy, jiya jiya da faruwar abu amman har gidajen jaridu sun buga labaran karya, kuma ni ban saka a rusa gidansu ba, dole akwai hannun wani a cikin lamarin nan”
“Don't tell me rubbish...”
Ammy ta daka mishi tsawa, sai ya ja ya tsaya a gurin kamar hoto yana kallon yadda ran mahaifiyarshi ya bace, ta dayan bangaren kuma kiran Aisha na shigo wayarshi.
JAMILA POV.