Sashe 48
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama ta tambaya hankalinta a tashe. Baba Mani ya nufi ind dayar motar dake rushe gini take aje domin jin ba'asi, dayar motar kuma ta nufo inda muke tsaye gadan gadan kamar mu ma zata kwashe mu da gudu muka bar gurin ni da Mama, Mama ta nufi gurin su Baba Mani ni kuma na dawo gurin dayan dake kokarin rushe mana gini ina mashi hannu amman be kula ni ba, cikin bulon da suka rushe nana na gini na dauki wasu na fara jifar motar ta su da duk kalar duwatsun da na samu kamar wata mahaukaci haka na zama har sai da na kashe motar bayan ya riga ya rubar da ginar dakin Mama ya fito ya nufo inda nake tsaye.
“Ke baki da hankali ne?”
“Ba ni da hankali, Azzaluman banza me muka muku da zaku rusa mana gida?”
“Abiey ne ya saka mu yi mu umarni kawai muke cikawa”
“Abiey...!”
Mutumen ya fada min sai na maimaita sunan ina mamakin yadda Abiey zai saka a rushe gidan da muke kwana, bayan kuma ya san ba ni da inda zan raba da yafi min nan. Na nufi inda Mama da Baba Mani suke tsaye kamin na karasa Mama ta nufo ni sai muka hadu a tsakiyar gidan da zan iya kira da fili wannan karon hawaye shar nake gani a idon mahaifiyata har sautin kukanta yana fita, kukan da na dade ban gani ba, mutane sun zagaye mu sai kallo suke an rasa wanda zai saka baki yayi magana.
“Zahra sun ce Abiey ne ya saka su rusa gidan, ki kirashi ki ce yayi hakuri dan girman Allah, mu zai saka a matsala ba Malam ba, dubi mutanen da suka mana taro kowa so yake ya samu abun gulma kuma kowa mu zai dorawa laifi”
Sanyin saukar hawaye na ji a kumatuna, zuciyata na raya min kamar Abiey ba zai yi haka ba, sai na samu kaina da kasa cewa eh ko aa, domin ba ni da tabbacin shi din ne ko akasin haka, idan ma ba shi din ba ne to waye ne? Ai jiya shi ya aiko aka tafi da Baba kuma na yi magana da shi miyasa be hakura har sai ya turo an rusa mana gida? Duk cikin fushin ne?amman ban san Abiey da irin wannan zafin zuciyar ba.
“Kayan mu”
Mama ta fada tana kallon motar da mutumen da yayi min magana ya kunna ya nufi dakinta, ni da ita muka ruga a aguje domin kwashe wasu kayan kamin a rusa mana dakin, matan makota da a yanzu suka fara fitowa suka biyo bayanmu mazan da suke abokanin Baba kuma suka nufi motar domin sake yin magana da dayan mai rusa gidan, gurin da Mama take aje kudi ta fara lalabe sai dai yadda suka nufo mu da motar na tabbatar idan suka tararda mu taka mu zasu yi da motar domin ba da wasa suke aikinki ba. Hakan yasa na ja Mama muka bar kayan a nan mutanen da suka fara taya mu diban kayan su ma suka gudu, haka muka tsaya a gefe muna ji muna gani aka rusa ko wane bango na gidan saka mai da shi fili, wani bangare na ginin har ya sauka kan ginin makotanmu.
“To miye amfanin haka? Wannan ma ai ya zama zalumci taya zaka rusa gidan mutum bayan ka kama shi ka boye Allah kadai ya san abun da zai saka ayi masa, waya sani ma ko ya kashe shi”
Shi ne abun da Baba Mani yake fada kamin ya fara labartawa makotanmu abun da ya faru, daman jiya a gaban idon wasu komai ya faru.
“Mama bari na kira Abiey”
“Ki kirashi ki ce mashi me? Aikin gama ai ya gama, wayar ma ban san inda take ba”
Mama ta fada tana share hawaye, sai wata makociyar mu ta bukaci mu shiga gidanta mu zauna domin a inda muke tsaye fili ne ba gida ba.
[11/2, 12:20 AM] Oum_Nuwaira🥰: 3️⃣5️⃣
A lokacin da ya isa gidan be fada ma Ammy komai ba, sai dai be isa ya boye mata damuwarshi ba domin abun a bayyane yake a fuskarshi, tea da yake sha ma wani lokacin idan kwanta yau be sha ba yana shigowa ya shiga ďakinshi ya kwanta. Hakan kuma ba karamin mamaki ya bawa Ammy ba, domin ta san ďanta tsakanin jiya da shekaran jiya zuwa yau yana cikin farincikin da ya dade be samu ba. Sai da ya gaji da kwanciya ya shiga bandaki ya watsa ruwa ya fito ya yayi abun da ya zame masa wajibun wato saka turare sannan ya saka karamin wando ya kwanta ruf da ciki ya yi dora kanshi akan fili ya rutse ido, kamar an tsikare shi sai ya tashi zaune ya dauki wayarshi ya rike a hannun ya kama number Mama da Zahra take kiranshi da ita yana ta kallo kamar ya kira kuma yana ganin haka be dace ba, saboda abun da ya faru a yau. Ya busar da iskar bakinshi ya koma ya kwanta ya dora wayar a kirjinshi, kamin ya dago ta ya kira yayan shi, ringing biyu ta yi be daga ba, be kara mashi kira na uku ba ya aika mashi sako.
_Ya Auwal ka sa a saki mutunen nan kuma kar su illata shi please_
Yana gama tura sakon ya ja blanket ya lullube ba dan yana jin bachi ba, babu abun da ke yawo a kwakwalwarshi sai tunanin Zahra, he wanted to call her so badly amman yana shakar yin haka saboda Mahaifiyarta.
“I shouldn't”
Ya furta yana rufe ido kamar mai bachi.
“But mutumen nan ya wuce gona da iri ai, ďan shi yayi min yanzu kuma shi? No i can't tolerate it”
Ya sake fada still idonshi a rufe, Ammy ce ta turo kofar ďakin ta leko tana kallon ďanta, already ya ji motsin murda kofar dakin da Ammy ta yi ta bude, kuma jikinshi ya ba shi cewar ana kallonshi hakan ya saka ya dago har ya kalli kofar. Ammy na ganin haka sai ta karaso cikin ďakin ta zauna kusa da shi tana kallon kamshi.
“Aliyu ka samu matsala da Zahra ne?”
Ya tashi zaune yana kallonta.
“Ko da Mai Martaba?”
Nan ma be ce komai ba kamar mai tsoron fada mata.
“Ko kuma a bangaren kallon ne wane abu ya faru? Ko ka yi fada da wani ne?”
“Babu ko daya Ammy zan kwanta ina jin bachi”
Ya amsa mata a tunaninsa be dace ya fada mata haka a yanzu ba, domin kuwa baya son Ammy tana jin wani bad abu yana faruwa bangaren Zahra.
“Okay Good Night ka yi addu'a kamin ka kwanta”
“Okay”
Ya fada yana komawa ya kwanta Ammy ta bishi da kallon dake nuna cewar akwai abun da Abiey yake boye mata, ta dade zaune a ďakin har sai da ya fara runtse ido sannan ta tashi ta fice, tana fita ya bude idon ya kwanta rairai yana kallon ceiling, sai da yayi yakin gaske sannan bachi ya dauke shi be farka ba sai Asuba, sai da ya fara rage ace dakin sannan ya shiga bathroom yayi alwala ya fito ya gabatar da sallah Asuba a dakin, bayan ya gama ya dora da karatun Alkur'ane, sai da rana ta fito sannan ya rufe karatun ya maida kur'anen a muhalinsa ya bude windows rana ta hasko ďakin na shi sannan ya koma kan gadon ya kwanta ya mika hannunshi ya dauko wayarshi, ba tare da tunanin komai ba ya kira number Mama da zimmar zai gaisa da Zahra, ko kadan jin wayar a kashe be mashi dadi ba har ga Allah muryarta ya so ya fara ji, domin rabin mafarkinsa nata ne. Aje wayar yayi a gefe ya koma bachinsa na safe da yafi ko wane bachi yi mashi dadi.
Kamar mataccen haka ya rika sharar bachi mai nauyi ko motsawa baya son yi, daman dabonshi da bachi mai nauyi irin haka har ya manta. Daker Ammy ta tashe shi, shi ma sai da ta hada da girgiza shi.
“Aliyu”
“Na'am”
Ya amsa kana ya motsa ba tare da ta bude ido ba.
“Wannan wane irin bachi ne? Tun safe har 10 na safe”
“Ten ta yi”
“Har ta gota, ka tashi ka shirya kana da baki”
Ya bude idonshi da ya takure saboda bachi ya kalleta.
“Guest?”
“Yeah”
“Kuma ni suke son gani?”
“Eh yan jarida ne”
Tashi yayi zaune.
“Yan jarida? Me zai kawo su gurina?”
“Kana magana kamar baka san waye kai ba? Maybe suna son tatattaunawa da kai ne akan wani abu”
“Ba a tattauna sa ni haka nan Ammy har sai an rubuto min takardar da neman izini idan na amince na bada dama ake yi amman ba haka nan kai tsaye ba”
“Idan kuma wani abu ne da ya shafi aikinsu fa? Domin ba ďan jarida daya ba ne”
Abiey ya sauka saman gadon da sauri ya nufi gurin windo dake fuskantar harabar gidan ya leka sai dai be iya hango kowa ba.
“Da gaske Ammy?”
“Karya zan maka Aliyu? Tun jiya na lura baka cikin natsuwa idan akwai wata matsala ka fada min”
“Matsalar dake akwai bata kai yan jarida su ce za su yi hira da ni ba, waya ma ya ba su izinin shigowa?”
“Ni”
“Suna ina?”
“Kofar falo”
Bathroom ya nufa ya wanke bakinshi a gurguje ya fito ya be damu da canja jallabiyar dake jikinshi ba wanda yayi sallah da ita da asuba ba ya nufi kofa ya fice kamin ya sauko downstairs, Ammy ta tsaya tsakiyar stairs din tana kallon Abiey da ya nufi kofar fita falon. Hannu ya kai ya bude kofar falon ya fito waje yana kallon mutanen da sai a yau ya taba ganin fukokinsu su kusan shida biyar maza mace daya, ganinshi yasa suka mike tsaye suka karaso inda yake tsaye yana kallonsu da saurinsu two of them na dauke da camera yayinda biyun kuma suke rike da microphone one of them kuma tana rike da pen da abun rubutu.