← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 127

Sashe 101

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Deen dai be ce komai ya jefar da bulalar dokin ya fice daga gidan, ruwan zafi Mama ta dora akan wuta ta rikoni ta dawo da ni ďaki ta dauko ruwan tana gasa min jiki, ina kuka tana hawaye.

“Indai ba ki natsu kin yi hankali ba, wata rana sai yayi miki dukan da ya fi karfin jikinki ya kashe ki, kuma na a isa ayi komai ba, a yanzu ma idan na ce zan yi magana laifina za a gani, Allah ya saka miki”

Ina kuka da ihu Mama ta gasa min jikin, har sai da makota suka shigo Tambayar ba'asi, domin ko dazun da yayi min dukan nan na yi ta ihu balle kuma yanzu. Ni da Baba sai muka koma majinyata biyu a gidan shi yana jinyar dukan mahaukaci ni kuma ina jinyar dukan Deen. Wata kila yayi nadamar dukan da yayi min ne ko kuma daga baya tausayina ya kama shi idan zai shigo duba ni sai siyo min nama ko ice cream saboda ya san ni sarkin kwadayi.

Ranar da aka yi kwana na uku da faruwar lamarin na yi wanka na saka tufafin Yaya Maryam daman tun a lokacin da na sato su nake ta dauko sakawa ban samu dama ba sai yau, wani abu mai kama da hadin baki ban yi minti goma da saka tufafin ba sai gata ta sallamo a gidan ta saka salati tana son ta kai hannu ta dake ni har sai da Mama ta shiga tsakani.

“Mama wannan sabon tufafina ne fa, ban taba sakawa ba daman ina dubawa ban gani ba nasan ke kadai zaki iya saka hannu ki dauketa”

Mama ta kai min wani rankwashi mai zafi a kai.

“Ai wani lokacin duk abu da ake miki ke kike jawa kanki wahala, miye na sato maka kaya? Ba ce min kika yi ta ba ki ba?”

Na yi zuru zuru da ido irin na marasa gaskiya.

“Mama ki ce ta yi hakuri to”

Na roka ina zuboto baki gaba kamar na yi kuka, ranta ya bace sosai daman na saba yi mata haka sai dai na lura kamar wannan ya fi yi mata zafi, muna cikin gidan Deen ya shigo ya gaisa da su Mama ni dai ko gefen da yake ban kalla ba, haka kuma be hana shi aje min ledar hannunsa ba sannan ya juya gurin Baba yace.

“Motar tana waje Baba”

“To”

Baba ya amsa ni da Yaya Maryam da Mama muka yi masa kallon rashin fahimta jin cewar Deen ya bata masa zancen mota, sai a lokacin ya sanar da Mama cewar wai gidan Hajiya zai koma saboda ita ma ya bata hakkinta ba zai yiyu ya zauna a nan kadai yayi jinya ba.

“Amman kuma Malam ba zaka sanar da ni ba sai da zaka tafi Fisabilillahi?”

“To yanzu ba sanar da ke nake ba? Wai miyasa kika cika fitina ne Fisabilillahi? Wani lokacin ina duba kamar halinki ne Zahra ta dauko Wallahi, sam sam baki tausayina yanzu ina kwance a halin ciwo ai kamata yayi ki dauke min cefane da wasu lalurorin gida amman ina kullum sai kin karbi kudin cefane a hannuna, kuma kina dai kallo mahaukaciyar yar nan taki ta janyo min wannan lalura”

“Allah ya kiyaye ya baka lafiya, ni na yafe kwanan ka zauna a can har sai ka samu lafiya”

Cewar Mama sai Deen ya karbe.

“Baba Zahra tana da Hankali ba mahaukaciya ba ce, kawai dai bata jin magana ne”

“Haka dai kuke gani amman daga ganin idon wacan kasan ba na masu hankali ba ne”

Kasa kasa na watsa masa harara yadda ba zai gani ba, Deen ya rika shi tare da wani abokinsa suka fita da shi daga gidan. Yaya Maryam dai sai kallon ikon Allah take.

“Wai Mama yanzu jinyar ce ba zata yafe masa yayi a nan ba sai ya tafi gidanta?”

“Haka dai ya so, daman ba a komai yake iya kwatanta adalci ba sai idan ya shafi bangarenta, kina jin yana zancen na matsa masa da karbar kudin cefa ne, to waye zai ba mu idan ba shi ba? Ita cefanenta yake duk karshen wata ni kuma sai dai ya rika min guntu guntu a hannu, ka yi magana ace kishi kake saboda ita ya saba yi mata tun kamin na shigo”

“Kuma yana siyo mata nama be naki ba Mama”

Na kara mata da wani, a take ran Yaya Maryam ya bace.

“To Mama idan kina son abu ki rika karba cikin kudinki kina siya mana, sai ki zauna a haka ina son abu ke baki siya ba kuma shi ba zai siya miki ba?”

“Ai ina masa zancen kudin nan na san laifi zan yi, ni tun da ya karbi kudin sau biyu kawai ya ba ni ribar daga nan ban sake sanin yadda aka juya kudin ba, idan na tambaye shi sai yace kudin marayu ne kara a rika ajewa”

Sam ban san da zancen wasu kudi da Mama ta bawa Baba ba sai a lokacin, aiko na mike tsaye na rausayar da kaina, na nufi daki ban ce masu komai ba, ina jin suna da zancen ita da Yaya Maryam, ni kuma na bude jakata ta makaranta na dauko kullin ledar da na sato a dakin Deen ya bude ina dubawa domin sai yau Allah yayo hankalina ya kai na bude ledar, wani abu ne a ciki mai kamar ganyen ko ma dai na ce ganye sai kwayoyi magani farare fes kamar maganin ciwon kai sai dai ya dara maganin ciwon kai girma.
[11/27, 9:20 PM] Oum_Nuwaira🥰: 6️⃣3️⃣

Na fito da kullin maganin a waje na nunawa Mama a tunanina ko maganin mallaka ne.

“Mama kalli har da wani magani na samu a dakin Deen waya sani ma ko na mallaka ne”

Mama ta karba ta shinshina ta mikawa yaya Maryam sai na ji ta saka dariya.

“Zahra kin shiga uku dakinsa kika shiga kina masa bincike kuma?”

Mama ta yi mata alama da ta yi shiru duk a gabana sannan ta kalleni ta ce.

“Ba maganin mallaka ba ne, maganin da maza suke sha a tea ne”

“Oh shi ne Deen yake sha kenan?”

“Eh bar shi anan zan saka a wuta, karki sake shiga dakinsa kina masa bincike, ban dan lalacewa ba ma miye kaiki dakin namiji Zahra?”

“Nama fa naje dauka shi ne na hado da ledar, Mama ba ni zan kona”

“Aa barshi a nan idan na tashi zan kona”

Bata yarda ta ba ni, suka cigaba da hirarsu ita da Yaya Maryam har Yaya Maryam take bata shawarar ta karbi ragowar kudinta da suke hannun Baba ta fara wani sana'ar da shi, a lokacin da na lura hirar ta yi musu dadi hankalinsu ya dauka akan abun da suke tattaunawa sai na tashi na nufi daki na dauko jakata makaranta na yi musu sallama na kama hanyar zuwa makarantar sai dai ba makaranta na nufa kai tsaye ba, daman can na saba da shiririta abu mai wahala na tafi makarantar islamiya kai tsaye ba tare da na biya ta wani gurin ba. A gurin da na fi samun abun dadi na nufa kamin ina isa kofar gate din gidan motar Abiey na isowa kofar gidan ni da masu gadi har rigen bude masa kofar muke, bayan na shiga ciki sai na saki kofar na karasa gurin motar da ya fito yana murmushi tare da wani sarauyin da ba zai wuce sa'arsa ba, nuna ni saurayin da nake kyautata zaton abokinsa ne ya yi.

“Kar dai ita ce wanda kake ba ni labari”

“Ita ce fa”

Na dan matsa baya ina kallonsu domin ban fahimci abun da suke magana a kai ba.

“Amman ba ta yi kama da wadanda za su aikata wani abun shirme ko kiriniya ba”

“I'm telling you, Zahra mu shiga ciki ko”

Abiey ya karasa yana nuna kofar dakin, sai na yi murmushi na wuce gaba domin gidan ba bakona ba ne, suka biyo bayana ni na fara shiga falon na zauna sannan Abiey ya haura sama abokinsa kuma ya zauna akan kujera yana kallona sai na ji kunya ta kamani.

“Ammy amman baki fada min ba ba, ba zan dawo yanzu ba, ga Zahra ma ra zo, Okay”

Shi ne abun da Abiey ya sauko yana fada da waya a kunnensa kamin ya kalli abokinsa.

“Ammy ta fita kuma yunwa nake ji Wallahi”

“Ina mai aikinku”

“Ta yi tafiya, kuma ko tana nan kasan bana cin abincin masu aiki”

“Ai kai yunwarka ma mai sauki ce da ka sha tea zaka iya cewa ka koshi, amman ni idan ban ci abinci mai nauyi ba ba zan gane kan garin ba”

Abiey ya kalli.

“Zahra zaki girkawa Abokina Sauban indomie? Kin iya ai ko?”

Na yi kuri da ido kamar marar gaskiya, can kuma na daga kai.

“Eh na iya”

“Ga kitchen can”

Ya nuna min hanyar kitchen din, sai na aje jakar hannuna na mike tsaye na nufi kitchen, kusan a tare muka shiga ya dauko min abubuwan da zan yi amfani da su, sannan ya shiga dorawa kansa ruwan tea yana zolayata.

“Kyakkyawa ranar kika ja mana zuma kika gudu ko? Na balle ni a baya da kai sosai fa Ammy kuma kin taimaka mata har tana cewa ashe zata iya gudu idan wani abun ya taso”

Na yi dariyar da na tabbatar kara min kyau ta yi domin har wani wara ido yayi yana fadin.

“Wow Gaskiya Allah yayi hallita a gurin nan”

Na rufe fuskata da sauri ina dariya.

“Bari na baki damarki kar na rudaki, idan ruwan tea nawa ya tafasa sai ki kirani”

“Toh, amman karka dawo kitchen din sai idan na kira ka”

“Yes Ma'am”
Chapter 101 · 0% Book details