← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 127

Sashe 7

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ni ma ai cikin ne da ni be kamata kana bari raina yana baci ba”

“Yours is fake tana kuma na gaskiya ne”

Maganarshi ta tsoke ta irin sukan da ya bayyana a fuskarta, bata sake cewa komai ba ta bude motar ta shiga, sai ya juyo ya kalleni.

“Zahra ki kwantar da hankalinki a nan zaki haihu da yardar Allah, kuma ina kara tunatar da ke cewar daga yanzu awon cikinki har zuwa ki haihu ya dawo hannuna”

Na daga masa kai.

“Zan shiga ciki kar kanwar mijina ta same ni a nan”

“Okay”

Na juyo da saurina na dawo na nufo gida, sai da na fara lekawa na ga babu kowa aje sannan na shiga na cire Hijab din na rataye na shiga bandaki na sai na tararda butar da Yaya Maryam tace zata aje min. Jinginawa na yi gurin hawaye na sauko min na kai hannuna na dafe zuciyata dake min zafi.

‘Ba zan iya bada cikin nan ba, ba zan bada wannan cikin ba’

Na fada a raina ina sulalewa kasa na zauna ina kuka marar sauti, ban fito bandakin ba sai da na ji muryar Yaya Maryam tana fadin.

“Zahra har yanzu kina bandaki gashi har hudu ya sauko? Ba a son jimawa a bandaki fa”

Share hawayena na yi na fito daga bandakin rike da butar dake kokarin zamewa a hannuna ta fadi, har ta yi kamar zata nufo ni sai ga Mama ta fito a dole ta tsaya inda take ni kuma na nufi magudanar ruwa na duka na fara alwala ina ta kuka tun ina yi cikin karfin hali har ta kai bana iya boyewa sai da kuka ya fito, Mama ta rafka tagumi tana ta kallona a zatonta kukan rashin Deen kawai nake, sai dai ba kukan rashinsa kawai ba har na kuskuren dana aikata wanda yanzu ya dawo ya dame ni. Yaya Maryam ce ta zo ta rika ni na mike tsaye sai ta rumgume ni.

“Ki yi ta fadin Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”

Na daga mata kai, sai dai kuka baya bari na furta, ina rike da ita har muka shiga falona da babu komai saboda an siyar da kujerun gurin neman maganin Deen, uwar daka ta shiga da ni ta zauna saman sallayar da Mama ta gama sallah da ita.

“Me aka miki Zahra?”

“Yaya Maryam ba zan iya bada cikin nan ba, ina som abuna kuma matar da zan ban san wacece ita ba, idan na bata ya zama nata har abada kuma ban san wane hali zai kasance ba”

“Toh ya zaki yi Zahra? Kin riga kin aikata kuskure, ni da zaki dauki shawarata da sai ki fada kowa ya sani idan ma shari'a ta kama ayi sai ayi”

“Aa matsala zamu shiga idan aka yi haka”

“Yanzu me suka ce miki?”

Na fada mata komai, a take ta harzuka.

“Wallahi babu inda zasu je dake, waya san ma ko so suke su kasheki idan kin haihu saboda asirinsu yayi ta rufuwa babu wanda ya sani”

A take hankalina ya tashi, domin zuciyata bata raya min haka ba sai a yanzu da Yaya Maryam ta yi wannan maganar.

“Balle sun ga kin fara nuna musu cewar kina son danki”

“Yaya Maryam ko dai na gudu?”

“Ki je ina? So kike hankalin Mama ya tashi? Kuma ki shiga a bakin duniya? Zahra ki rika tunani idan zaki yi abu”

Na fara yawo da idona ina ta tunanin mafita.

“Na tafi ruga gurin su Hajjo, kin ga babu wanda zai san ina can ma”

“Zahra kina da hankali kuwa? Me zai kaiki can? Garin da ko nepa babu komai na jindadin rayuwa? Kuma tafiyar kwana uku? Idan ma kin tafi shi zai warware wannan matsalar ne? Zaki kara saka Mama da Hajiya a tashin hankali ne kawai”

Na sauke ajiyar zuciya, a zahiri na nunawa Yaya Maryam ba zan je ba, sai dai zuciyata bata daina raya min tafiyar ba.

“Guduwa ba ita ce mafita ba, dan Allah karki tafi”

Na daga mata kai.

“Ba zan je ba, amman dan Allah karki fadawa Mama komai ciki har da maganar nan da muka yi”

“Na miki alkawari ba zan fada ba, tashi kije ki yi sallah kar ayi Isha'i”

Na tashi kamar yadda ta bukata na shiga bandakin bedroom dina na yi alwala na fito da tunani kala kala, na yi ta rokon Allah a cikin sallah ta, tsakanin guduwa da kuma zamana, domin zuciyata ta fi natsuwada tafiyar, idan na gudu ai ba za su san inda nake ba, balle har su takura sai sun karbi babyn da zan haifa, amman kuma idan na tafi wa zai yanka min rago a can? Suma ai dole za su yi mamakin zuwana da tsohon ciki, mutanen karkarar mutane ne masu kara da girmama wata kila za su iya yanka min daya daga cikin dabobinsu idan ma ba su yanka min ba, sai na tafi da kudi na yanka nawa.
Sai da duhu ya soma yi sosai sannan Abban Husna ya zo ya tafi da Yaya Maryam, sai dai ba mu rufe gidan ba saboda tunanin Bahijja zata dawo, amman shiru hakan ya saka Mama ta kira waya ta tambaya ko lafiya sai aka ce mata lafiya kalau a can zata kwana, a daren daga ni sai Mama muka kwana a gidan, washe na farka da dan kuzarina na share dakina Mama ta dumamana mana shinkafar jiya kuma ta dama mana sauran kamun da aka siyo min jiya, Yaya Maryam kuma bata iso gidan ba sai 12 na rana tare da duka yaranta kasancewar yau weekend babu makaranta, kusan yanzu a nan take wuni kullum saboda ta rage min kewa da katuwar kular abincin suka zo, ta yi mana tuwo a gidanta miya kawai ta girka a gidan. Ana kiran sallah azahar muka ji tsayawar mota a kofar gidan, da farko na yi tunanin Dr Hamid ne mo Jamila suka sake zuwa, ba ni kadai ba yar Yaya Maryam dake zaune muna cin abinci a tare na lura hankalinta ya tashi da jin tsayawar motar musamman da muka ga an dauki lokaci ba a shigo cikin gidan ba, yara ta ma duk abinci suke ci balle na ce su leka waje domin su ga ko waye.

“Waye a waje? Na ji kamar mota ta tsaya kuma har horn an yi”

Mama na rufe baki wani namiji maji karfi ya shigo dauke da buhun Shimkafi na jefar a bakin kofar gidan mai binsa ma ya aje saman wanda wacan ya aje suka sake fita suka shigo da mai da kayan tea suka jera mana a gurin aiko yaran Yaya Maryam da gudu suka tashi suka fita ganin wanda ya aiko kayan da kuma inda suke dauko su, suna fita Dr Zainab ta shigo Ammy na bayanta sai wata bakuwar fuska da ban sani ba, Ammy na sanye da yadi da farin mayafi Dr Zainab kuma ta saka abaya kanta da hula ta rike dankwalin abayar a hannunta, bakuwar dake tare da ita kuma tana sanye da atamfa sai mayafi da ta rufe kanta zuwa bayanta da shi.

“Assalamu Alaikum”

Kusan a tare suka min hada baki gurin yin sallamar, sai na sauke kaina kasa na samu kaina da kasa amsa musu, Yaya Maryam da Mama suka amsa suna kallonsu, tun kamin ayi musu izinin zama Dr Zainab ta nufi wata kujerar zama ta mata ta dauko ma Ammy ta aje mata, Mama ta tashi ta shiga falo ta dauko tabarma ta shimfida musu Dr Zainab da Matar suka zauna a kai, har suka gama gaisawa da Mama da Yaya Maryam ban dago ba sai da Ammy ta kirani da sunan da ta saba kirana da shi.

“Zahra autata har yanzu fushi kike da Ammynki?”

“Ammy kina tunanin zan manta da abubuwan da suka faru ne?”

Na amsa mata ba tare da na kalleta ba, har yanzu ina tuna yadda ta tsaya kai da fata ta rantse danta ba zai aure ni ba. Dr Zainab ta ce

“Haba Zahra ashe ba zaki iya shafe abun da ya faru ba ki manta da komai”

Na kalleta.

“Da zan iya shafe wani abu, da na shafe tahirin saninku da na yi a rayuwata...”

“Ke Zahra... ”

Mama ta daka min tsawa sai na dube ta.

“Mama mutanen nan sun wulakanta, idan ku kun manta ni ban manta ba”

“Daman gaisuwa muka zo Allah ya jikansa ya bada hakuri ya sauke ki lafiya, Ammy tashi mu tafi”

Dr Zainab ta fada a fusace tana mikewa tsaye, ashe sanin da na yi mata na saurin fushi bata canja.

“Ayi hakuri Zahra rashin fahimta ne aka samu, kuma abubuwa sun biyo ta hanyar da ba mu yi zato ba”

Ammy ta fada sannan ta saka hanunta jaka ta ciro kudin da zai kai 50k ta aje kusa da Yaya Maryam.

“Zamu tafi Allah ya bada hakuri”

“Amin Allah ya bada lada”

Mama ta fada, sannan suka fice ba tare da na sake kallon inda suke ba.

“Zahra ba a haka gaisuwa suka zo be kamata ki nuna musu wani hali ba”

“Mama kamar kin manta mutanen nan? Allah kadai ya san dadin da za su ji da suka san Deen ya mutu ko ma waya fada musu ya mutu? Allah na gode maka da ya kasance ba sakina Deen yayi ba sai da mai rabawa ta raba balle ayi min dariya”

Na fada hawaye na sauko min.

“Ko kunya ba su ji ba”
Chapter 7 · 0% Book details