← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 127

Sashe 5

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Wai yanzu aka kira shi aka fada masa mutumen da ya zo yana neman details dinsa jiya ya rasu yau”

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”

Abiey ya furta da karfi yana dafe kanshi zuciyarshi ta buga da mugun karfi.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”

Ya sake furtawa be taba tsammani zai ji wani abu akan mutuwar Deen ba, can kuma ya dago ya sake duban Sauban.

“Da gaske ya rasu?”

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”

“Yes amman ai miye na mu a ciki mu? Kai da ya kamata ka yi murna?”

“Haba Sauban miye abun murna a mutuwar wani?”

“No Haba Abiey this is your turn fa da zaka gyara tsakaninka da Zahra, kasan daman ance mai hakuri mawadaci”

“Wane hali Zahra take ciki yanzu?”

Abiey ya tambaya yana tuna yadda zata shiga tashin hankali.

“Shi ne mai muhimmanci ba mutuwar Sauban ba”

“Ko dai miya aikata min dai ai musulmi ne, so ya kamata ka san abun da zai fito bakinka kai na fa musulmi ne”

“Toh Allah ya masa Rahama”

Ya fada ba dan yayi niya ba, Abiey be ce masa komai ba ya bude motarsa ya shiga, da tausayin Zahra ya iso gida ya san yadda take kuka babu kakkautawa idan wani abu ya same ta, balle kuma wannan sai a yanzu yake jin rashin jindadin bata taimakon da be yi ba akan lokaci. Labarin mutuwar Deen ne abun da ya fara labartawa Ammy, ita kanta ta kadu matuka da jin mutuwarsa, ta aje spoon din hannunta ciki yanayi ya tausayi ta ce

“Allah sarki Zahra zaki sake shiga cikin wani tashin hankalinka kuma”

Ya shafa kansa cikin damuwa ya ce.

“Ammy kina ganin akwai wata hanya da zan iya taimaka mata ne?”

“No kar ma ka soma, kana yin wani yunkuri za a ce ka jidadin mutuwarta, mu ma ba zamu je mata gaisuwa ba sai an kwana biyu”

“Amman zan bincika na ji idan tana cikin wata matsala maybe we could help”

Ammy ta dafa shi tana murmushi.

“No karkayi gaggawar aikata komai Aliyu, na sa kana son Zahra amman ka dan dakata na lokaci, yanzu ka shiga ka yi wanka ka shirya jirginku zai tashi 5pm ka sani kuma yanzu 4:37”

Ya daga mata kai cike da gamsuwa, sannan ya mike tsaye ya nufi upstairs. 5pm daidai ya isa Airport sai dai har biyar da kwata, suna cikin jirgin be tashi ba saboda passengers ba su gama shiga ba.
An kawata gurin kamar ba cikin jirgi ba, domin ga bakwaye sai yayi zaton wani kasaitaccen falo ne da ba shi da girma sosai, wasu passengers suna gaba gurin zaman mutane uku uku su kuma suna VIP, ya maida fuskarsa kusa da window, ya dora kafarsa daya saman daya gaba daya hankalinsa da tunaninsa yana gurin Zahra ne, me zai fara mata? Me ta fi bukata?

‘This time around i won't let you down Zahra i promise, zan kula da ke irin kulawar da baki taba mafarki ba, i will be right beside you, i will guide you ba zan taba bari hawayenki su zuba ba akaina i....’

Matashiyar budurwar dake tsaye tana sanyi da uniform din masu aikin jirgin ta katse masa alkawarin da yake dauka a zuciyarsa.

“Hi kamar Abiey”

Ya daga mata kai, sai ta sakar masa murmushi.

“Ka gane ni kuwa?”

Ya sake dubanta.

“Kamar mun hadu”

Ya amsa fuska ba yabo ba fallasa, sai ta sake yin murmushi.

“Ummiter”

Ta fada masa tana kokarin tuna masa sunanta kamar ance mata neman sani yake, be ce mata komai ba ya sake dauke kai zata sake wata maganar wata ma'aikaciyar da ba zata wuce sa'arta ba ta shigo gurin tana nemanta.

“Ummiter Ya Bashir yace idan mun sauka mu kira shi akwai kayan da Anty Jamila zata zaba sai a zo mata da su”

Ummiter ta yi murmushi.

“Okay”

“Will you guys excuse me please i have something important to think about”

Abiey ya fada yana kallonsu with serious face, yan matan masu kama da juna suka kalli sunan su sannan suka juya a tare suka fice.

*Littafin nan n kudi ne, biya ki karanta cikin aminci, pay 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 and send the evidence of payment to 08036126660*
[10/1, 5:16 PM] Oum_Nuwaira🥰: 1️⃣7️⃣

https://arewabooks.com/book?id=62d7b1c97fc1109aa61b7fca

MARUBUCIYAR LITTAFAN
1. ZAGON KASA
2. HAFSATU MANGA
3. ZAKI
4. FULANI
5. CIWON SO
6. BAKAR WASIKA

Duk zaku iya Samun waƴannan ne a Arewabooks, Ga link nan a sama👆🏻
Ayi following nawa da kuma comments.

*Littafin nan n kudi ne, biya ki karanta cikin aminci, pay 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 and send the evidence of payment to 08036126660*

ZAHRA POV.

Bayan Jamila ta fita na kwanta saman tabarma na dora hannuna daya saman cikina ina jin wani irin kaunar ďa ko yar da zan haifa, ban taba jin sonsa da kaunarsa irin na wannan karon ba, ashe ba zan iya cika alkawarin Deen na kula masa da abun da na haifa ba? Da kuma saka masa sunansa ko sunana idan mace ce, na sani da ace Deen ya san da cewar na siyar da cikin nan da sai yayi fushi da ni saboda yana so na balle kuma abun da zan haifa masa, not just Deen Hajiya da Mama ma ba za su yafe min ba, miyasa na aikata? Ka yafe min Deen ina kokarin ceto rayuwarka ne rayuwar da ba zata tsaya ba, kuma ban yi nadama ba aikata hakan ba saboda na yi saboda masoyina.

“Anty Zahra kuka kike?”

Maganar da Bahijja ta yi min ne ya saka na taba fuska sai na ji hawaye ya sauko ta gefen idona.

“Da Ya Deen ya san zaki yi kuka da yawa bayan mutuwarsa, da ya rokeki kar kika yi ko dan abun da yake cikinki, kuma kin sani Ya bayan son kukanki, ba kuma ke kadai kika yi rashi ba na fiki jin yadda kike ji”

Na kwalleta daga kwance dake yayinda take zaune bakin kofar falona, sai na tashi zaune.

“Ba ki fini jin komai ba Bahijja, ke dan'uwa kika rasa zaki iya aure mijinki ya maye miki gurbinsa, mace ko uba ta rasa aka ce idan ta yi aure ta tashi daga marainiya saboda mijinta ne zai rika kula da ita, ni kuwa mijin na rasa kacokan kin kuwa san zafin rashin abokin rayuwa Bahijja, miji ko kuntata maka yake wata rana sai ka yi marmarinsa balle kuma ni da Deen be min komai ba sai kyautatawa, ba zan taba samun miji irinsa ba, wannan kadai ya isa ya bani gwarin guiwar rike alkawarinsa na kin yi aure har karshen rayuwata”

Na karasa hawaye na sauko min biyu biyu, ni kadai na san yadda nake ji a zuciyata sai kuma mata irina da suka rasa na su mazanjen, na shafa cikina.

“Deen ya dade yana kwallafa rai a cikin nan, ashe Allah ya kaddara ba zai ga abun da zan haifa ba”

Bahijja ta hada kai da guiwa ta fashe da wani irin kuka mai taba zuciya, wanda ya saka Mama da Yaya Maryam fito da sauri sai dai ganin nima ina kuka sai fahimtarsu dalilin kukan na mu gaba daya.

“Haba Zahra mamaci fa addu'ah yake so ba kuka ba, na san zaki ji ba dadi kuma dole ki ji damuwa, amman idan kin ji haka ki rika furta Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”

Mama ta sai na maimaita hawaye na sauko min.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, Mama mutuwa tana da ciwo Mama ni kadai na san abun da nake ji, shikenan Deen ya tafi kenan?”

Mama kanta sai da na saka ta kuka ita da Yaya Maryam, Bahijja ma daker aka samu ta yi shiru balle kuma ni mai gayya mai aiki, tabbas mutuwa akwai da ciwo, mutuwa baki da tausayi, babu ruwanki da soyayya, idan na kalli fadin gidan nan ace babu Deen a ciki sai na ji zuciyata ta yi min wani iri, yadda muke mu'amala zamantakewarmu, rayuwarmu da yadda yake min idan ya shigo, idan zai fita ma, sai abun ya tsaya min a rai, minti daya biyu sai na sauke ajiyar zuciya nake iya samun numfashina ya daidaita. Da taimakon Yaya Maryam na koma bedroom dina na kwanta ina kokarin rufe ido na ji ta ce.

“Ina son magana dake Zahra”

Na kara bude idon da ban gama rufewa ba na kalleta.

“Miya faru?”

Ta nufi jakata data saka karkashin gado ta janyo ta bude tana ciro takardar yarjejeniya na tashi zaune babu shiri ina kallonta gabana na mugun faduwa.

“Miye wannan?”

Na kura mata ido na ma kasa kallon takardar data nufo ni da ita, tsabar tsoro da tashin hankalin ganin takardar da Yaya Maryam ta yi a lokaci na tabbatar da za a daka min tsawa zan iya faduwa na suma.

“Na yi ta karantawa na maimaita amman ban gane inda kan rubutun ya nufa ba duk da kasancewar da hausa aka rubuta shi”

“A ina kika gan shi?”

Na tambaya hawaye na sauko min.

“A cikin jakarki”

“Mama ta gani?”

“Bata gani ba, amman yanzu zata gani kuma ta ji komai”

“Fada mata kamar kin kara jefani a cikin matsala ne kawai, ni kuwa a yanzu mafita nake nema”

Sai ta matso kusa da ni.

“Kar dai da gaske kin aikata Zahra?”

Na sauke kai kasa ina hawaye.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, Zahra me yake damunki? A ina kika hadu da wadannan mutanen? Taya ma aka yi suka dora ki a wannan hanyar? Anya kina cikin hayyacinki kuwa? Kin kuwa san abun da ake nufi da ďa? Ko dan baki haihu kin ji abun da ake ji ba? Zahra ina ganin kamar kin yi hankali ashe har yanzu hauka da kurciya suna nan tare da ke?”

Na yi mata alama da ta yi shiru saboda ina gudun kar Mama ta ji.

“Kina tsoronta kika aikata abun da kika aikata?”

“Ba zaki fahimce ni ba Yaya Maryam, ba zaki fahimci yadda nake ji ba”

Na fashe da kuka marar sauti, sai ta matsa kusa da ni sosai ta zauna fuskarta cike da tausayina ta ce.

“Da gaske kin aikata Zahra?”

Na daga mata kai still ina kuka, sai ta dafe kai ta fara ambaton Allah.

“A lokacin idona a rufe yake ina neman mafitar yadda zan yi na samu mafitar kudin da za'ayi ma Deen aiki”
Chapter 5 · 0% Book details