Sashe 62
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Eh haka tace amman akwai maganin da na dorata a kai ne wanda muke fatar zai karbeta ko kuma ya karbi jaririn, sai dai mijin nata ne ba shi da hakuri kin san be taba haihuwa ba sai wannan karon shiyasa ya daga hankalinshi sosai akan lamari, rokon da nake son na yi miki shi ne ina son ki kara min time nan da kwana biyu mu ga yadda maganin zai karbe ta, sai dai bana son ki fada mashi ko kuma ki nuna mashi wani abu, saboda zai iya nuna rashin yarda ko kuma ya ga kamar bana son a kawo yaron gurin wani likitan ne”
Cikin Mamaki Dr Zainab ta ce.
“Daman kanwarka ce?”
“Eh uwarmu daya uba daya, ai tana fada min sunanki ta siffanta min ke sai na gane ki domin ita ma kanta tace ta fara ganin sauki amman mijin nata ne be yarda ba, ita kuma bata son abu ya zama biyu duk wani bincike da ya kamata mu yi mun yi amman yana ganin kamar dai ban yi abun da ya dace ba”
“Allah sarki shiyasa na ga ta fita ďakin tana kuka, ba matsala, zan daga kafa Inshallah kasan mai neman haihu kamar mutuwa tana neman rai ne ko'ina shiga yake”
“Haka ne ni ma ai ban ga laifinshi ba.... ”
Haka suka jera suna tafe suna hira har suka isa gurin da za su rabu kowa ya nufi gurin aikinshi.
ABIEY POV.
Yana tura kofar ďakin ya hangota kwance an saka mata oxygen an daura mata drip, babu kowa a dakin sai ita kayan da tukunyar oxygen da kuma machine din dake nuna yadda numfashinta ke tafiya, karasawa yayi kusa da ita ya tsaya kanta yana ta kallon fuskarta da wani irin tausayi, ya dade a haka sannan ya zauna yana kallon dayan hannunta dake karamin yatsanta ke sanye cikin wani karamin abu mai kamar zobe, ya sake kallon fuskarta dake ta haske dogon hancinta na kara fitar da kurciyarta da kyau da Allah yayi mata.
“Na fada miki Zahra ba zamu iya ba, ko mutuwa na yi ina da tabbacin za ki wahala kamin zuciyarki ta karbi wannan kaddarar balle kuma ace ina raye kin san da ina rayen kuma zan rayu da wata ba ke ba”
Yayi murmushi idonshi na cika da kwalla zuciyarshi cike da rauni.
“Ina kishinki yake? Taya zuciyarki zata iya daukar rashina a karo na biyu? A farkon ma ya kika kare balle a yanzu? Abubuwa da yawa sun lalace Zahra we can't fix it, wata kila da yanzu muna a matsayin mata da miji amman ji yadda kaddara ta yi da mu”
Ya shafa hancinsa iyakar kokarinsa yayi na hawayenshi zuba.
“Da farko Deen, yanzu kuma Ammy Mai Martaba, Step Fasher dinki, ban san abun da Allah zai mana nan gaba ba amman Zahra ni ma ina jin kamar rayuwata ba zata yi tsawon da zan dade ina rayuwa da wata macen da ba ke ba, rabuwar mu ta farko ta maida ni kamar mahauci kuma na kamu da ciwon zuciya a lokacin da kika sake dawowa rayuwata i thought na warke ashe ba haka ba, silar karuwar ciwon ne”
Yayi shiru ya sauke kanshi kasa hawayen da yake ta kokarin hana su zuba suka sauko mishi.
“Kowa da kaddararshi ni ban rasa uba amman na rasa gatanshi, ban rasa uwa ba amman na rasa farinciki”
Ya dago yana kallon pretty face dinta.
“Wasu mutanen za su yi mana kallon wawaye, miyasa za ki fadi ki suma saboda da ni ko su ce miyasa ni wani abun zai same ni saboda ke, amman soyayya wani abu ne mai asali tsakanin bawa da Ubangijin ma akwai soyayya balle kuma tsakanin dan'adam da ďan'adam, to ina kuma ga mace da namiji, first love wani ciwo ne da ba a taba warke shi har a bada no matter how bad it hurts, ba ki fi Yasmin da sauran matan duniyar nan kyau ko asali ba Zahra, Allah sai ya saka min son ki ke kadai Zahra ba dan kina autar mata ba, be bude min zuciya saboda na so wata macen bayan ke ba Zahra, kuma sai ya kawo wata katanga yayi mana tsakani da ke abubuwa marasa dadi suke ta faruwa Allah shi ya bar wa kansa shi sani wata ni da ke mu samu farinciki a gaba”
Ya mika hannunshi ta shafa gefen fuskarta.
“Idan kuma be hukunta na mukasance a nan a tare ba, Allah ka min kyautar wannan kyakkyawar halitar taka a aljanna a matsayin mata, Allah kai ka saka min kaunar Zahra kuma ka sani ina kaunarta ya Allah idan har ba zamu rayu tare a duniyar nan ba, ya Allah ka mantar da ita soyayyata ta yadda zata samu sukunin rayuwa da wani cikin aminci, Allah karka azabtar da ita da kaunata, ni kuma ka bar min kaunarta ta yadda zan samu salama ko da mai irin sunanta na ji”
Ya mike tsaye ya yana cigaba da kallon fuskarta, dayan hannunshi ya saka ya share hawayenshi.
“Mun fada kaunar juna a lokacin da ba mu san minene so ba, kuma ba mu san komai zai faru ba, so be dubi cewar ke har talaka ce ni ďan mai kudi ya hada mu, haka so yake be duba kalar fata ko asali, so na gaskiya babu ruwanshi da komai... Pretty i'm broken deep down Zahra kaunaki kullum karuwa take a zuciyata”
Yayi baya baya yana kallonta da murmushi a fuskarshi.
“Get well soon Babe, I love you”
Ya furta yana jin kamar kar ya tafi, ya dade tsaye bakin kofar yana kallonta sannan ya bude kofar ya fice ya zuba hannayenshi aljihu tashi zuciyar na mashi ciwo sosai kamar yadda ta saba, shi kanshi ya tabbatar ya fi Zahra juriya ne kawai ba dan haka ba shi da a yanzu yana kwance fiye da ita. Sauban na hangoshi ya yi ma motar key ya bude mashi front seat, Abiey ya shiga ya zauna yana kallon harabar asibitin kallo daya zaka mashi ka fahimci yana cikin damuwa.
“Ta samu sauki?”
Abiey ya kalleshi.
“Mai irin wannan ciwo baya taba warkewa Sauban you got lucky baka taba rasa masoyiya ba, matar da kake so take son ka ita ka aura, that's why you will never understand how painful it's”
Sauban ya juya motar suka fara tafiya.
“Wai daman can Zahra tana da ciwon zuciya?”
“Tana da ciwon so dai, irin wannan abun idan wata fargaba ko rashi suka same mutun shi yake sakawa zuciyarshi ta buga wani lokacin ma ana rashi shi gaba daya”
Abiey na fadar haka ya juyar da fuskarshi yana kallon titi da motoci kamar ba shi yayi maganar ba.
“Sauban ina son ka nemi auren Zahra”
Sauban ya kalleshi daman be gama mamakin furucinshi na dazun ba aka kira waya maganar su ta yanke.
“Wasa dai kake yi ko?”
Abiey ya kalleshi.
“Ka taba ganin na yi wasa akan wani lamari da ya shafi Zahra? I take everything about her serious”
“Taya zan nemi auren Zahra Abiey ya kake magana kamar baka cikin hankalinka”
“Na san abun da nake yi, wannan ce kadai mafitar da nake da ita da Zahra zata samu relief, and i believe zaka iya min abun da na bukata”
“No ba zan iya ba, idan ma wasa kake yi ka daina joke a part, taya zaka nemi auren yarinya ku rabu baka samu aurenta ba yanzu kuma ka ce na nemi aurenta? Na ji na nemi aurenta idan kuma na nemi aurenta ta amince fa?”
“Shi ne abun da nake so ai, amincewarta ko da bata amince ba ina son ka shiga ka fita har sai ta amince ta aureka”
Cikin tsananin mamaki Sauban yake kallon abokinshi.
“Abiey wai da gaske kake ne?”
“Yes and i mean it, ina jin ban taba rokon wani abu a gurinka ba, wannan ne karo na farko kuma karo na karshe matukar ba ka amince min ba”
“Abiey ka san fa na yi aure kuma ina son matata muna zaune lafiya, sai kawai na zo mata da maganar aure a yanzu? Duka duka yaushe ma aka yi auren to? So kake ka haifar min da fitina a zamantakewar mu?”
“Idan ka ga dama zaka iya haifar da kanka fitana, idan kaka dama ka barta ta sani idan kaga dama ka boye neman auren da yin auren gaba daya”
“Ai dole labari zai kai mata, kuma mutane ai sai su zarge ni”
“Ka aje zancen zargi a gafe, karka kalli nutane da kyali kyalin duniya idan zaka yi taimako, Sauban ba zaka ce min aa ba, kana ganin halin da yarinyar take ciki i care about her so much, i feel her pain i laugh when she's laugh, idan wani abu marar kyau ya sake samunta i won't forgive myself, Zahra tana so na amman ta zabi ta hakura da ni saboda farincikin iyayena, akwai soyayyar da ta wuce wannan ne ta aure mutumen da be dace ya zama mijinta da farko yanzu kuma ba mu san iya abun da zai faru ba, Zahra need someone to talk to, wani wanda zai fada nata cewar komai zai wuce zai zama tarihi, wanda zai kwantar mata da hankali ya saka ta samu natsuwa”
“Mutane za su kallon na ci amana Abiey kuma ita kanta Zahra ba zata aminta da ni ba”
“Kai zaka saka ta aminta da kai Sauban dole ne ka min wannan, for the sake of our friendship”
“Abiey yadda kake da kishi kake zaunar Zahra har zaka iya cewa na nemi aurenta?”
Abiey ya hade yawu a yanzu din ma da yake gabatar mashi da bukatarshi wani kishin ke fisgarshi.
“Dole ce ta saka”
“No ba zan iya ba”
Sauban ya amsa mashi a fusace, kallonshi Abiey yayi ya dauke kai.
“That's means you end our friendship....”