← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 127

Sashe 23

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ban san manufarsa a yanzu ba, ko da zan nemi taimako zan nema a gurin sa a yanzu? Bari na fada muku abun da na boye lokacin da Deen yake cikin ciwon nan sai da naje neman taimako gurin Abiey amman be taimaka min ba, sai ya nuna be ma san ni ba”

Ina rufe baki Mama ta fito daga dakin tana fadin.

“To ke miya kaiki a haka kuma kike zancen sake neman taimakonsa kwanakin baya? Har kike tunanin zai iya daukar miliyan ashiri ya baki?”

“Miliyan ashiri na me?”

Yaya Maryam ta tambaya, sai Mama ta fada mata tana kokarin zaunawa.

“Wai ta fanso ďanta, mutumen da ya so saka mu a kunya a ranar daurin aurenki kike tunani zai miki haka? Yanzu ma ban zan abun da yan'uwansa suke nufi ba ai Wallahi amanar Zahra sai ta fita a gurinsa”

“Wata kila kuma duk ba mu fahimci abun ba Mama”

Daga ni har Mama kallonta muka yi.

“Kamar ya?”

Mama ce ta tambaya ni kam kasa cewa komai na yi.

“Wani lokacin abubuwa suna zuwa ba ta yadda muka tsammani ba, kuma gaskiyar mutum ba zata iya fitar da shi ba sai da hujja”

“Ni fa ban gane wannan abun da kike kokarin fada ba?”

“Mama Abiey ya shigo har cikin gidana tare da mijina mun yi magana ta fahimta da shi, farkon abun da ya kawo shi a gurina na bincikar lafiyar Zahra ne da kuma bata taimako idan tana bukata, sai da ya fadada min abun ya kwance sirrin dake boye ya cire ni daga cikin hudun da nake ciki”

Na aje spoon din hannuna.

“Ya dai shimfida miki karya ya shirya yadda zai wanke kansa ya samu karbuwa a gurinki, saboda amana ta kama shi kuma yana son ya sake cutar da ni”

Mama ma dariya ta yi.

“Maryam kina da karamar kwakwalwa, maganar wuni daya ta saka kin manta da duk abun da ya faru?”

“Maganar wuni daya tana iya wanzar da zaman lafiyar da aka shekara dubu ba a samu ba, wuni daya na iya warware yakin da aka dade ana yi, kuma tun lokacin da abun nan ya faru ba mu ji bangaren Abiey ba, ba mu taba tsayawa mun saurara ba, sannan Mama akwai wasu abubuwan da ya kamata hankali ya fahimta”

“Da alama Abiey yayi miki biya mai kyau kudi ya baki ko ya miki alkawarin wani abu ne? Shiyasa har kika zauna kina tsara wannan maganar”

Sai ta kalleni tana murmushi.

“To ni waye sai siye saboda na wanke shi? Wanke shi a gurinki ba ina nufin ki so shi ba, kawai dai ina fadar abun da na fahimta wanda shi ne gaskiya”

“Kamar ya?”

Ta kalli Mama.

“Mama baki yi tunani ba lokacin da Ammy ta rantse da Allah Abiey ba zai auri Zahra ba? Kuma ta ce idan har ya aureta zata tsine masa albarka? Da ace bata son Zahra tun farko ba zata bari ayi baiko ayo lefe a biya sadaki ba”

“Ai sheri suka mata alhalin karya ne”

“Dr Zainab ce ta shirya haka saboda bata da wata mafita a lokacin sai wannan, amman abu ai ya kamata ace mai hankali yayi tunani ace duk soyayyar da Abiey yayi da Zahra sun rabu a ranar daurin aurensu? Kuma tun lokacin Abiey be yi aure ba dace yaudararta yake son yi da yanzu yayi aurensa shi ma har ya haihi ko ya kusa haihuwa, bayan kuma duk abun da ya faru yanzu ya dawo yana bibiyarta shi fa saurayi ne a yanzu ita kuma ta yi aure har ta haihu, idan ba kyau ba me ye Zahra take da shi da zai saka Abiey ya dawo yana neman sulhuntawa da ita har yana damuwa da damuwarta, yana da kudi iyayensa suna da kudi yayi suna da zai iya neman auren yar kowa ya a bashi, amman duk ba yi ba”

“Karya yake yi ya yaudare ni ne kuma amanata ta fara fita shiyasa yanzu ya dawo yana neman inda zai fake”

“Fada min Zahra kamin yanzu Abiey ya taba nemanki da iskanci?”

Na girgiza kai.

“Be taba ba ai be ga fuska ba”

“Shi na san akan ce idan namiji ya kwanta da mace ba zai aureta ba, ya yaudare amman ke ya rasa ranar da zai miki haka sai ranar da za a daura aurenku? Alhalin ba ki tana masa komai ba?”

“Daman Deen ya taba fada min ai yayan manyan mutane ba sa auren yayan talakawa, haka baya faru a zahiri sai a littafai ko a fina fina kuma na yarda tun da gashi anyi min”

“That's the point Deen ba shi ya lalata duk wata alaka a tsakaninku, ke kanki kin san son da Abiey yake miki ba na wasa ba ne kuma babu abun da zai saka yayi miki haka..”

Mikewa na yi tsaye na shuri da plate din danwaken da ta kawo min.

“Ban taba jin na tsaneki ba sai yau, Deen ya gama min komai Maryam tun da ya cire kunya a ranar da Abiey ya so saka ni, kuma ya rike ni amana har karshen rayuwarsa, Wallahi babu wani abu da zaki fada da zai saka na ga hasken Abiey ko da digo daya ne, babu wani abu da zaki yi ki saka na ga laifin Mijina sai dai na ke ki bata kanki a gurina, mijina yayi mutuwa kyakkyawa babu wanda zai bata masa suna”

Mama ta mike tsaye ta rike ni domin fuskata da hawayena sun nuna maganar da nake da gaske nake yinta.

“Maryam be kamata ki yi wannan maganar ba haba?”

“Wallahi Mama dan baki san gaskiya ba ne, daman zuciyata ta dade tana raya min abubuwa kawai dai ban ce komai ba, amman ki duba yadda lamarin nan ya faru kina gani kin san akwai lauje cikin nadi, sannan ki duba yadda Deen yake cewa ta masa alkawari bayan mutuwarsa ba zata auri wani ba, ciwon nan nasa ma fa son yayi ta dauka kawai dai ba a son ana fadar abubuwan marar kyau akan mamaci ma amman Wallahi Deen din nan ba mutumen kirki ba ne ni daman ban so aurensa da Zahra ba”

Ban san lokacin da na nuna da yatsa ba.

“Karya kike yi Maryam Deen mutunen kirki tun da be taba kashe kowa ba, kuma be sace abun kowa ba kuma ba zaman banza yake ba yana da sana'a, Deen ya gama miki komai a rayuwa tun da ya rufawa yar'uwarki asiri ya aureta a lokacin da wani banza ya so ya tona mata asirin, kuma daga yau sai yau karki sake furta wata kalmar akan mijina”

“Dole ne na fada miki gaskiya saboda ni yar'uwarki ce...”

“Na datse zumuncin dake tsakanina dake daga yau, indai saboda yan'uwantaka zaki fada min wata magana marar dadi akan mijina to daga yau karki sake kirgawa da ni a cikin yan'uwanki”

“Saboda wani banza zaki....”

“Mijina ba banza ba ne ban yafe miki ba Maryam”

Mama ta rike domin kokarin kai mata hannu nake duk kuwa da na san bana iya dukanta.

“Ya isa haka haba Maryam, ko Deen be auri Zahra ba be dace ki masa haka balle ya auri yar'uwarki”

Fashewa na yi da kuka sai Mama ta rika ni ta saka ni ďaki, Yaya Maryam kuma ta dauki jakarta ta fice tare da yayanta ko sallama bata mana ba, bana taba jin bacin irin na yau ba, ban tana jin na tsani Maryam irin yau ba, ashe a cikin yan'uwanka ma akwai makiyanka, ko kadan bana son na ji wata magana marar dadi akan Deen domin be rage ni da komai ba, kuma na san Abiey karya kawai yake masa. A yau na tabbatar da wani bacin rai yafi gaban kuka domin ina shiga dakin hawaye suka daina min zuba sai bugawa kirjina yake kamar ya fado, lallai a yau na kara tabbatar da Abiey ba mutumen kirki ba ne kamar yadda Deen ke fada min.

“Ka yi gaskiya baka raye amman yana maka kazafi saboda ya bata ka a gurin mutane, mugun halinsa na ta kara bayyana, na so ace kana raye Deen ka ga wannan ranar kunnuwanka su ji maka abun da makiyina yake fada bayan ranka, mutum mugun ce dan'adam butulu”

Na fada ina murmushin takaici.

“Yau da yar'uwata za a zauna a zagi mijina? Wannan bakinciki yayi min yawa da wannen zan ji? Rashin mijina ko na ďana ko kuma na abun da Maryam ta yi min a yau”

Na fada daman can ko lokacin da ina budurwa idan muka samu matsala da ita bana kiran da Yaya Maryam sai dai Maryam kai tsaye.

“Mama wai ki ji wannan abun? Allah ma ya isarwa Deen”

Mama dai bata ce min komai ba, ni ka dai na yi ta mitata har na yi na gama ban ji bakinta.

“Zahra kin ga mutumen nan yana ta kira amman bana son ki dauka”

Na fito da sauri daman tun dazun nake ji wayarta tana ringing sai dai ban maida hankali a gurin ba saboda raina a bace yake.

‘Wata kila fada zai yi yace miyasa na kira Jamila?’

Wata zuciyarta ta raya min sai dai hakan be hana ni picking ba.

“Hello”

“Zahra ya gida?”

Na ji muryarsa tsabanin yadda na yi zaton zan ji ta.

“Lafiya kalau”

“Am na yi magana da Jamila akan matsalar yaron nan muna son zaki matsa nononki mu gwada ba shi mu gani saboda mu na son mu gano inda matsalar take”

Na kai hannuna a kirjina ina jin wani irin sanyi marar misaltuwa, sai dai ban yanke hukunci kai tsaye ba.

“Zan yi shawara da Mama tukuna idan na yanke hukunci zaka ji ni”

Ina fadar hakan na yake wayar na zauna kusa da Mama da sauri ina fada mata.

“Amman ke zaki iya kina matsar nononki kina bashi?”

“Eh mana Mama tun da har akwai ruwan nonon mai zai hana na yi haka, kuma gwadawa za'ayi aga idan shi ma be saka shi ciwon Cikin ba”

“Ina tsoron kar asirinmu ya tonu Zahra? Saboda idan kina ba shi nono wata rana za a gane, kuma duk ranar da asirinki ya tonu zaki sha magana a gurin mutane Hajiya kuma ban san da wane idon saki kalleta ba”
Chapter 23 · 0% Book details