← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 127

Sashe 38

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Zaki iya zuwa ke kadai ko na raka ki?”

“Zan iya”

Na amsa muryarta na isar da damuwata.

“Lafiya kika yau?”

Ban amsa mata ba na juya na fice, ko da na fito Direban mai manyan shekaru yana tsaye kofar gidan yana jirana, sai na gaishe shi ya amsa min sannan ya wuce gaba na bi bayansa, kamin na isa gurin motar har ya bude min gidan baya, shiga kawai na yi na zauna ya rufe motar sannan ya shiga mazaunin direba yaja motar. Ina ta kallon titi da daidaikun mutane har muka isa kofar gidan sai da yayi horn sannan aka bude masa gate din ya ja motar zuwa cikin gidan har gaban Entrance din gidan ya faka motar ina ganin haka na bude na fita ban jira an yi min iso ba na doshi kofar daman gidan ba bakona ba ne. Door bell na fara dannan sannan na murda kofar sai na same ta a bude da alama an shiryawa zuwan nawa domin ban san Momy da barin kofar falo a bude ba da safe. Sai da na jefa kafata ciki sannan na yi sallama muryata kasa kasa, Jummai da Ammy dake tsaye gurin dinning suna magana suka juyo suna kallona, Jummai ta amsa min a yayinda na ga sauyin fuska a gurin Ammy domin a take murmushin da take ya gushe, hakan kuma ba karamin faduwar gaba ya saka ni ba.

“Bismillah Zauna....”

Daga can inda take tsaye ta min nuna da kujera, sai na karasa gurin kujerar na zauna maida kaina kasa, sai ta karaso kusa ta zauna a kujerar dake facing din wanda nake zaune sai da ta gama kallona sannan ta juya ta yi magana da mai aikinta.

“Jummai dan ba mu guri zamu yi magana”

“Toh Hajiya”

Ta amsa sannan ta nufo kofar fita falon ta bude ta fice ta rufo kofar.

“Kin san dalilin da ya saka na ce a dauko min ke?”

Na girgiza kai alamar aa ba tare da na kalleta ba.

“Gargadi nake son na yi miki, ke kin sani ba kyau kika fi sauran matan duniya ba, balle ki ce idan Aliyu ya rasa ki ya rasa kyakkyawa mace har abada, ba asali kika fi su, ba ku da arzikin da ďana zai rika bibiyarki akansa, so ne kawai da Allah ya dauka ya saka masa a zuciyata, kuma mun yi miki duk wani hallacin tun kamin abubuwa su lalace, ko da ace da gaske Aliyu ya fasa aurenki ya kamata yanzu da ya dawo neman yafiyarki ki yafe masa, amman jindadi ya saka ki daga hannunki ki mari ďana saboda ya nuna yana sonki? Zahra ke fa bazawara ce a yanzu ďana kuma Saurayi ne, Ciwon So ba Ciwon Hauka ba ne, kuma mai son ka baya ganin ramarka da ace kina son Aliyu kamar yadda yake son ki da yanzu ke kike rokon ya dawo ku yi soyayya da juna ko da kuwa ya yaudare ki, son nan da kika masa zai rufe miki ido ki kasa ganin laifinsa, amman Alhamdulillah ina yi ma Allah godiya da ya saka Aliyu be aureki ba, domin lokuta da yawa mutum yana son abun da ba alheri ba ne a gurinsa, na tabbatar ke da Aliyu babu alheri a zamanku shiyasa har Allah ya kawo abubuwan da suka faru aka fasa auren”

Na dago na kalleta ina jin wani ruwa mai kama da hawaye suna taruwa a fuskata.

“Na kira ki a nan ne saboda na shaida miki cewar Mai Martaba yayi ma Aliyu mata yarinya mai hankali mai tarbiya kuma yar gidan manyan mutane, ke kin fi kowa sanin takun sakar da suke da Mai Martaba yanzu kuma Allah ya kawo daidaito a tsakaninsu, dan Allah dan darajar mahaifinki karki zama silar da zata rusa auren Aliyu da Yasmin domin suna son junansu, jarabawar son da Allah ya dorawa Aliyu kuma muna nan muna addu'a muna nan dake zai warke kamar be taba yi ba, ki kwantar da hankali daga yau inda Aliyu ďana ne ni na yi cikinsa na haife shi na shayar da shi na raine Shi har ya girma kuma zan fada masa magana ya ji, to ba zai sake bibiyarki ba balle har ki jidadin wulakanta shi, Zahra ko ke kadai kika rage mace a duniyar nan to mun yafe ki Aliyu zai mutu be yi aure ba”

Gyaran zamanta ta yi sannan ta kalleni.

“Saboda ke Aliyu ya dauki tsawon lokaci yana fada da yar'uwarsa, wata kila za a iya fada da yar'uwa a kwashe lafiya, amman ba za ayi da uwa a kwashe lafiya ba, haka ma ba za ayi da mahaifi a kwashe lafiya ba, saboda haka ina son ki tsaya da Aliyu irin tsayin da zai san da gaske kika, kuma ki yi masa kalamin da zai fahimci gaskiyarki, Zahra bana son wata alaka ta sake shiga tsakaninki da ďana, bana son na sake jin sunanki a bakin Aliyu! Sabanin haka zai janyo matsala ni a tsakanin Aliyu da mahaifinsa haka ma da sauran yan'uwansa da kuma ni da ma haife shi, mun riga mun san baki son Aliyu, to ina mai tabbatar miki Aliyu ba zai sake wahala akanki ba har abada...!”

Da wani irin karfi na hade yawun bakina, hawaye kam ban san adadin wadanda suka min zuba ba, tun suna zuba da sanyi a ciki har suka koma zuba da zafi kamar za su kona min fatar fuska.

“Zaki iya tafiya....”

Ta nuna min kofa, sai na mike tsaye ina jin kamar na fadi nufi kofar ina takawa a hankali jiri na daukata, zuciyata ta cika fam kamar zata fashe kaina kuma ina jin kamar babu komai a cikinsa. Ban san na iso gate din ba har sai da na ji daya daga cikin masu gadin wanda ya sani yana salati sakamakon buguwa da kaina yayi da gate din.

“Subhanallahi Zahra lafiya”

Ya kalli saitin inda kofar take sai dai hawayen dake min zuba ba su bar ni na ga kofar da kyau ba, sai na kai hannu na lalaba na fita tafiya kadan na yi na samu guri na zauna ina jin kamar ban taba shiga tashin hankali irin wannan ba, miyasa abubuwan nan za su zo min a lokaci daya? Na runtse ido da mugun karfi sannan na saka hannu na share hawayena na bude idon na mike tsaye na fara tafiya, sai da na yi nisa na isa titin sannan na samu Napep na hau sai da ya fara tafiya sannan ya tambaye inda zai kai ni, sai na fada masa unguwa uku gurin Hajiya. Ban sauka ba sai da isa har kofar gidan.

“Malam bari na shiga na fito ka kai ni gida”

Na fada masa saboda babu kudi a hannuna, sai ya kashe sautin wakar dake tashi ya kashe napep din ni kuma na shiga cikin gidan dake bude. Bahijja na fara cin karo da ita tana bakin kofar dakinsu tana goge wandonta na makaranta da dutsen goge tufafi na gawayi.

“Sallama Alaikum”

Na yi sallama bayan na kusa isa kofar dakin.

“Wa'alaikissalam”

Ta amsa da mamaki na san ba zai wuce na ganina da ta yi ba kamar daga sama bayan kuma ta san ina jego ban isa fara fita ba, yanayi na kuma be nuna zuwan nawa na lafiya ba ne.

“Ina Hajiya?”

“Tana daki Lafiya?”

Ban sake ce mata komai ba na nufi dakin na shiga sai na kusa cin karo da Hajiya da ke kokarin fitowa.

“Zahra Lafiya?”

“Ba lafiya ba Hajiya, zuwa na yi na tambaye ki kuma ina son ki fada min tsakani da Allah, idan kin boye min ba zaki boyewa Allah, kuma duk ranar da na gane gaskiyar ba zan taba jindadin boyen min da kika yi ba”

“Miya faru Zahra?”

Kamin na ce komai Mai Napep din dake waje yayi horn.

“Bahijja je ki sallame shi”

Kamar umarni take jira sai ta tashi da sauri ta shiga daki ta dauko kudi ta fita waje, Hajiya kuma ta kama ni ta karasa shiga da ni dakin ta zaunar.

“Tambaye ni abun da kike so Zahra na miki alkawari matukar na san gaskiya zan fada miki”

Na kalleta idanuwa na cika da wasu hawaye daman can ba su cire jan da suka yi na kukan da na yi.

“Hajiya da gaske Deen yayi garkuwa da Mijin Yayar Abiey saboda a fasa aurena da Abiey? Da gaske Deen shi ya shiga tsakanin Soyayya ta da Abiey?”

Wani dauke numfashi ta yi ta sauke ajiyar zuciya sai ta amsa min kai tsaye amsa da mamakinta ya kusa saka ni suma.

“Gaskiya margayi ya shirya komai saboda ya bata alakarku da Abiey kuma saboda a fasa aurenku”

Baki sake nake kallonta sai ta fara hawaye.

“Amman be fada min yayi garkuwa da mijin Dr Zainab ba sai bayan da aikata, ki yi hakuri Zahra ki yafe masa ya aika abun da ya aikata ne saboda yana sonki...”

Na girgiza mata kai hawaye na sauko min.

“Wannan ba so ba ne, son kai ne... Idan har da gaske yana so ne, to zai so abun da nake so ne, ba ya jefani a halin da na shiga ba, Hajiya kuma kin san da wannan kika bar ni na tsani Abiey? Bayan shi yake da gaskiya? Wace irin uwa ce ke?”

“Wata uwa ce Zahra mai son abun da ďanta yake so, Zaharadeen be san komai ba a rayuwarsa sai shaye shaye, amman sanadin ki ya rage har ta kai ga ya daina gaba daya, shin miya ba zan so haka ba?”

Ta tashi daga inda take zaune ta nufi karkashin gadonta ta janyo wani akwaitin karfe ta bude ta dauko wani kwali ta miko min. Kamar ba zan karba ba sai kuma na saka hannu ya karba na bude farar takardar na fara yin arba da ita sai na saka hannu na dauka na bude takardar.
Chapter 38 · 0% Book details