← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 127

Sashe 1

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read


[9/28, 3:25 PM] Khadija Candy🥰: 16

Tun ina kuka muryata na fita har takai baka iya jin kukan nawa hawayen ma suka daina zuba sai ciwon idon suke min, bana iya ganin komai domin bana iya daga idon na kalli kowa, iyakar abun da zan iya shaida shi ne hankali ne be bace ba, domin ina jin lokacin da Mama da Yaya Maryam suka rika ni suka fito da ni mutane sai Allah ya ba da hakuri wasu na addu'ar Allah ya jikansa, ban tabbatar da mota muka shiga ba har sai da na ji muryar Mijin Yaya Maryam da kuma karar rufe motar da ta yi, ta zagayo ta dayan gafen ta shiga ta kwantar da ni jikinta.

“Kanwata ki yi hakuri kin ji? Allah baya barin wani dan wani, da yana barin wata rayuwa saboda wata, da ya bar uwar da mutuwa ta dauke ta bar jariri, ita mutuwa tana kan kowa, ke kanki idan lokacin tafiyarki yayi babu wanda ya isa ya tare, ke da kika rasa uba? Ai ke kin san zafin mutuwa Zahra, mun rasa uban tun ba mu mu mallaki hankalin kanmu ba balle yanzu da kika yi aure? Inda sabo ai ya ci ace kin saba da mutuwa ko? Ki yi hakuri ki dauki halin Annabawa, ki yi ta maimaita Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, yanzu addu'a da neman yafiya Deen yake nema ba kukanki ba, ki yi imani da Allah Zahra ki bar masa komai, Manzo Allah Sallalahu Alaihi Wassalam yace baya tare da mu wanda idan masifa ta same shi yake marin fuskarsa, yake kururuwa irin ta lokacin jahiliya wato mutun ya rika fadin ya bani ya lalace ya shiga uku da wasu maganganu da basa nuna cikar imanin bawa ga Ubangijinsa, yake keta tufarsa ko ya aske gashin kansa, sai kuma Annabi yace ka yi bushara ga masu hakuri wadanda idan masifa ta same su sai su ce mu a gurin Allah muka fito kuma a gurinsa za a mayar da mu, wato Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un hakika suna da yabo mai girma daga Ubangijinsu da kuma kyakkyawan sakamako”

Na daga mata kai kamar zan iya, cikin iyawar Allah ya yardarsa kamin mu isa gida bakina ya bude na yi ta nanata Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, Yaya Maryam na rike da ni har muka isa bakin kofar shiga gidana, a lokacin ne na ji wani abu ya taso ya tunkari zuciyata ya tokare kahon zuciyata, a yau zan shiga gidan da Deen ba zai sake shiga ba har abada, zan rayu ba tare da mijina ba. Wasu hawayen suka zubo min, haka muka shiga cikin gidan da har mutane sun fara taruwa a ciki, domin an sanar da rasuwarsa tun muna asibitin kuma abokinsa ya karbi makullin gidan ya bude saboda su suka zo da gawarsa da kuma mahaifinsa.
Duk makota na da suka shigo cikin gidan suna ganina sai hawaye wadanda zuciyarsu bata da karfi kuma suka saka kuka mai sauti, abun da ban sani ba, ashe an yi masa wanka anyi masa sutura, ina dosar falona sai mutane suka rika cewa kar a bar ni na shiga saboda ka yi kuka.

“Ba zan yi kuka ba ku bari na ga fuskarsa dan Allah”

Babu wanda ya bada goyon bayan a bar ni na ga gawar, ciki kuwa har da yan'uwansa da kuma nawa yan'uwa ciki har da Mama da ta iso yanzu bayan shigowa ta, domin a asibitin muka baro ta tare da Hajiya da aka sakawa drip. Hankalinta zai tashi be kamata a barta ta gani ba, zata yi kuka, kowa da dai da abun da yake fada.

“Ba zan yi komai ba, na san ni ai ba kowa ba ce tun da ban tare ransa na hana shi fita ba, na karbi wannan kaddarar da hannu biyu kuma na shirya rumgumarta kuma da yardar Allah sai na cinye ta, dan Allah ku bar ni na masa gani na karshe wannan ce kadai dama ta”

Na fada cike da gwarin guiwa, wata kila sun yardar da ni, ko kuma kalamai na ne suka karya musu zuciya, sai aka amince min na shiga na ga mijina. Daga bakin kofar Yaya Maryam ta sake ni na karasa cikin falon da kafafuwa da bake jin sun yi min nauyi har jini ya fara saukowa domin sun dan kumbura. A cikin karaga na hango shi kwance an masa sutura da farin lailai wanda shi ake yi ma kowa sutura talaka da mai kudi, bafada da Sarki, yana kwance a mike gurin daya babu motsi, a yau jikinsa na zama ba na shi ba saboda rai ya bar jikin, a yau sai dai a juya shi ba dai ya motsa ba, hakika na tabbatar da rayuwa ba komai ba, a jiya yana raye a yau kuma gashi a kwance. Na karasa kusa da shi na zauna na kai hannuna cike da imani na yaye likkafanin iya fuskarsa, sai na yi arbar da kyakkyawar surarsa fuskarta na ta haske kamar na kira shi ya amsa min.

“Ya masanin yau da gobe da jibi da anjima, ya buwayi gagara misali, ya mai rayawa mai kashewa, ya Ubangijina wanda kai kadai nake yi ma bauta, Allah ka sani na yi zama na amana da soyayya da mijina, ni da shi duka bayinka ne Allah masu yawan tsaba maka, Allah a yau ina son ka shaida na yafewa mijina duk abun da yayi min wanda na sani da wanda ban sani ba, da wanda ya sani da wanda be sani ba, ya Allah ina roka masa gafararka rahmarka da jinkanka, domin kai mai yawan yafiya ne mai yawan gafara, Allah a yau mijina ba shi da gata sai naka, Allah ka isar masa ka dauke masa tsoro da azabar kabari da na alkiyama, Allah ka sani Deen ya kyautata irin kyautatawar da miji na gari zai yi ma matarsa ya samu aljannarka, ya Allah ka bashi, yadda ya tsare mutunci ya tsare ci da sha na, Allah ka tsare shi daga azabar wutarka, Allah ka sani yayi min muhalli yayi min sutura Allah ka yi masa muhalin da sutura a aljanna, Allah ka yafe masa zubansa wanda ya aikata maka akan kuskure ko ganganci, wanda ke tsakaninsa da bayinka ka daukar masa, Allah ka lullube shi da rahmarka”

Na shafa addu'ar da na yi tare da hawayen da suka sauko min, sannan na yunkura na daga na sumbanci goshinsa.

“Ina son ka mijina, amman Allah ya fi ni sonka, fatar da ka yi ta haduwa da ni a aljanna Allah ya tabbatar mana sai wata rana Deen”
Chapter 1 · 0% Book details