Sashe 39
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_Zuwa ga wanda zata karanta wasikar nan zuciyata tana mai sosuwa da abun da na aikata, amincin Allah ya tabbata a gareki Zahra na sani a lokacin da zaki karanta wasikar nan bana raye domin rayuwata gajera ce shiyasa na zabi rayuwa da ke kamin mutuwa ta dauke ni. Na aikata abun da na aikata ne Zahra saboda ina kaunarki tun daga lokacin da na fara saka ki a idona zuciyata ta kamu da son ki, sai dai ba ni da halin nuna miki saboda hankalinki ba a gurina yake ba, kuma na san idan na nemi aurenki ba za a ba ni ba saboda ba ni da aiki bana sana'ar komai, gashi rayuwata ta lalace tun ina da kananan shekaru na girma da shaye shaye sanadiyar aike da ake ina soyawa, a lokacin da na ankara na gane illar abun da lokaci ya riga da kure min domin kuwa har shaye shayen ya yi min illa, sai dai son ki ya saka na fara boyewa Zahra, na fara kokarin sauyawa saboda na same ki, kamin zuciyata ta daya min cewar ba zan tana samun aurenki ba, saboda hankalinki gaba daya yana gurin Abiey ko bayan Abiey kina da wasu samarin da suke sonki wandanda suka fi ni komai, da za su siye soyayyarki a gurinki ko a gurin iyayenki, a ranar da aka yi miki baiko da Abiey Zahra ban dauka zan kai safe ba saboda bakinciki da ciwon zuciya, amman kowa be fahimci haka ba, daga lokacin ne na daura damarar ko ta halin yaya sai na aureki domin likitan da nake zuwa gurinsa yana duba ni ya tabbatar min da cewar na kamu da ciwon hanta mai hatsari, kuma idan har ban dauki mataki ba zan iya rasa rayuwa, a lokacin ba ni da wani buri da ya wuce na ga na mallakeki Zahra hakan yasa na boyewa kowa maganar kuma na aikata abunda na aikata saboda na san rayuwata ba mai tsawo ba ce, soyayyar da nake miki ta saka bana iya dauke hannuna daga jikinki balle har na nisance ki. Abiey yana da komai Zahra ni kowa ba ni da komai a zuciyata sai kaunarki kuma na shirya mutuwa a lokacin saboda ke, da gaske da ace Dr Zainab bata aikata abun da na umace da shi ba, babu abun da zai hana na kashe mijinta a lokacin, domin ina jin idan har ban same ki ba rayuwata bata da amfani, ina kaunarki Zahra fiye da yadda Abiey yake Sonki sai dai bana da wasu hujjoji da zan gamsar da ke akansu saboda na boye soyayyarki ne a cikin raina, kuma ba ni da wasu qualities da zai saka ke ko danginki su kauna ce ni, saboda na lalata rayuwata da shaye-shaye, amman Abiey mahaifinsa Sarki ne, mahaifiyarsa kuma mai kudi ce, shi ma sanannen mutum ne yana da kudi kuma baya shaye shaye ba kamar ni ba, ba zan iya kara da shi ba, gashi yayi min shigar kutso ya riga ni furtawa, na sani idan na furta cewar ina son ki a lokacin ba za a saurare ni ba, kuma ba za a bani ke ba, wata kila ma ace hassada na ke miki, ke ma kuma ba zaki kalle ni ba._
_Na sani abun da zamu haifa mace ko namiji biyu uku ko daya ba za su alfahari da ni ba, amman ni ina alfahari da ke da duk abun da za ki haifa min, kuma ina sonki kar tsanata ta saka ki kyamace yayana, kar tsanata yasa ki kyamaci mahaifiyata domin zaki karanta sakon nan ne bayan bana raye Zahra mahaifiyata kuma bata da kowa a lokacin sai Bahijja sai ke da abun da muka haifa, ki yafe min Zahra ki yafe min ki yafe min Ciwon so ne ya saka ni aikata haka, dan Allah kar abun da na aikata ya saka ki ji kin tsane ni ne, kuma har hakan ya saka ki manta da ni daga masoyinki mai kaunarki har abada.... DEEN_
Shakaf takardar ta jika da hawayena ina dagowa Hajiya ta miko min hotunana da suka dade da bata.
“Ga hotunanki, ajiya ta kare mai su ya tafi Zahra....”
Hajiya ta fada tana kuka, jimke hotunan na yi na lumshe ido, sai na ji Bahijja ta fashe da kuka.
[10/25, 12:25 PM] Oum_Nuwaira🥰: 3️⃣1️⃣
ABIEY POV.
After like awa daya da fitar Zahra Abiey ya sauko falon yana sanye da kananan kaya, kai tsaye dinning ya nufa inda mahaifiyarsa take zaune tana shan tea ya ja kujera ya zauna kusa da ita.
“Good Morning Ammy”
“An tashi lafiya”
“Alhamdulillah”
Ya amsa yana sauke ajiyar zuciya sannan ya dauki karamin tea cup ya aje gabansa.
“Bari na boiling ruwan tea”
“Jummai ba ta dade da zuba su a flask ba, na ce kar ta zuba da wuri saboda baka son ya dade a aje”
Kallonta yayi fuskarsa da murmushi ya mike tsaye.
“Ammy bari dai na tafasa shi da kaina”
Tabe baki ta yi ta girgiza kai tana kurba tea din.
“Aliyu”
Ya juyo
“Na'am”
“Idan ka dora ruwan ka zo ina son magana da kai”
“Okay”
Ya amsa sannan ya shiga kitchen ya dauki kettle din dake wanke aje ya sake wankewa sannan ya kunna tap ya zuba ruwan ya gona, kana ya juyo ya fito daga kitchen, a inda ya zauna dazun ya sake zama ya bude coolar dake gabansa ya dauki plantain ya kai bakinsa.
“Jiya ka dawo late kuma baka kwanta da wuri ba, domin ka kai har 1am a balcony, kuma na san dakin ka ma baka samu bachi da wuri ba, shiyasa ka fara late”
Ya dan yi jimmm sai kuma ya daga mata kai yana tauna plantain din a hankali.
“Why?”
“Jiya dai na je na yi magana da Yasmin, after that Sauban ya fada min Matarsa tace ta ga Zahra a wani gidan an gabatar da ita a matsayin yar aiki, to i went to that house na yi magana da ita na dauke ta na kaita gida, bayan na dawo kuma sai tunani ya hana ni kwantawa da wuri”
Ammy ta aje kofin tea dake hannunta tana kallonshi da irin duba na fahimta.
“Aliyu, ko ka lura yanzu zamani ya canja da za'ayi irin soyayyar da kake yi ma Zahra?”
“Ban fahimta ba”
“Shin baka taba tambayar kanka miyasa kai kadai kake son Zahra ita bata son ka ba?”
“No Ammy Zahra tana so na mana... ”
Ya amsa mata yana murmushi mamakin jin abun da ke fita bakinta.
“Me Zahra ta yi wanda zai tabbatar maka da haka? Da ace Zahra tana son ka kamar yadda kai kake son ta na tabbatar da yanzu ta bar komai ya wuce, shin fada idan kai ne zaka iya daukar fushi da Zahra na tsawon lokaci ko da ace ita take da laifi?”
“Ammy hankalin mace ba daya ne da na namiji ba”
“Haka ne, shiyasa ta zo har nan ta yi min warning cewar bata son ďana ya sake shiga lamarinta bayan ta mareka a gidansu ta ci mutuncinka, kuma ta tabbatar min da cewar ita tana da wanda take so”
Ya gyara zamansa da sauri.
“Zahra ta zo nan Ammy?”
“Eh ba ta wuce awa daya da fita ba”
“Kuma da gaske ta fadi abun da kika fada min yanzu?”
“Zan fara yi maka karya ne akan Zahra?”
A sauke kanshi kasa zuciyarshi na wani irin halbawa da mugun karfi.
“Aliyu ba zan cilasta rabuwa da Zahra ba, amman zan baka shawara a matsayina na mahaifiyarka idan zaka ji ka cire yarinyar nan a ranka ,wata kila ba alheri ba ce a gurinka shiyasa Allah be baka ita ba, kuma iya kar soyayya ka nuna mata Allah ma ya sani”
“Deen ya ci nasara...!”
Ya furta yana runtse ido tare da murmushin takaici.
“Wani lokacin kuma har da son zuciya, da ace Zahra na maka Kwatankwacin son da kake mata da yanzu ta yafe maka ko da kuwa ace ka aikata mata hakan da gaske, dan haka nake son ka bawa zuciyarka hutu ka saurara mata da zancen Zahra har na wani lokaci, shawara ta biyu kuma karka lalata zancen baikonku da Yasmin saboda Mai Martaba, kuma na tabbatar yarinyar nan tana sonka idan kuwa haka ne ya kamata ka duba mata domin ka fi kowa sanin yadda Ciwon So yake, wata kila ma sanadin haka Allah ya dube ka ya baka Zahra, Kuma Yasmin tana da tarbiya tana da hankali amman ita kuma kyakkyawa ce kamar Zahra”
Ya kalli Ammy da sauri.
“Ammy bana son Yasmin ban taba jin ina Son Yasmin so na aure ba ko soyayya, kawai dai ina mata kallon yar'uwa ne duk kuwa da kasancewar ban hada komai da ita ba, kuma tsakani da Allah zuciyata babu wanda take so sai Zahra, and Ammy kin sani mata basa son Kishiya ni ma kuma kaina ban shirya aje mata biyu ba...”
Yana kai aya Ammy ya mike tsaye a fusace ta daki dinning din.
“Toh sai ka je ka ji cigaba da son Zahra har sai son nata ya kashe ka sai a nada kambu a baka, amman bari ka ji na fada maka karka sake min maganar yarinyar a cikin gidana, kuma ina mai tabbatar maka matukar baka auri Yasmin ba, ba zan taba goya maka baya ka auri Zahra ba, ko da ta dawo maka, yarinyar nan bazawara ce ba budurwa ba kai kansa kasan abun magana zaka ja a gurin familyn mahaifinka amman a haka na goya maka baya saboda ina tunanin yarinya ce mai hankali, amman yanzu na gane kalarta kuma saboda ita ba zan yarda ka lalata auren da Mai Martaba ya nema maka ba”
Kamar ta jefar da kujerar bayanta haka ta ja baya da karfi ta fice daga dinning, Abiey ya bita da kallo yana mamakin yadda ta dauki zafi sosai akan Zahra. Mikewa yayi tsaye ya nufi upstairs dakinshi ya shiga ya dauko keys dinsa da wayarsa ya fito, sai da ya fice daga falon sannan ya kira Sauban ya labarta masa abun da ya faru tsakaninsa da Ammy.