← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 127

Sashe 45

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“I miss you...”

Ya furta har lokacin murmushi yake sai ya juya daga gefen da yake kwance ya saka wayar a hands-free ya sauka kan gadon ya nufi bathroom. Sai da ya raba jikinshi da tufafi sannan ya isa gaban shower ya kunna ya rufe ido, ta fara jika kanshi ruwan na sauka a jikinshi, ba zai iya kwatanta farinciki shi a yau ba, bayan godiya ga Ubangijinshi babu abun da yake sai da ko'ina na jikinsa ya san da farinciki zuciyar dake raba masa jiki da kaunar Zahra a yau, yana murza shower gel yana murmushi annurin fuskarshi na kara bayyana, sai da ya tabtace jikinsa ko'ina fes sannan ya kashe shower ya dauki karamin tawul ya daura ya fito rike da dayan yana goge jikinsa. Gaban katon madubu ya tsaya a zahira zaka yi tsammanin kyakkyawar surar jikinsa da mazantakar da Allah yayi masa yake karewa kallo, a baďini kuma tunanin rayuwarsa da Zahra yake, har ya shafa mai ya fesa jikinsa da turare ya nufi closet ya dauko pajamas ya saka be daina murmushi ba, shi kansa ya san ya kusa tabuwa a yau, domin ji yake ya cike wani gurbin wani karon rami dake zuciyarsa sai yake jin kanshi cikakaken namiji a yanzu. A inda ya aje wayar ya nufa ya dauka ya matsar da ita kunnensa har lokacin Sahibarsa bachi take tsalle yayi ya fada kan gadon yaja filo ya rumgume ya kara wayar a kunnensa ya rufe ido yana jin kamar Zahra na kusa da shi.

“Sleep tight Hiayatee... You have everything now”

Ya fada sannan ya kashe yanke wayar yana jin kamar ya dawwama yana sauraren numfashin bachinta. Ji yake kamar ba shi da damuwa kwata kwata a rayuwarshi a yau. Baka bukatata a yau, bachi ya fada masa shi kuma sai ya amsa masa da yes domin juyi ya rika yi kan gadon ya kasa bachi farinciki dake ransa da zumuncin sake saka Zahra a idonshi a gobe be bari bachi ma ya zo kusa da shi ba, ashe ba kowa bachi ke iya sata ba domin a yau Abiey ya tabbatar da haka, farinciki ya hana shi bachi ya rufe ido amman ya kasa bachi, da ya gaji da juyi akan fado ne ya tashi ya fito dakinsa ya sauko falon ya nufi kitchen ruwan zafi ya fara tafasawa yana ta kallon kitchen din kamar yau ya fara shiga.

“Abiey...”

Ya juyo yana jin kamar a lokacin Zahra take kiranshi, saitin inda take tsaye a wacan lokacin yake kallo tana rike da cinyar naman kaza.

“Zan cinye wannan sai ka cewa Ammy kai ka ci”

“Ba zan ce ba saboda ba ni na ci ba”

“Ni kuwa zan fadawa wannan yarinyar gaskiya na ce mata ba aurenta zaka yi”

Ya daga kafadunsa.

“I don't care idan na rasa mata, ke ma ba zaki samu miji ba”

A shagwabe ta murguda mishi baki ta harareshi ta sude hannunta tass sannan ta nufi kofa ta fice tana watso mashi harara. Juyawa yayi yana kallon kofar yana murmushi kamar dai wacan lokacin da komai yake faruwa. Ajiyar zuciya ya sauke ya dauki ruwan da ya gama tafasa ya zuba a cup ya fito ya dawo dinning. Zallar tea ya hadawa kanshi da two cube sugar ya matsa lemun tsami ya saka kayan koli sannan yaja kujera ya zauna ya fara motsawa, sai da ya rage zafi sannan ya fara kurbawa sai a lokacin ya tuna cewa be ci komai ba a yau kaunar Zahra kuma bata bari ya ji yunwa ba. A hankali yake kurba tea yana ajewa har yayi rabi sannan ya kwantar da kansa kan kujerar dinning din yana kallon Pop.

ZAHRA POV.

Ban san iya awanin da wayar ta dauka a kunne bayan nayi bachi, ni dai na farka na fa wayar a can gefe ni kuma ina karshen katifa rabon da na yi bachi mai dadi haka har na manta, duk kuwa da kasancewar babu komai a cikin mafarkina sai ďana. Bayan sallah asuba da kaina na fito na kunna wutar da Mama ta saba kunnawa na dora tukunya ita kuma ta zuba ruwan zafi sannan na koma na kwanta ita kuma ta yi alwala ta shiga ďaki ta yi sallah. Misalin bakwai na safe aka yanka ragon da Mama ta bada kudi aka siyo, na yi tunanin Baba zai shige gaba ayi komai da shi kamar yadda ya shige gaba gurin siyo ragon, amman sai abun ya sha banban domin saka talkamin shi yayi ya fice daga gidan bayan ya karya da dumamen tuwon da Mama ta yi, Sai da Mama ta nemo wani makocinmu ya yanka mata ragon aka gyara aka yi komai, sannan aka shigo dashi ciki gida, abun ka da kai mutane arziki kam la'asar ta yi har an gama gyara naman an soye shi rumus, sannan ta debar musu wanda zata ba su ta kara ta shigo min da nawa ta dauki nata.
A ranar na yi waya da Abiey ya fi a kirga, each and every minute sai ya kira ya ji lafiyata da muryarta, kinnci abinci? Me kike so? Me kike ji? Akwai abun da yake damunki? Su ne abun da yafi tambayata kamin ya roki a bar shi ya zo ya gan ni, ni kuma bana son na samu da Baba hakan yasa ban ba shi dama ba, ko baya ga wannan akwai mutane da yawa a gidan mu a yau da suka taya Mama aiki be dace su gan ni na tsaya da wani ina magana ba, wannan dalili ya saka Dr Hamid ma daya kira ni ya sanar min cewar yana kofar gidanmu yana son ganina ban fita ba, har ya gaji ya tafi, sai dai na wuni da rashin jindadin ďana a kusa da ni musamman soya naman nan da akayi sai a lokacin na ke kara ganin laifin abun da na aikata domin na yi sadaka a inda be kamata ba, Hajiya Jamila bata da kirki bata cancanci ďana ba, haka ma Deen be cancanci na siyar da rai saboda na ceto ranshi ba...

Da haka na kwashe kwana hudu ko kofar gidan ban je ba, a tsawon kwanakin nan kuma babu komai a zuciyata sai farinciki na kulawar da Abiey yake ba ni duk kuwa da kasancewar a waya ne kawai muke iya kasancewa tare da juna, ta dayan bangaren kuma ina tunanin ďana zuciyata na raya min kamar ba lafiya ba, musamman kwana biyun nan da Dr Hamid ya matsa min da rokon yana son na je gidan na bawa yaron Nono ko kuma na matsa a kai masa sai na ki yin ko daya, wani lokacin ma idan ya kira ni ba zan daga ba domin na san maganar da zai min kenan. A
Ranar da Mama ta karbi girki Ina zaune tsakar gidan ina wanke under wears dina ya shigo da cefane be yi sallama ba daman kwana biyun nan gaba daya ya canja daga shi har Hajiya domin ko naman da Mama ta aika musu kin karba ta yi, Baba ma da Mama ta ba shi na shi be karba ba, sai wani shan kamshi yake idan ya shigo cikin gidan, idan kuma yayi arba da ni kamar ya ga wata makiyiyarsa wani lokacin har mamakinshi nake, yadda ya take gaskiya idonsa suke nuna masa karyar a matsayin gaskiya..

“Sannu da zuwa”

Be amsa min ba, hakan yasa ban samu kuzarin na tashi na karbi ledar hannunshi ba. Har sai da ya karasa inda Mama take zaune tana gyaran shimkafa.

“Sannu da zuwa Ya kasuwar?”

Ita kam ya amsa mata shi ma ciki ciki kamar baya son magana, daki ya shiga be dade ba ya fito ya fice daga cikin gidan. Be dawo ba sai bayan sallah Isha'i yau ma a waje Mama ta yi mashi shimfida saboda ya bukaci haka duk da kasancewar akwai wutar nepa a dare. Ina jin yana kokarin kama Bbc ni kuma na gyara kwanciyata wayar Mama na gefena domin a yanzu kullum da wayarta nake wuni na kwana saboda yawan kiran Abiey.
Abun ka da ďan halak hausawa suka ce kak'i ambato, ina tsaka da tunaninshi a raina sai kiranshi ya shigo, sai na yi murmushi sannan ya dauka.

“Guess what?”

Na ďan yi shiru alamar nazari sannan na ce.

“Ka siye wani abu?”

“No wrong... Ina kofar gidanku”

“Wasa kake?”

“I'm serious”

Na tashi zaune da sauri.

“Amman Abiey na fada maka idan zaka zo ka kira ni”

“Na gaji ne Zahra kullum idan nace ina son ganin fuskarki sai ki kawo min wani uzuri, ki hana ni zuwa kin san kuma yadda nake marmarin ganin fuskarki”

“Shikenan zamu hadu a wani gurin amman ba gidan nan”

“Saboda me? Don't tell me mutane kike tsoro? + inda nake a yanzu mutane ba za su gan ni ba, kuma babu ma mutane da yawa a unguwar kin ga garin akwai hadari yawancin masu iyali duk sun shige gida”

“Abiey ba zai yiyu na fito ba”

“Ki taimaka min ko kofar gida ne ki tsaya ma ga fuskarki sai ki koma Wallahi Zahra na yi missing dinki tun ranar nan ban sake saka ki a ido ba”

“Akwai wata yar karamar matsala ne”

“Wace matsala?”

“Baba baya son ina kula mutane a yanzu sai nan gaba”

“Fuskarki kawai nake son gani Zahra please”

“No Abiey ba zan iya fitowa ba”

“Fine zan kwana a nan, ko kuma na yi sallama na shigo cikin gidan ki zabi daya”

“Ba zan iya zaba ba Abiey dan Allah ka tafi”

“Ba zan tafi ba sai na ganki Zahra”

“Kai ma ba girmanka ba ne a rika ganinka a unguwarmu”

“You think wasa nake ba zan tafi ban ganki ba? Trust me Zahra ba zan tafi ko'ina ba sai na ganki”

Na kashe wayar gaba daya gabana na mugun faduwa, domin har ga Allah bana son tashin hankalin Mama a yanzu, ga furucin da Baba yayi bmna cewar idan har na sake fita na fita kenan babu dawowa, na san kuma Mama ba zata yarda da wannan ba, hakan kuma ba karamar matsala zau haifar musu ba. Ina tsaka da neman mafita na ji sallamar yaron da zaton almajiri ko ďan makocin yana fadin.
Chapter 45 · 0% Book details