← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 110

Sashe 99

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha ta dafe kanta ta zauna a akan kujerar parlour da babu haske ta ce, "ni na gama aikin nan Safeera, ko da basu zarge ni akan ina fitar musu da sirri ba na daina, balle an zarge ni akan abinda ban aikata ba. Haka kawai akan aiki za a nemi ganin bayana? Sai ka ce aikin shiga aljanna ko na samun rahama? Su je can su ƙarata, amma ni na daina aikin gabaɗaya."

Safeera ta ce, "saboda su sai ki daina?."

"Ai na ma daina Safeera, ki je kawai, in ya tambaya ki ce na daina aiki, amma don Allah ki dawo ta nan."

Hasken falon aka kunna dukkansu suka kalli wajan, suka ganshi sanye da manyan kaya yana waya kamar ba ya son magana.

Safeera ta juya zata tafi, dan gabaÉ—aya kwarjini yake yi mata sosai, har mamakin Islaha take yi in ta ga yadda take faÉ—a masa duk abinda ta ga dama, ita ko kallonsa bata iya yi saboda kwarjini.

Zata sauka kenan Islaha ta ce, "don Allah ki dawo, kar ki tafi gida."

Ta waiwayo ta ce, "Islaha na bar Mama da ƙannena su kaɗai, ina so na koma gida nima."

Kamar zata yi mata kuka ta ce, "ni dai don Allah ki dawo in kin tashi daga wajan aikin, kar ki tafi."

"Ki zo mu tafi aikin, sai in dawo."

"Har abada, na gama aikin jarida."

"Shine burin ki fa."

"Na ajjiye." Safeera bata sake magana ba ta sauka tana dariya.

Bata sake kuskuren sake kallon inda yake ba, har mamaki take yi in yana waya anya mutanen da ya ke magana dasu suna jin me yake faɗa? Magana yake yi kamar ba ya so, a ciki yake maganar yana yatsine fuska kamar ko yaushe. Rehaan ya yi ajiyar zuciya yana shafa kansa, ta ƙasan ido take kallonsa ya cigaba da danna wayarsa.

Murmushi ta ga ya yi har haƙoransa suka bayyana, ya lumshe ido still yana kallon wayar bai ce komai ba.

Sai kuma ya kalli fuskar wayar alamun video call ya ce, "kin raina ni?." Cikin english ta ji mace ta ce, "me ka ce? Ka san ban iya fulfulde ba balle hausa." Ya sake yin murmushi kafin ya canja harshe zuwa hindi suna hira yana ta murmushi kamar ba shi ba.

_Budurwarsa ce mana, in ba ita ba wa zai dinga yiwa wannan murmushin?. Ko Mamy ba ya yiwa wannan fara'ar, amma yana yiwa wata yar india, shima da alama ya yi gadon babansa, ya É—auko yar india. Amma bata yi sa'a ba, zata auri ragon maza. Duk da ya yi min kirki kuma ya taimake ni, amma bazan fasa faÉ—ar halinsa._

Ita kaÉ—ai take gulmarsa a zuciyarta, bata san me ya tsare mata ba take gulmarsa ba.

Sai kuma ta ga ya kashe wayar ita dai bata ce
masa komai ba shima kuma bai ce mata komai ba.A lokacin aka kira ta a waya ta saka a kunne ta ce, "Hamma Saleem ya aiki?."

Saleem ya ce, "Lafiya lau Islaha, ba ki taho ba?."

"Na gama aiki da ku ai, ni na ajjiye jarida gabaÉ—aya."

"Meyasa?."

"Haka kawai."

"Haba Islaha, kamar ba ke ba? Don Allah kar ki taorata."

Ta taɓe bakinta cikin ko in kula ta ce, "Saleem kenan, zamu yi magana zuwa gobe in sha Allah" daga haka ta yanke wayar a bayyane ta ce, "haka kawai akan aiki ana neman kashe ni, me zai saka na koma? Su je su yi duk abinda suke so, ni na daina."

"Tsoro ki ka ji?."

Da sauri ta juya ta kalle sa ta ga ita yake kallo da alamun shi ɗin ne ya yi magana ba wani ba, suka haɗa ido dan bata taɓa tunanin zai yi magana ba.

Islaha cikin sanyi murya ta ce, "Eh tsoro nake ji, bazan iya zama a inda aka ƙoƙarin kashe ni ba, bayan kisa harda sharrin da bazan manta da shi ba. Har yanzu wasu basu yarda bani ce a videon nan ba, akan me zan kai kaina inda ake son kashe ni? Gwara na haƙura kawai." Ta ƙarasa tana sunkuyar da kanta ƙasa

Ya zuba mata ido yana nazarinta sannan ya ce, "Kina son aikin?."

Ta ɗago tana kallonsa, sai ta yi raurau da ido kamar zata yi kuka ta ce, "amma aikin ba ya sona, ina son aikin jarida saboda burina ne, amma aikin jarida ba ya sona. Gwara na haƙura na basu space tunda suna ganin nice nake tare musu ɗaukakarsu, sai su yi abinda suke so."

Yadda take kallonsa idanunta ya ciko da hawaye ya saka shi ya lumshe ido ya buÉ—esu a kanta, ya gyara zama yana kallon ta ya ce, "ai su basa nan, beside yau za a kai su prison."

"Bayansu akwai wasu, tunda aka samesu za a samu wasu masu irin ƙudurinsu a zuciya. Gwara na haƙura kawai, na yi fatan Allah ya zaɓa min abinda ya fi alkhairi a rayuwata."

Ya yi shiru kamar bazai ce komai ba sai daga baya ya ce, "in tsoro ya saka ki ka ajjiye abinda ki ke so an yi nasara a kan ki, sun samu nasara tunda kin bar abinda suke so ki bari. Behind every success there are challenges, Every achievement comes with its own unique struggles, ke wannan ne ƙalubalen ki. Ba dani da ke aka yi attacking ɗina ba?."

Islaha É—ago ido tana kallonsa ganin yadda ya zuba mata ido yana kallon ta kamar ba shi ba, ya ga ya wani nutsu yana magana kamar ba shine mai talakarta da faÉ—a ba. Sai ta É—aga masa kai ta ce, "eh dani, but...."

Ya dakatar da ita ya ce, "but what..? Ina da banbanci dake?."

"Eh mana, kai daban ni daban."

Ya yi murmushi ya ce, "every succes is succes. In ki ka bari aka yi nasara a kan ki kin faɗi" ya faɗa yana yi mata alama da thurm ɗinsa ya juyasa ya kalli ƙasa alamun rashin nasara.

Ta kalle sa tana mamakin yadda yake yi mata maganar da zata ƙara masa ƙarfin guiwa, basu taɓa doguwar magana shi da ita irin haka ba, sai dai faɗa ya haɗa su. Rehaan ya ce, "ki cigaba da aikin ki as you can, in za ki bari ki bari saboda ra'ayin kan ki ba dan wasu ba. So don't let anythings make you afraid, har ki ce za ki daina aikin ki saboda su."

Islaha ta yi shiru tana sauraren yadda yake yi mata magana cikin yanga da iyayi, ba a taɓa yi mata maganar da ta shiga zuciyarta lokaci ɗaya ba, bata taɓa jin bata son abu an yi mata magana ta ji tana so ba sai yanzu.

Jin kalamansa take yi kamar ruwa ya ɗauka yana watsawa zuciyarta har ta wanke tas, tana tunanin wato shiyasa masu kuɗi suke samun nasara a rayuwarsu, ba sa barin ƙaramin abu ya tayar musu da hankali har su daina abinda yake gabansu saboda shi.

Ta É—ago ta yi masa murmushi a karo na farko a zamansu, ta yi masa murmushin da ya kai zuciyarta ba iya fuskar ta ya tsaya ba.

Ta É—aga masa kai ta ce, "na gode."

Bai ce mata komai ba ya ɗauke kansa amma shi kansa ya ji daɗin hirasu, basu taɓa zama sun yi magana haka ba sai dai faɗa ya haɗasu, amma yau sai ya ji abin daban a ransa.

Kiran da ya shigo wayarta ya saka ta É—auka ba tare da damuwa ba ta ce, "Hamma tun jiya nake kiran ka ba ka É—auka, kana ina?."

Saheer ya ce, "bana jin daÉ—i ne. Ya ki ke?."

Islaha ta ce, "me ya same ka?."

"Kar ki damu ba wani abun bane. Kina lafiya, ina fatan kin samu sauƙi ko?." Ta ɗaga kai kamar yana gabanta tana wasa da adon rigarta ta ce, "na ji sauƙi."

"Komai ya wuce ko?."

Ta É—aga kai ta ce, "ya wuce Hamma. Ashe daman Ummi da Muslim ne? Daman ka jima kana cewa baka yarda da shi ba, ni kuma har ga Allah da zuciya É—aya nake tare dasu."

Saheer ya ce, "ke dai ki ga mutum kawai."

"Haka ne kam, Yaushe za ka koma?."

"Zuwa next week zan koma, bazan dawo ba sai kin dawo gida."

Ta yi numfashi ta ce, "ni fa ko na bar nan bazan dawo gidan Mama ba, gwara na samu wani wajan na zauna."

Saheer ya ce, "zamu san abinda zamu yi in lokacin ya yi, saura kwana nawa?."

Islaha ta ce, "saura sati biyar lokacin ya cika, lokacin ne ba ya gudu, kamar ba kwana ake yi ana tashi ba. GabaÉ—aya na gaji da zaman, so nake nauyin da yake kaina ya sauka na huta."

Saheer ya ce, "uhum! Har wani nauyi ne a kan ki?."

"Hamma aure fa, ai ka san ko ya ya ne aure dai sunansa aure. Nauyi ne a kaina mana, tunda Allah ne ya É—ora min."

"Ya yi kyau. Sai ki sauke nauyin ai."

Ta yi dariya ta ce, "ina nan ina sauke shi."

Saheer ya ce, "shikenan zan je wajan Adda."

"Sai ka dawo."

Daga haka ta yanke wayar ta ɗora ta a ƙirjinta ta rufe idanunta, dan ita har ga Allah ta manta da Rehaan a wajan, wayarta take yi da zuciya ɗaya ta manta shaf yana wajan a zaune.

Sai ta buɗe ido ta ce, "saura kwanaki kaɗan na bar gidan nan na huta da wannan tashin hankali, ni kaina na ƙosa lokacin nan ya yi, ko za a daina yi min sharrin ina kawo wani parlour nan" ta faɗa tana lumshe ido tare da kwanciya a jikin kujera.

Rehaan yana jin duk hirar da take yi, har amsar da Saheer ya ke bata yana ji.

Lokaci É—aya ya ji zuciyarsa babu daÉ—i ko kaÉ—an, ya so ya tashi ya bar mata wajan, amma gudun kar ta yi tunanin wani abun ne sai ya zauna, amma ko kaÉ—an bai ji daÉ—in wannan wayar ba ko kusa, har zuciyarsa yake jin kalamanta ma su É—aci.

Ya sake kallon ta ya ga idanunta a rufe, ya ɗauke kai yana tunanin da gaske saura wata ɗaya, ya aka yi lokacin ya yi gudu haka bai sani ba?. Ya miƙe ya sauka, giftawarsa ta gani ta buɗe ta ga har ya sauka.
Chapter 99 · 0% Book details