Sashe 50
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai kuma ya yi shiru yana tunani sai ya kira Sadik a waya yana ɗauka ya ce, "Sadik akwai kuɗi a hannunka? Akwai inda ba a gama saka kayan wuta a gidana ba, shi nake so na siyi na ƙarasa a huta. Bana son komawa Nijar ban gama abubuwan da suke gabana ba."
Sadik da mamaki ya ce, "Gaggawar ta me ye?."
"Ta aurena mana, ka manta nan da wasu kwanaki kaÉ—an Islaha zata dawo mu yi aure?."
Sadik ya yi tsaki ya ce, "Wallahi ban taɓa sanin ba ka da hankali ba sai yau, kai wai har jiranta ka ke yi ta fito ka aure ta? Ko kishin abinda ka ke faɗa ji a ranka?."
Saheer ya ce, "Kaine ba ka da hankali da ba ka san meye so ba, kuma meye abin kishin tunda ina sonta?."
"Soyayya in dai irin wacce ka ke yiwa Islaha ce Allah ya yi wadaranta, dama nawa ka samu saboda ita ka ƙi karɓa?. Ko a yanzu akwai dama a hannun ka, amma kana ƙoƙarin saka ƙafa ka yi ball da ita."
"Ka ga, in kana da kuÉ—i ka bani, in babu ka yi min shiru. Wata biyar kamar yau za ka ga ta zo, a ranar da auren ta ya mutu, a ranar nake so a É—aura mana aure."
"Ko? To kai za ka yi mata iddar kenan?."
"Babu idda a zamanta da shi, ana idda ne don a tabbatar akwai ciki ko babu, to ita babu wannan labarin."
Sadik ya sake yin tsaki cikin takaici ya ce, "Kai kana tunanin zata fito haka ba tare da anyi komai ba, kana zaton zama kawai suke yi a waje É—aya ba tare da ya mori sadakinsa ba?. Ka tuna naira miliyan hamsin ya bata, a tunanin ka kuÉ—insa a banza zasu tafi bai fanshe da wani abun ba?."
Saheer ya ce, "Malam ya ishe ka haka, ka daina yi min wannan maganar."
"Dole na yi maka, na lura kana neman ɓacewa daga hanya mai kyau, kana ƙoƙarin ɗora kanka a gurɓatacciyar hanya. Zan iya yi maka rantsuwa akan ko da Islaha zata fito baza ta fito kamar yadda ta shiga ba, in ma ta fito ɗin fa kenan. Gwara ka saki jikinka ka karɓi damar da ta zo maka, ka tara kuɗin gama gidan ka, in ta fito fine, in bata fito ba daman ka samu rabon ka."
Saboda haushi Saheer kashe wayar ya yi ya dafe kansa, yana jin wutar kishi tana kunnuwa a zuciyarsa, shaiɗan sai hango masa Islaha yake yi cikin bahagon yanayi. Ya daki kanaa da ƙarfi, ya ɗauki waya yana kiranta amma bata ɗauka ba, ya yi tsaki yana ji kamar ya miƙe ya je gidan, da hanzari ya miƙe ya fita daga ɗakin cikin yanayi mai zafi.
Islaha lokacin da ta shiga ɗaki laptop ɗinta ta ɗauko, har zata sakka downstairs sai ta kalli ƙofar ɗakinsa, ta tsaya tana kallon ƙofar a bayyane ta ce, "Sai na shiga ɗakin nan, na ga meye a ciki."
Ta ajjiye laptop ɗin akan kujera ta shiga ɗakin, ta bi ɗakin da kallo dan komai a kashe yake ba ka ganin komai. Ta kalli gefenta ta ga switch, ta harari switch ɗin dan daƙyar ta iya amfani da shi da ta zo gidan, touching switch ne, wanda sai ka kula za ka gane yadda ake amfani da shi. Ta danna haske ya gauraye ko ina ta bi ɗakin da kallo.
Ɗakin yana da wani irin kyau mai ɗaukar hankali, ga girma kamar zaka raba ball a cikinsa. Falon da yake cikin ɗaki ne yake burge ta, ta ƙarasa ta buɗe glass door ɗin ta bi falon da kallo ganin babu abinda babu a cikinsa kuma komai fari, ga wasu kujeru kamar gado kamar kujera. Ta tsaya tana kallon luxury parlour, kafin ta fito ta shiga prayer room da aka gidana shi a karkace, kai tsaye alƙibla ya ta kalla.
Sai ta ji prayer room É—in ya fi burge ta sama da falon, ga shi dai ba shi da girma, bai fi zaman mutum biyu ba.
Ta kalli alkur'anin da yake ajjiye ta riƙe baki ta ce, "Ashe ya san karatun alkur'ani" ta fito tana kallon bed ɗinsa.
Closet ɗinsa ta shiga tana kallo, ta ga kaya kamar wajan siyarwa, musamman suits da yallabiyya suna rataye a jikin anger, komai yana mahallinsa. Islaha ta wajan ta kalli bathroom ta ce, "Daga an fito daga wanka sai a shirya kenan. Allah ka yiwa Hamma arzuƙi ya yi min irin haka, har prayer room ɗin can ina so" ta faɗa tana ɗaukar hait burner ɗinsa.
Tana kunnawa hayaƙi ya fara fita kaɗan kaɗan, ƙhamshi ya cika mata hanci, ta juyata a hannunta ganin samanta da comb, ta taɓe baki ta ce, "wai burner ta gashi ce kenan? Allah ya isa, ni da na ke mace ma ba na turara gashina, sai dai na saka hair spary na wuce wajan. Amma shi yana namiji kalli kayan gyaran gashi har ya fi nawa, kalli turaruka kamar ba a so. Allah ya yi mana arzuƙi mu samu abinda ya fi wannan, ba dan an gama gina gidan da zamu zauna Hamma ba, ai da na saka an yi min closet ɗin nan."
Ita kaÉ—ai take jawabinta ba da wani ba, ta kai hannu ta buÉ—e drawer, ta ga undies ne kawai a ciki a shirye kuma a ninke. Shorts É—in gabaÉ—aya kamfanin Nike ne, haka takalmansa na ball, da slipper duk kamfanin Nike ne.
Islaha ta taɓe baki ta ce, "Wannan dai sai dai in cleaner ɗinsa ne yake gyarawa, wancan ragon me zai iya? Komai ya gaji kamar ba namiji ba. Shi fa wannan da mace ya yi kama, bashi da wata kama da ta yi kama da ta maza, komai....."Maganar ta tsaya a lokacin da hotonsa ya gifta a idanunta ranar da ta gan shi babu riga.
Ta runtse ido ta ce, "Astagafirullah! Allah ka sa na daina tunanin wannan mutumin."
Bathroom ta buÉ—e tana kallo ta ce, "wow!."
Ta shiga tana kallon ko ina a bathroom ba, ko body wash É—insa ma sun fi kala goma, ga perfumes, ga shampoos, towels, bathrobes da sauran haukan da bata san na meye ba.
Ta gyaÉ—a kai ta ce, "Allah ka azurta ni, wallahi sai na yi irin banÉ—akin nan. Ni fa ina son luxury life, kawai Allah bai yi zan auri mai kuÉ—i bane, amma da anga gayu" ta faÉ—a tana kunna wani waje take iska ta fara fitowa alamun dryer ne.
Bathtub yana waje É—aya daban, mai cycle shape na mutane biyu, har da wani pillow a jikinsa guda biyu alamun an yi sa ne domin couples. Shower glass ma yana wani waje daban, ga latirine É—in ma a wani waje daban, komai perfect kamar ka kwanta a ciki.
Ta gama kallonta sannan ta fito tana kashe hasken ko ina tana raira waƙar sarkin waƙa tana cewa, "Allah ka ba mu kuɗi, amma wanda ya amsa kuɗi, amin." Ta gama kallon ta ta kashe hasken ta fito falo, ta ɗauki laptop ɗin ta sauka ta koma ɓangaren Mamy.
Babu kowa a falon ta wuce É—akin da aka ajjiye ta tana ta kunna laptop É—in tana dannawa.
Aiki take yi sosai, tana haÉ—a questions interview É—in da zata yiwa guest É—inta a gobe.
Tana cikin aiki aka buɗe ƙofar aka shigo, ta ɗaga kai ta ga Banisha ta shigo da Laptop a hannunta tana cewa, "Bruh ga Sis Islaha" ta faɗa tana juya screen ɗin ta haska masa fuskar Islaha ita kuma ta kalli screen ɗin.
Kai tsaye suka haɗa ido da shi yana zaune a sofa ya miƙe ƙafa, hannunsa riƙe cup yana shan tea.
Kallo É—aya ta yi masa ta É—auke kai, Banisha ta ajjiye mata laptop É—in ta ce, "Ina zuwa" ta faÉ—a tana fita, ita kuma ta share shi bata kuma kallonsa ba balle ta ce wani abun.
Shi kuwa kallonta ta yake yi yana mamakin ƙarfin hali irin na yarinyar, tunda suka fara zama bata taɓa ce masa good day ba, yanzu ma ga shi an haɗasu ta wani juyar da fuska tana aiki kamar bata ga kowa ba. In akace a duniya akwai macen da zata yi masa haka zai iya cewa ƙarya ne, amma ga wata da ya raina, yake yiwa kallon ƴar bariki ta mayar da shi kamar abin wasa.
Islaha har ga Allah ta manta da laptop É—in da Banisha ta bari a wajan, aikinta take yi hankali a kwance kafin ta duba wayarta.
A bayyane ta ce, "ashe Hamma ya kira ni" ta faÉ—a tana kiransa.
Shi dai Rehaan kallon ikon Allah yake yi, yana jinjina ƙarfin hali da zaƙewar ta, yana so ya ga adadin lokacin da za ta ɗauka tana raina masa hankali, shiyasa ya yi shiru yana kallon duk wani motsinta kamar tv.
Saheer yana É—auka ta ce, "Hamma ka kira ni bana kusa sai yanzu na ga kiran ka."
Saheer ya ce, "Ina so na ganki Islaha, ya za a yi?
Za ki zo ne ko na zo?."
Islaha ta buÉ—e ido waje ta ce, "A'a kar ka zo, in an yi sallar la'asar zan fito, a ina zan ganka?."
"Ki kira ni in kin fito É—in, zan faÉ—a miki inda za ki je."
"to Hamma. Ka siya min lays cheese." Saheer ya amsa mata ita kuma ta kashe wayar tana murmushi har ga Allah ta manta da wani Rehaan a gefenta.
Kamar an ce ta juya ta kalli system ɗin, sai ta ga ya zuba mata idanu kawai yana kallonta. Islaha ta dafe ƙriji cikin firgici ta ce, "Innahu min sulaimanu, wa'innahu bismillahir rahmanir rahim!" Ta faɗa a tsorace irin wacce ta ga aljani, dan da gaske ganin fuskarsa tsoro ya bata.
Maimakon ta yi masa magana sai ta ga babu amfanin yin maganar, ta sake É—auke kanta dan wallahi in bai yi mata magana ba itama baza ta yi ba.
A lokacin Banisha ta dawo ɗakin, Islaha ta kalle ta ta ce, "Banisha ana neman ki, ɗauke laptop ɗin ki aiki nake yi.†Banisha ta ɗauka ta fita.