← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 110

Sashe 77

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ɗan yi murmushi ta ce, "Ma sha Allah! India, Engaland, Nigeria, in aka baka zaɓi akace ka zaɓi ina za ka ɗauka?."

Ya É—an sauke numfashi ya ce, "Nigeria."

"A ina ka fi jin daɗin rayuwa a cikin waɗanan ƙasashe?."

"Englaand."

"Muna ta jin magana tana ta yawo a ko ina, ana ta yaÉ—awa ana cewa Mr Rehaan ya yi auren sirri, da gaske ne akwai auren ko babu?."

Nana Haleema.

RDB3P58
Nana Haleema.

Rehaan ya ɗan yi shiru yana kallonta, ita kuma ba shi ta ke kallo ba, ta ɗan ɗauke kanta tana addu'ar Allah ya sa kar ya tona musu asiri ya amsa ta shiga uku. Shi kuma kallonta yake yi ganin ta wani nutsu kamar ba itace mai bakin rashin kunya ba, kamar ba ita ya ritsa ta kasa magana ba.  Rehaan ya ɗaga kai ya ce, "kin ce auren sirri, kuma me ki ke so na ce miki?....." ta ɗago ta kalle shi suka haɗa ido.

Ya ɗaga gira sama ya ce, "Sirri ne" ya faɗa yana kallonta.  Sai da ta yi ajiyar zuciya saboda jin daɗi sannan ta ce, "abinci fa? Biryani, Fura da nono ko kuma Burger, wanne ka fi so?."

"non of the above."

"muna jin labari akan Mr Rehaan yana shirin shiga siyasa, da gaske?."

"No."

"Akwai shirin shiga siyasar nan gaba?."

"babu."

"Kwanaki an kai maka hari, har aka dinga tunanin an cutar da kai. An samu labarin waÉ—anda suka kai harin?."

Ya girgiza kai alamun a'a ya ce, "ana aiki akan hakan."

"Kasancewar ka mutum na farko a Yola mai  ƙarancin shekaru da Allah ya bawa dukiya da baiwa mai yawa, wanne irin ƙalubale ka ke fuskanta akan hakan?."

Rehaan ya ɗan yi shiru yana tunanin meye ƙalubale da hausa, ya san kalmar amma ta kwanta masa bai fahimci maganar ba.

Ya ɗan kalle ta ya ce, "Ƙalubale...." Ya faɗa yana kallonta alamun me take nufi.

Islaha ta yi masa kallon ka raina min hankali, amma da yake babu damar magana sai ta ce, "ina nufin challenges."

"Mun yi maganar attack, and babu privacy."

"Inda za ka zama shugaban ƙasar nigeria, wanne abu za ka fara gyarawa?."

"Tsaro. Nigeria babu tsaro at all."

"Me yake saurin ɓata maka rai?."

"Mutum mai fuska biyu, a haka kamar mutumin kirki, amma ba haka bane."

Islaha ta san da ita yake amma bata nuna ba ta ce, "Me ya ke saka ka farin ciki?."

"My family."

"Akwai wani shiri da Mr Rehaan yake yi wanda zai taimaki nigeria gabaÉ—aya?."

"in sha Allah."

"Allah ya taimaka ya ba da nasara."

"amin."

"Daga ƙarshe wacce shawara zaka bawa matasa ma su irin shekarun?."

"Be smart, work hard, work smart. Kar ka raina duk abinda Allah bayar, a tsarkake zuciya."

Zata sake magana ya rigata ya ce, "Ya sunan ki ka ce?."

Ta wani kalle sa suka haÉ—a ido, ta san da gangan yake yi mata hakan dan bata da bakin ramawa tunda a gaban camera take, sai ta ce, "Islaha."

Rehaan ya ce, "Kin san parrot?."

"Na sani."

"Meye sunan shi da hausa?."

Ta kallingefenta sannan ta ce, "Ban san sunan da hausa ba" ta faÉ—a jin yana raina mata hankali.

Rehaan ya ce, "ki ƙara parrot a gaban sunan ki."

Ta yi murmushi mai sauti ta ce, "na gode Mr Rehaan."

Islaha ta sake kallonsa ta ce, "mun gode da aka ba mu aron lokaci muka tattauna da kai a cikin wannan shiri na mu."

Ya gyaÉ—a mata kai yana kallon fuskar ta ya ce, "can i ask you a question?."

Islaha duk da gabanta ya faÉ—i, amma tunawa a gaban camera take sai ta ce, "Yes Sir."

Ya É—an yi jim kamar zai yi magana sai kuma ya ce, "is okay."

"Mun gode da aka ba mu damar kasancewa da kai, haƙiƙa babbar nasara ce a gare mu da garin Yola gabaɗaya." Da ido ya bata amsa ta kalli camera ta yi sallama da masu saurare sannan aka kashe camera.

Jazy ya yi clapping hannunsa ya ce, "weldone miss, kin yi ƙoƙari."

Ta yi muemushi ta ce, "thank you Mr Jafar."

Ta kalli Rehaan ta ce, "thank you Mr Rehaan."

Bai ce komai ba ya miƙe tsaye Chairman ya ce, "mun gode ranka ya daɗe."

Ya yi ya ce, "Your welcome, amma nan gaba ku canja presenter, wannan kamar bata san aikinta ba."

Islaha ta wani kalle sa jin abinda ya ce, kowa ya kalle sa dan babu wanda bai yaba mata ba, Rehaan bai ce komai ba ya shiga ciki.

Chairman ya ce, "Duk ƙoƙarin da Iskaha ta yi, ko akwai tambayar da ki ka yi bai ji daɗi ba?."

Jafar ya yi dariya yana aiyana Chairman bai san dawar garin ba ya ce, "Ku manta kawai, ya faɗa ne kawai, amma Islaha ta yi ƙoƙari. Kar ku damu" ya faɗa yana shiga ciki.

Sai a lokacin Chairman ya ji daɗi, ya ce, "islaha ke ta daban ce, Allah ya cigaba da ba ki kariya." Ta amsa Safeera ta yi hugging ɗinta dan hirar ta ƙayatar.

A kunne ta raÉ—a mata ta ce, "ke gayen nan anya bai afka ba, wani irin kallo yake yi miki fa."

Ta mintsine ta a ciki ta ce, "Allah ya kiyaye."suka yi dariya gabaÉ—aya aka fara tattara kaya.

A lokacin Jazu ya fito ya kalli Islaha ya ce, "Miss, Rehaan yana magana da ke." Gabanta ya faɗi, dan bata so a san da wani abu a ƙasa tsakaninsu.

Ta kawar da tsoron ta ce, "Dani kuma? Allah ya sa ba laifi na yi."

"Kar ki damu" ya faÉ—a yana dariya ya fita daga falon.

Ta kallu Chairman ta ce, "mai zai kira ni ya cemin?."

Chairman jikinsa har rawa yake yi ya ce, "Jeki mana, ba ki san me zai ce ba."

Ta nufi inda Jazy ya fito ta same sa a zaune ya cire court ɗin jikinsa ya ɗora ƙafa kan ɗaya.

Ta tsaya tana kallonsa ta ce, "gani."

Ya É—ago ya kalle ta amma bai ce komai ba, sai ta ce, "ance kana kira na, kuma na zo ka share ni."

Ya san Jazy ne ya turo ta, shi kuma ya cewa Jazy ya tura musu kuÉ—in mota, sai ya ce bazai tura ba bara ya kira Islsha ta tura musu, shine ya turo ta.

Ya ɗauki cheaque  ya ce, "It's just a small gift for your TV channel."

Ta hararesa kafin ta miƙa hannu ta karɓa ta ce, "sun gode."

Rehaan ya kalli idanunta  ya ce, "ke babu ke?."

"Ai ban ce ina buƙata ba."

"Su ma basu ce ba."

"kai kaga zaka iya, ni ban ce a bani ba, bani da buƙatar ko sisin ka."

Rehaan ya É—aga gira yana kallonta ya ce, "Saboda ke matar Rehaan ce?."

Islaha ta kalle shi da mamakin abinda ya ce, rana ta farko da ya kirata da matarsa tunda suka fara zama tare. Bata nuna masa ta yi mamaki ba ta ce, "Waye Rehaan É—in?."

Rehaan sai da ya yi murmushi sannan ya ce,"Your guest."

"Ni ba matarsa ba ce, ni Contract wife ɗin Rehaan ce, lokaci na ke jira na kama gabana, bani da buƙatar komai nasa" ta faɗa kawai ta juya ta fita.

Tana fitowa ta bawa Chairman ta ce, "ya ce gift ne."Chairman ya karɓa ya ga kuɗin ya zaro ido ya ce, "15 milions."

"Ga shi nan ka gani, don Allah mu tafi na gaji wallahi" ta faÉ—a cike da gajiya.

Suka fito gabaÉ—aya ana ta cecekuce akan kuÉ—in har aka shiga mota. Islaha a hanya ta sauka, dan sun yi da Barr zasu haÉ—u. Safeera aka sauke ta a gida gab da zata shiga gida Saheer ya ce, "Safeera."

Ta kalle sa ta ce, "Hamma, ina yini."

"Lafiya lau. Ina ta kiran ki ba ki É—auka ba.

"Wallahi ba ma nan, mun je interview dasu Islaha shiyasa."

Saheer ya ce, "na yiwa ƙawarki laifi, ina ta neman sulhu ta ƙi bani dama."

Safeera ta ce, "gaskiya dai Hamma Saheer ba ka kyauta ba, ta zo nan tana ta kuka, kuma ta bani labari. Ko me Islaha zata yi bata cancanci abinda ka ce mata ba, dan ka san ta yi auren nan saboda kai, tana zauna saboda kai, tana yin komai saboda kai. Har saɓon Allah take yi saboda kai."

"saɓon Allah kuma Safeera?."

"Eh mana Hamma. Magana da take zuwa tana yi ai saɓawa Allah ne da rashin ɗaukar aure da mahimmaci. Maganar da ta ke yi da kai rubuta mata zunubi ake yi, tunda kai ba muharraminta ba ne, kuma ba magana irin ta yaya da ƙanwa ku ke yi ba, kuna magana akan yaushe za a ku yi aure da sauransu. Ka ga kuwa babban laifi ne tunda da aure a kanta, babu ruwan Allah da auren da tayi, aure sunansa aure tunda an shaida an kuma ba da sadaki. Ina yawan yi mata faɗa akan hakan, amma sai ta nuna min kai ka fi kowa mahimmaci a wajanta, amma kuma kaine ka faɗa mata maganar da ta saka ta kuka. Gaskiya ta ji haushi, ta ta ce min bata taɓa jin haushinka kamar ranar ba."

Saheer ya yi ajiyar zuciya ya ce, "kuskure aka samu, in Allah ya yarda baza a sake ba."

"Me zai hana baza ka faÉ—a mata asalin waÉ—anda suka baka ita ka kai gidan marayu ba?."

"Safeera inda zai yu zan faÉ—a mata, amma abin ne babu daÉ—in ji shiyasa bana so ta damu."

"To ka samu abinda zaka faÉ—a mata, wanda ka san zata iya É—auka kafin ku sake haÉ—uwa, dan tana kewar iyayenta sosai kuwa."

"in sha Allah zan yi. Ki ta ya ni bata haƙuri, ko da ba mu haɗu ba ta ɗauki wayata na bata haƙuri. Kamar yadda ki ka ce zan dinga kiyayye haɗuwa da ita har lokacin da komai zai daidaita. Hankali ya gushe, na manta da haramcin da yake cikin hakan, ba ita kaɗai ake rubutawa zunubi ba har da ni, tunda na san tana da aure."

"Hakan ya fi kam, Allah ya taimaka mana."

"Amin Bestiyn bestie, na gode da ki ka fahimce ni.
Chapter 77 · 0% Book details