← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 110

Sashe 11

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safeerw ta ce, "Ke ƴar halak ce, ki daina wannan banzan tunanin. Sadaukar da rayuwarki ki ka yi saboda shi, babu macen da zata iya ganganci da rayuwarta akan namiji kamar yadda ki ka yi. Kina son Saheer kowa ya sani, shiyasa ki ka yi duk abinda ki ka yi saboda ya samu kuɓuta ya dawo gare ki, kuma kin yi nasara ga shi ya dawo. Don Allah ki nutsu, ki bari a kwana biyu sai ki zo ku yi magana, zai fahimce ki yadda ya kamata."

Islaha bata ce komai ba sai kuka take yi mai sauti, Safeera ta ce, "ki daina kuka don Allah, ki yi haƙuri komai zai wuce."

Islaha bata daina kuka ba sai jan numfashi take yi, sai kuma ta lumshe ido ta ce, "ni zan yi cancelling contract É—in nan, bazan iya zaman wata biyar a nan ba. Kwana É—aya da na yi ji nake yi kamar a gidan yari nake, bazan iya zaman sati É—aya ba balle na wata biyar, bazam iya ba Safeera."

"Dole ki yi haƙuri ki zauna, zama ya kamaki Islaha, dole ki zauna ko bakya so." Katse kiran ta yi ta kifa kanta a kan kujera tana kuka sosai.

Rehaan yana tsaye a falon bata san yana nan ba, duk abinda take faÉ—a yana jinta kuma yana kallon ta. Ya yi tsaki ya bita da kallo ganin yadda take kuka kamar ranta zai fita, kukan da take yi ne ya saka har ya shigo ta san ya shigo ba, amma da zata ji motsinsa ko ya ya ya ke.

Ya shafa kansa kaɗan, ya hau sama ba tare da ya faɗa mata saƙon Abba ba, bai jima ba ya sakko, footstep ɗinsa ya saka ta kalli wajan suka haɗa ido dashi. Bata ɗauke ido daga kallonsa ba, shi kuma ya janye idanunsa daga cikin nata yana sakkowa inda take a hankali.

Islaha ta miƙe tsaye tana jira ya ƙaraso dan tana da case da shi, yana ƙarasowa zai gifta ta inda ta ke cikin murya mai sanyi da rauni ta ce, "Can we cancel the contract? Gaskiya bazan iya zama a gidan nan na sati ɗaya ba balle kuma wata biyarc Ina buƙatar barin gidan nan da gaggawa, ina da abubuwan da zan yi wanda bazan iya yinsu daga nan ba, kuma sun fi zaman yarjejeniyar nan mahimmaci a gare ni, allow me to go, na yi maka alƙawarin zan baya ka kuɗinka.”

Shi dai kallon ta kawai yake yi ganin ta wani firgice, kana kallon ta ka san ta ci kuka ta gode Allah, ya yi nata shiru bai tanka ba dan ba shi da lokacin wannan wasan na ta.

Ganin bai ce komai ba sai Islaha ta ce, "zan iya yin aiki a ƙarƙashinka har sai ka cire kuɗin da ka ke bina, amma mu kawo ƙarshen contract ɗin nan, sannan ka sake ni islamically."

Wani kallon up and down yake yi mata jin tana raina masa hankali, sai ya kawar da kansa gefe ya sake kallon ta sannan ce, "let's go" ya faÉ—a yana wuce ta.

Islaha bata motsa daga inda ta ke ba ta ce, "zuwa ina?."

Ya waiwayo ya sake kallon ta idanunsa suna yawo akan fuskar ta, jin rainin hankalin tambayar da ta yi masa ya saka ya ce, "siyar da ke."

Islaha ta buÉ—e idanunta waje tana kallonsa ta ce, "za ka iya ai, waye ya sani ko sana'ar ka ce?."

Bai sake kallon ta ba dan ba shi da lokacinta ya ce, "let's."

"Bazan fita ba sai an faÉ—a min inda za mu je, ka faÉ—a min ina za mu je sai na biyo ka, in ban ji dalili ba babu inda zan je."

Ya girgiza kai bai ce komai ba, dan shima bazai faÉ—a ba sai dai a fasa zuwa wajan Abban gabaÉ—aya. Ya dawo da baya zai koma sama sai Abba ya kirasa a waya, yana É—auka Abba ya ce, "kuna ina ne? Jiran ku muke yi fa."

Ray ya kalle ta sannan ya ce, "Ta ce baza ta zo ba Abba." Islaha ta ɗan buɗe har tana dafa ƙirji jin sharrin da ya yi mata, sai ta dabarbace ta ce, "ni ban ce bazan je ba."

Jin abinda ta ce sai ya yanke wayar yana yi mata kallon akace ba ki da kunya. Islaha ta harare shi ta ce, "kai na cewa bazan je ba sai ka faÉ—a min inda zaka kaini ba shi ba, ka daina yiwa mutane sharri kana faÉ—ar abinda basu faÉ—a ba, kuma ko babu komai yanzu na san inda zamu je."

Shi dai bai ce mata komai ba ya fita, ta bi shi da harara ta ɗauki mayafinta da aka kawo ta da shi jiya ta saka ta biyo bayansa bayan ta rufe ƙofar.

Sai a lokacin ta ke kallon ɓangaren nasa, daban yake a cikin gidan, ga shi babba kamar gida mai zaman kansa, har gate ne da shi kamar ba a gidan ba, ga wajan ajjiye mota a ɓangaren kamar. Ɗawisu ta gani suna ta yawo, sai tattabaru da suke ta zagawa a wajan alamun a wajan ake kiwon su.

Ta jikin gate ɗinsa ta ga wani apartment iri ɗaya da na kowa na gidan, dan ɓangrensa ne kawai ya fita daban kamar ba a gidan yake ba. A lokacin ta ga ya ƙarasa aata ƙofa ko waiwayonta ba ya yi, ta ɗaga ƙafa da sauri ta ƙarasa, yana buɗewa ya shiga ta bi bayansa da sallama a bakin ta.

Tana shiga Daada ta tarbe ta da fara'a har tana tafi tana faɗin, "Ga Ishlaya, barka da zuwa. Ƙaraso nan ku zauna kusa dani."

Islaha dai kanta yana ƙasa tana murmushi, dan Ishlaya ɗin nan yana bata dariya, ko bata yi niyar dariya ba indai zata ce Ishlaya sai ta yi dariya, ta ƙarasa inda Daada take ta zauna a ƙasa.

Daada ta dafata ta ce, "Ishlaya ya na gan ki kamar kin yi kuka, lafiya?."

Islaha ta girgiza kai ta ce, "Lafiya lau, Barka da dare."

Daada bata amsa gaisuwar ba ta ce, "ban yarda ba, ko wannan mara kunyar ne ya yi miki wani abun?." Islaha ta girgiza kai alamun a'a amma murmushi take yi.

Daada ta ce, "duk abinda yake damunki ki zo ki faÉ—a min, in akwai abinda ki ke so ina nan ina jiran ki, kar ki dinga takura kan ki, kin ji ko?." Islaha ta É—aga kai alamun to nan ma bata ce komai ba.

Daada ta ce, "ya zaman baƙunta?."

"Alhamdu lillah."

Islaha ta kalli Abba da yake yiwa Rehaan magana ta ce, "Ina yini."

Abba ya kalle ta da murmushi ya ce, "Lafiya lau, Islaha ko?." Islaha ta amsa da eh dan babu yadda zata yi, da wani ne daban bazai yi gangancin yi mata wannan tambayar ba.

Daada ta ce, "na kira ku nan ne dan na yi mu ku nasiha, kuma na ba da amanarta a hannun ka."

Sai ta kalli Rehaan da ya ke danna wayarsa ta ce, "Kai ba danna waya na kira ka ka yi ba." Ray ya É—ago ya É—an kalle ta sai ya ajjiye wayar ya haÉ—e hannayensa waje É—aya.

Daada ta ce, "Ga amanar mata nan na ba ka, in ka cutar da ita Allah bazai bar ka ba, in ka wulaƙanta ta ina so ka san babanka ka wulaƙanta, in ka yi mata wani abun da ya sosa ranta ina tabbatar maka da ga wanda ka yiwa nan a zaune. Ka riƙe ta hannu biyu, ku yi zaman lafiya daga nan har a tashi duniya, ka ji ko?."

Kamar ba da shi take magana ba, sai da ta É—an jima da magana maganar sannan ya É—aga kai alamun ya ji.

Daada ta kalli Islaha ta ce, "kar ki damu da yadda auren yazo, ki yi haƙuri ki kwantar da hankalin ki komai zai wuce, kin ji?." Kamar yadda bai yi magana ba itama bata yi ba, ta yi murmushi kawai.

Daada ta kalli Rehaan ta ce, "na san iyayenka sun dawo daga kai ƙanwar ka, ka shiga da ita ɗakin ko wacce su gaisa ka gabatar mata dasu."

Bai ce komai ba ya dai kalli Daada kawai kafin ya ɗauke kai, ya rasa meyasa ko yaushe sai ta ƙirƙiri abinda ta san ba ya ƙauna.

Daada ta kalli Abba ta ce, "Ba ka ce komai ba."

Abba ya yi murmushi ya ce, "Allah ya ba da zaman lafiya, Allah ya É—orar da zaman har abada."

_Ba amin ba, zaman nan bazai taɓa ɗorewa ba in Allah ya yarda._

Islaha ta faÉ—a a ranta tana jin addu'ar ta yi mata nauyi sosai, shi kansa Rehaan abinda yace kenan, yana girgiza kai dan ba addu'ar da zai ce amin ba ce. Daada ce kaÉ—ai ta amsa da amin tana fara'a, ta sake kallon Islaha ta ce, "an kai miki abinci?."

Islaha ta ce, "Mama ta kai min da kanta.

Daada ta washe baki cikin jin daɗi ta ce, "Saddiƙa ƴar albarka kenan, tana ta ɗawainiya da ke a gidan nan, na san daman in ba ita ba babu wanda zai kula da lamarin ki. Har gwara ma ta tsakiyar da ta ƙarshe za su kwatanta abin arzuƙi da daddatko irin na fulani, amma ta biyun ƙarshen nan daman ba halin fulani ne da ita ba, balle ta san kara da datattakun su."

Babu wanda ya tanka mata a cikinsu, sai Rehaan da ransa ya ɓaci, ba ya son wannan baƙar maganar da take yawan faɗawa Mamy a a gaban ko waye, amma bai tanka mata ba ya share ta.

Abba ya kalli Ray ya ce, " ku je wajansu, in kun dawo ka zo ina neman ka." A ciki Rehaan ya amsa da to ya miƙe tsaye ba tare da ya kalli Islaha ba.

Daada ta ce, "ku je ku gaisa da mutanen nan gidan."

"To Daada, a huta lafiya" ta faɗa tana miƙewa ta fita, shi tuni ma ya fita daga falon ta biyo bayansa tana harararsa.

Daada ta bita da kallo tana murmushi har ta ɓace daga ganinta ta ce, "Ya ka ke ganin haɗin nan don Allah? Ba ka ga sun dace da juna ba?."
Chapter 11 · 0% Book details